Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 3

Chapter 3

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,215 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ma kamar tijarar da mahaifiyarta za ta yi mana idan ta ji wannan maganar". Amir ya yi zancen cikin tashin hankali. Haka suka kwana a zaune yadda suka ga rana haka suka ga dare. [12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE* ©️Maimuna Tijjani Iyam ________________________________________ Page 4️⃣2️⃣ Washe garin ranar da ƙyar nake iya buɗe idona na jigata na zama majinyaciya tuburan ko yatsan hannuna ba na iya ɗagawa, duk yadda na so na tashi na gabatar da sallan asubahi na kasa tashi haka na ci gaba da zama yashe a wajen numfashina yana fita da wani irin sauti mai ban tsoro da haifar da firgici. "Ya Subhanallahi! Lafiyarki kuwa?". Na yi an jefa mini tambayar lokaci guda ana ɗago n daga inda nake yashe, dishi-dishi idanuna suke gano mini wacce ta takaima mini daren jiya ta nuna mini banɗaki. "Lafiyar ki kuwa ki na ji na?". Ta ƙara watsa mini tambayar tana riƙo hannuna ta sanya cikin nata tana murzawa a hankali. Da ƙyar na iya raba tsakanin haƙwarana da suka manne da juna tamkar wanda aka sanya mayen ƙarfe a tsakaninsu na furta zancen can ƙasan maƙoshina. "Don Allah ki taimaka mini da ko ruwa ne na sha, kar yunwa da ƙishirwa su yi ajalina". Ba ta amsa mini ba ta tashi ta fita babu jimawa ta dawo ta miƙo mini buredi da shayi. Ban yi wata-wata ba na karɓa kofin na kafa bakina sai da na sha kusan rabi kana na dire kofin, na soma yagan buredin ina ci hannu baka hannu ƙwarya. Take na ji cikina ya murɗa na ji tamkar ana ɗauɗaure mini dukkan kayan cikina, babu shiri na fita waje da sauri na dinga warara amai kamar zan amar da dukkan kayan cikina. Sosai na galabaita jikina ya yi sanyi ƙalau ko tashi daga wajen na kasa yi. Ta fito daga ɗakin tana ta jeranta mini sannu ta kawo mini ruwa na kurkure bakina na kwance fuskana kana na yi alwala. Ta riƙe ni muka shiga cikin ɗakin ita ta gyara wajen da na yi aman, ta dawo ta zauna a gefe na har sai da na iddar da sallan asubahin da na yi a makare na shafa addu'an da na yi kana na waigo ina kallon ta. Kafin na yi magana ta riga ni. "Sannu ya ya jikin nakin?". Na ƙirƙiro murmushin da iya ka cinsa kan leɓena na dasa a fuskata kafin na ce"alhamdulillah da sauƙi na gode sosai da irin kulawarki gare ni, ga shi kuma ko sunanki ban sani ba". Tun da na soma maganar take ta kallo na har na kai aya, ta gyara zamanta kafin ta ce sunana"La'aniyatu". Na waro idanuna waje cikin da mamaki na maimaita sunan"La'aniyatu kuma?". Ta gyaɗa mini kanta"sunana kenan, ba ki taɓa cin karo da irin sunan ba ko?". "Gaskiya tun da nake ban taɓa jin makamamcin irin wannan sunan ba. Amma kuwa kin san ma'anar sunan?". "Ina kuwa zan san wani ma'anarsa ni dai sunan da mahaifiyata ta sa min kenan. A cewarta sunan ne ya yi mata daɗi kuma da shi kowa yake ƙira tun tasowa ta har yanzu da nake yi miki wannan maganar". "Tirƙashi! Ita ma mahaifiyarta kin a cikin gidan nan take?". "Ƙwarai kuwa, Hajiya Babba ita ce mahaifiyata". Muƙut na haɗiye wani miyau mai ɗaci daga maƙoƙarona ina sauƙe ɓoyayyan ajiyan zuciya ban san lokacin da zuffa ya keto mini ba na fara fiffita da bakin hijabina. "Ke kuma me ye sunanki?". Kalamanta suka yi nasarar dawo da ni cikin hayyacina daga karatun wasiƙan jakin da na afka, sai da na furzar da zazzafan iska daga bakina kafin na ce"sunana Amatullah". "Daga wani gari kike don na ga alamar ke ba ƴar cikin garin nan ba ne, tun daga yanayin Hausarki na ga ne haka. Sannan me ya rabo ki da gidan iyayenki?". Na ja dogon numfashi na fesar kafin na yi jarumtar faɗin"sannu a hankali za ki san komai game da ni. Amma kafin zuwan wannan lokacin ina son ki yi mini wani alfarma guda ɗaga". Ta gyara zamanta alamar tana ji da saurarona hakan ya ba ni damar ci gaba da maganan cikin ƙwarin gwiwa. "Ina son na san wasu abubuwa dangane da tsarin gidan nan, wanda za su taimaka mini wajen gudanar da rayuwata a cikin gidan nan ba tare da wani matsala ta faru ba". Ta ɗan jim tana ta kallona kafin can ta furta"da farko dai kowa da kika gani a cikin gidan nan zaman kanta take yi, mafi akasarinsu iyayensu ne suka kore su ko kuma suka aikata wani mummunan abin kunyan da ya hana su zama a gaban iyayen ala dole suka haɗo kayansu suka baro iyaye da danginsu. Wasu kuma sun gagari iyayen ne shi ne suka sallama su suka shigo duniya, da yawan matan da za ki gani a cikin gidan akwai bakin uwa akan su wannan dalilin ya sanya ba sa kunya ko shakkan aikata komai. Abu na biyu shi ne komai na gidan nan na sayarwa hatta ruwan da za ki wanke idanunki da shi, in har ki na son zamanki cikin gidan nan ya yi tsawon rai dole sai kin zama fitsararriya ta buga wa a jarida wacce ba ta bari ko ta kwana, sai kin zama wacce ba ta raina ruwan shuka wacce duk wanda ya ɗaga mata ɗan ƴatsa sai ta karya shi komai tsufa ko kuma furfuransa". Babu shiri na dafe ƙirjina"na shiga uku! Wani irin zama ne wannan? Sannan wani irin sana'a matan gidan nan suke yi da suke iya ɗaukan nauyin kansu, tun da komai na sayarwa ne a cikin gidan?". Ta murmusa kafin ta furta"kowacce da kike gani tana da hanyar da yake kawo mata kuɗin shiga sai dai mafi akasarinsu jikinsu ne jarin su. Jikinsu suke bayarwa domin biyan buƙatan ransu. Suna hulɗa da manyan mutanen masu madarar kuɗi a hannunsu da masu riƙe da madafun iko. Ummata tana da ɗaurin gindi a garin nan don ta san manyan mutane da suke da ikon juya lamarin jahar nan shi ya sa take cin karenta babu babbaka babu wanda ya isa ya taɓa ta ya kwana lafiya". "Jikinsu fa kika ce suke bayarwa domin biyan buƙatansu. Zina kenan fa?". "Ƙwarai kuwa kuma ke ma ina mai tabbatar miki idan har ki na zaune a cikin gidan nan, a kwana a tashi wataran sai kin bi layin da suka bi. Don shi kaɗai ne hanyar rayuwa a cikin gidan nan shi kaɗai ne mafita ga duk wata macen da take zaune a cikin gidan nan". Na zabga tagumi da hannu bibbiyu ina sauƙe numfashi wani na bin wani tamkar wacce ta yi gudun ceton rai, ta dafa kafaɗuna"ba ki da wani mafita da ya wuce wannan, in kuma ba haka ba sai dai yunwa da ƙishirwa su yi ajalinki. Don ko mutuwa za ki yi babu mai kawo miki agaji a cikin gidan nan, kowa harkan gabanta take yi babu ruwan wani da wani. Kin ga rayuwar cikin gidan nan rayuwa ce da babu imani a cikin ta balle tausayi don haka tun wuri ma gwara ki yi ɗamara". Na furzar da zazzafan iska daga bakina kafin na ce"babu wani mafita sai wannan? Ni wallahi ko aikatau ne zan yi don

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});