Chapter 54
Chapter 54
har ya kai ki zuwa cikin halaka". Zafin da kalamansa suka yi mini ya sanya ni toshe kunnuwana da tafukan hannayena. "Ya isa haka na ce ya isa". Na yi zancen cikin sarƙafewar harshe da rawar murya. "Bai isa ba na ce bai isa ba. Kin cutar da rayuwarki a shekarunki har kin san ki iya zuwa cikin otel". "Ya ishe ka". Na yi zancen cikin zafin rai da ɗaga amo, tar na buɗe idanuna tare da nuna shi da ƴar manuniyar ƴatsata, jikina har izuwa lokaci bai bar rawa haka nan hawayen da suke kwaranya daga koramar idanuna ba su daina gudana ba. "Ka na tunanin Bawa yana da damar tsarawa kansa irin rayuwar da ta dace da shi ne? Ka na zaton cewa akwai wanda zai zo rayuwarsa ta lalace tun daga tushe sannan duhu ya mamaye hasken da ya zamo masa sandan jagora? Na san ka na da ilmi don ba ba ka yi zubin jahilai ba sai dai ilmin bai yi maka amfan tun da ya kasa samar maka da amshoshin mungayen kalaman da kake jifa na da su, ilminka bai tsinana maka komai tun da bai hana ka zartar da hukunci akan abin da ba ka da tabbacin akan sa ba. Ka sa an yi maka bincike akaina sai me ye na ce sai me ye? Me ye haka ya tsinana maka sannan ta ina hakan ya amfane ka?". Sai da na yarce hawayen da yake tsintiri a bisa kuncina kafin na sama zarafin ci gaba da maganar cikin raunin da yake fitowa kai tsaye daga ƙasan zuciyata. "Na ji na yarda binciken da ka yi a kaina ya kawo maka shi daidai, a cikin gidan karuwai nake rayuwa amma shin ka damu da binciko dalilin da ya yi silar zuwa na cikin gidan har nake rayuwa a cikinsa?. Na yarda zaman kaina nake yi ba na tare da iyayena, ƴan uwa balle kuma dangi. Babu wani wanda zai ƙwabe ni idan na yi ba daidai ba balle kuma wanda zai dawo da ni kan turba a sanda nake ƙoƙarin kauce hanya, amma shin ka binciko dalilin da ya sa na zaɓi na yi irin wannan rayuwar? Me yasa ba ka sa an binciko mana yadda na gudanar da rayuwata ta baya ba?. Ka taso a cikin gata ka sama duk wani kulawa, tattani tare da riritawar da ko wani ɗa yake samu a zamanin ƙuruciyarsa, ka ci abinci mai kyau, ka sha abin sha mai kyau, ka kwanta a waje mai kyau sannan ka sama ilmin addini da na zamani a makarantar da kulawa ya wadata. Ka rayu da kulawar iyaye da kuma dangi waɗanda da ka ce wash za su tambaye dalili, sannan ba sa bari hawaye ya zuba daga idanunka kafin ka nema an tanada maka shi ta ina hankali da tunaninka zai sarrafa mata cewar akwai waɗanda ba su sama kwatankwacin irin gatan da ka samu ba. Ban taso da irin wannan gatan ba ranka ya daɗe amma mahaifina bai bar ni na taso cikin rashin tarbiyya ba, haƙiƙa ya wadata ni da ilmin addini da ya kai matakin har na hadda alƙur'ani mafi girma da daraja a cikin dukkan littattafan da Ubangiji ya sauƙe wa Annabawansa". Na ja dogon numfashi na fesar kafin na sama lasisin ci gaba da amayar da zancen, idanuna suna hasko mini abubuwan daki-daki tamkar yanzu suke wanzuwa. "A zamanin rayuwata ta baya na yi shura na ɗaukaka ta yadda duk wata uwar da za ta yi ɗiyarta faɗa da nusar da ita akan ta guji ruɗi da ƙyale-ƙyalen cikin duniya da ni Amatullah take buga mata misali. Na rayuwa a matsayin kamilar mace, mai nutsuwa, mai tarbiya, wacce hankali ya ratsa jini da jijiyoyin jikinta, mace wacce ta san kanta. Wacce babu wani abun duniya zai ruɗe ta ko kuma ya sauya mata tunaninta da yadda takr hango abubuwa, ana tinƙaho da ni a cikin unguwa yayin malamaina a makaranta su na alfahari da ni kafin guguwar ƙaddarar dake sarrafa rayuwata ya jijjige kyakykyawan tarihin da na kafa tun daga tushe. Lokaci guda ya shafe duk wani aikin alkhairin da na rayu a kansa ya shafa miji baƙin fentin da zai bibiyi rayuwata har ranar da numfashi zai yi ban kwana da gangar jikina. Na ja wa dangina abin kunya na tozarta iyayena mussamman mahaifina ya kai munzalin da har wasu suke tantama tare da sanya shakku akan tarbiyyar da ya ba ni. Idan ka san mafari ba ka san ƙarshe ba don haka kar ka ƙalubalence kowa a bisa rayuwar da ka ga yana yi ba tare da ka zurfafa bincike ka kuma ji ta bakinsa ba. Danganta ni da kalmar karuwa da ka yi kuma za mu yi hisabi da kai a ranar da ake wa tare da Yaumul tagabum ranar da Allah zai haɗa Bayinsa tun daga zamanin kakanmu Annabin Adamu har zuwa zamanin ƙarshe". Ina dasa aya a zantukana na sunkuya na ɗauki bokati da moppern na yi shigewa ta cikin kicin na bar shi tsaye a wajen. Ina shiga cikin kicin ɗin na mayar da ƙofar na rufe tare da jingina jikina a jikin ƙofar, sannu a hankali na soma sulale wa ƙasa har sai da na yi zaman ƴan bori dirshan a ƙasa. Hawayen da suke gudana a idanuna suka ci gaba da zuba tamkar da bakin ƙwarya duk yadda na so na yi karanto wani yanki daga cikin addu'o'in da na haddace a cikin kwanyata, lamarin ya faskara komai ya gagare ni aikatawa. Haka na cigaba da kukan mara sauti illa zafi, radaɗi da kuma zogi a cikin raina. Da ƙyar na tashi na je na ɗauko mopper da tsumma kana na ɗaukin bokatin na buɗe ƙofar kicin ɗin na fito da zummar gyara inda ruwan ya zube. Ina fitowa idanuna suka sauƙa akan fuskarsa yana zaune akan kujerar zaman mutum biyu ya kwantar da bayansa a jikin kujerar, ya lumshe idanunsa tamkar mai bacci. Sai dai tun daga kallon farko da na yi masa na fahimci cewa ba bacci yake yi ba a farke yake. Ban b ta kansa ba na soma yin aikin da yake gabana na saka tsumman ina tsame ruwan wajen ina matse wa a cikin bokati sai da na tsame ruwan tas, na sama mopper na goge wajen. Na ji wani jiri ya na ɗiba na tare da ƙoƙarin kayar da ni ƙasa sai da na dafe jikin kujera kafin na iya tsaya wa akan ƙafafuna da suke rawa alamar sun gaza ga ɗaukar nauyin gangar jikina. Numfashina ya soma harɗewa waje guda jikina ya ɗauki zafi gau tamkar garwashin dake ƙasa tukuban tsire. Duk wani karatun da ya fara ziyartar ƙwaƙwalwata shi bakina ya soma karantawa ban gushe ina yi ba har sai da na ji wani sanyin nutsuwa ya ziyarci sashin ruhina, ƙarfi ya ziyarci sakakken gangar jikina da ya sake tamkar ƙanƙarar da aka jefa a cikin ruwa. Na cije leɓena yayin da nake ƙoƙarin tashi sai dai na kasa hakan sa boda nauyin da gangar jikina ya yi mini. "Ki na lafiya kuwa?". Na tsinkayo amon muryarsa tamkar daga sama ya sauƙa na'urar naɗan sautina, lamarin da ya sauƙar mini da wani karsashi a ciki jikina. Ban san lokacin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98