Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 22

Chapter 22

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,213 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

na amsa matsamin da take miƙo mini na ci gaba daga inda ta tsaya. Gwangwani madarar ruwa huɗu ta ɗauko duk ta ɓula su ban da madarar garin da ta ɗauko saket guda ta yanke bakinsu da almakashi. Ta ɗauko wani ƙaramin kwanon tangaran ta juye madarar garin a cikin ta dame shi da ruwa sannan ta juye cikin ruwan da yake tafasa akan wutan ta yi ta juya shi har sai da ya fara yin kauri, ta juye madarar ruwan gwangwani biyu ragowar biyun kuma ta ajiye su a gefe, ruwan flavour na ga ta tarfa a ƙadan a cikin kafin ta sauƙe shi. Ta ɗauko kofi mai marfi ta juye madarar ruwan guda biyu a ciki, gwangwanin huɗum gabaɗaya ta haɗa ta mayar da su inda ta ɗauko su. Tana juyo wa muka haɗa ido. "Wannan kallon fa?". Ta jefa mini tambayar cikin tsawa da ɗaga murya, na yi hanzarin rusunar da ƙwayoyin idanuna ƙasa tare da faɗin"ki yi haƙuri". Kafin ta kai ga furta wani kalma Hajiya Muhibbat ta shigo cikin kicin ɗin duk muka haɗe bakin wajen gaishe ta ta amsa mana fuskarta ɗauke da annurin da ya ƙara fitowa da kyawunta. "Sannunku da aiki". Ta yi furucin yayin da take sa hannu ta ɗauki ƙosan da yake gabana ta kai bakinta. "Amma ƙosan nan ba dai laushi ba, ke kika yi haɗa ƙullin ne?". Na jijjiga mata kaina alamar a'a tare da faɗin"ba ni ba ce". "Amma kuwa ya yi daɗi sosai. Na tabbatar Saif zai ji daɗinsa". Ta juya tana kallon Altine"ki shirya abincin a dinnig table, Amatullah kuma ta je sashin Saif ta ɗauko su Aryan ta yi musu wanka kafin ki gama". "To ranki ya daɗe uwarmu maganin kukanmu". Ba ta amsa mata ba ta juye ta fice daga cikin kicin ɗin tana amsa ƙiran da ya shigo cikin wayarta. Bayan fitanta mun fi mintuna uku cikinmu babu wanda ya yi magana, har na kammala tuyar ƙosan na sauƙar da man. Ganin shurun ya yi yawa ya sani kawar da shi ta hanyar faɗin"Anty ina ne sashin nasan na je na ɗauko su....". Tun kafin na rufe bakina take gallo mini harara wani na bin wani tamkar wacce na watsa garwashin wuta, ko na faɗi wani abun da bai yi mata daɗin ji a kunnuwanta ba. "Daman can ba ki san sashin nasan ba kika bari ta tafi daga nan ba ki tambaye ba?. Sai ki fita yanzu kam ai ki tambayo". Yadda ta furzo da zancen shi ya fi komai ƙona mini rai da har ban san lokacin da bakina ya suɓuce na furta kalaman da suka shayar da ita giyan mamaki ba. "Don na tambaye ki laifi ne? Na da ke ɗin gabaɗaya a ƙarƙashin Hajiyar muke kuma aiki muke yi don a biya mu". Ban tsaya sauraron amsar da za ta ba ni ba na fice daga cikin kicin ɗin zuciyata har wani tafasa take yi tsabar ɓacin ran da nake cikinsa. A rayuwata ta duniya na tsani a wulaƙanta ni balle a zo gandon da za tozarta ni. Sai da na fito cikin harabar gidan na riƙe ƙuguna ina tunanin inda ya kamata na nufa da zai sada ni sashin nasan, jiya dai lokacin da ya ce a shirya su Aryan za su fita wata ƙofa na ga ya shiga a cikin falon Hajiya babu jimawa kuma ya fito a shirye tana ba za ƙamshi. Na sauƙe ajiyan numfashi a hankali ina ƙara ɗaga kaina sama, idanuna suka sauƙa akan Baba mai gadi da yake nufo inda nake tsaye, hannunsa riƙe da bokatin ruwa. Da sauri na isa gare shi na kai hannu zan karɓa bokatin ya hana ni. "A'a ɗiyata bar shi ai ba za ki iya ba ma, wai bayi ne nake so na yi a shukokin nan mai musu bayin yau bai sama zuwa ba". Na saki taƙaitaccen murmushi kafin na ce"Allah sarki! Ni ma wai Hajiya ce ta ce a je sashin Saif a ɗauko su Aryan, kuma na kasa tantance wanne ne sashin na san". Da hannunsa ya yi mini nufi da sashin kafin ya furta"kin gan sa can shi ne sashin na san". "Ai kuwa Baba na gode sosai da sosai, Baba na ga zanen kanurai a fuskanka na ce ko kai ma kanuri ne?". Sai da ya murmusa kafin ya ce"gaba da baya ma kuwa, ni haifaffen jihar Borno ne cikin garin bama. Uwa da ubana duk kanurai ne". "Ni ma kuwa mahaifina kanuri ne sai dai ko kaɗan ban iya yaren ba". "Kuma ai ba shi ma da wahala idan aiyukan cikin gidan sun yi miki sauƙi ki dinga zuwa ina koya miki. Ko kuma ki zagaya wajen mai ɗakina". Cike da jin daɗi na furta"na gode sosai Allah ya saka da alkhairi". "Amin". Ya amsa da shi yana ƙara yalwata annurin dake kan fuskarsa, ya wuce wajen bayin shukansa ni ma na ɗauki hanyar sashin da na ya nuna mini. Wannan sashin da na ga ya shiga da safe ne. An ƙawata ƙofan sashin da shuke-shuken wasu turanni masu kyau da ɗaukar hankali da suka kasance launin gore da ruwan ɗorawa. Wasu a cikin wani abu kamar tukunyan ƙasa an taraye a sama. A hankali na isa bakin ƙofan na soma ƙwankwasa tare da rafza sallama. Har sai da na gaji da tsayiwar na juya zan tafi na ji an buɗe ƙofar na waigo na ga Aryan ne ko Ayan oho don ban iya tantance wane ne a cikin su ba. "Ayan ina Aryan ɗin?". Ta tsaya yana kallona"ba Ayan ba ne Aryan ne". "To ina shi Ayan ɗin? Mamanku ne ta ce ku zo a yi muku wanka". Kamar ba da Hausa na yi masa zancen ba ya tsaya yana ta kallona sai can ya ce"Umminmu?". Na gyaɗa masa kaina alamar e kafin ya ce da ni wani abu Saif ya iso wajen hannunsa saƙale cikin na Ayan. Ganin sa ya sanya ni na rusana ina gaishe shi sai dai bai amsa mini ba. Kwarjini da cika idon da ya yi mini ya sanya jikina fara karkarwa da ƙyar na haɗo kalmomin da zan furta suka zauna a bisa harshena. "Daman Hajiya ce ta ce su Ayan su zo a yi musu wanka". "Ki je abin ki za su zo". "To". Na amsa da shi a gajarce ina ɗaukan hanyar barin wajen, na runtse idanuna a ƙoƙarin daidaita nutsuwata da ta yi nisa da gangar jikina. Ni da uwata Hafsatu ta haife ni ban taɓa ganin mutum mai tsananin kwarjini da cika ido irin wannan bawan Allahn ba. Fuskarsa a sake take duk da ba ya murmushi amma fuskar ba a murtuƙe take ba. Ina tafe ina ta saƙe-saƙe a cikin raina har na isa sashin Hajiya ina shiga Aryan da Ayan suka shigo na kamo hannunsu ina faɗin"mu je na yi muku wanka ko?". Suka gyaɗa mini kansu alamar sun ji. Na ja hannunsa muka nufi cikin ɗakinsu, na cire musu kayansu na ɗaura musu towel muka shiga cikin banɗakin. Fanfon banɗakin irin na gidan Anty Zulaihatu ne mai na ruwan zafi da na sanyi, don haka ban shan wani wahala ba na kunna na ruwan zafin na tara na na tsirka shi da na sanyi daidai

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});