Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 27

Chapter 27

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,206 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

hago da har ban san sa'ilin na saki ƙara ba ina dafe kuncina cikin jin zafi da raɗaɗin da ya ratsa har cikin kwanyata. "Har kin isa ina magana ban yi wannan lalacewar ba. Tun farko daman na lura kaman kanki yana fisga sai na gyara miki zama tukunnan a cikin gidan nan kafin mu daidai". Tana ƙare zancen ta hankaɗe ni na sauƙa daga kan katifar zuwa ƙasa ta haye ta yi kwanciyarta. Na daɗe zaune a wajen ina jin raina yana yi mini wani irin zogi, yawun bakina ya jirkice ya koma mini tamkar maɗaci, zan iya cewa tun da nake a cikin duniya ba a taɓa cin zarafina an wulaƙanta ni irin na yau ba, na bi kayan jikina da ido da suka jiƙe sosai ina jin wani sanyi yana ratsa cikin jikina. A hankali na tashi na fita daga cikin ɗakin ina ɗaga ƙafata da ƙyar har na fito cikin harabar gidan na nema wani dakali na zauna ina shan hantsi tare da haɗa kaina da gwiwa. Take zuciyata ta soma karatu mini tsohon karatun da na daɗe da haddace shi a cikin kaina. Tabbas gata da mutumcin duk wata ɗiya mace shi ne gidan iyayenta haka nan babu inda za ta je a kanta da kima da daraja kamar a zo a tarar da ita a cikin gidan iyayenta. Na tuna da wani magana mai cike da hikima da darrusa masu yawan gaske. Inda yake ce wa da mu a wurare uku ya dace a sama mace wacce ta amsa sunan mace ba wacce ta rako mata zuwa duniya ba. Wuri na farko shi ne a same ta a gaban iyayenta, in ba a same ta a nan ba to a same ta a cikin gidan mijinta in ba ta gidan mijinta to a same ta a cikin kabarinta. Waɗannan wurare guda uku su ne suka fi dace da mazaunin mace, in ba ta gaban iyayenta, to ta kasance tana gidan mijinta tana bautar Ubangijinta domin neman aljannarta. In kuwa duk ba a same ta a nan ba to zai fi kyautuwa da saya mata daraja, mutumci, martaba da kuma kima idan aka tarar da ita a cikin kabarinta. Ban san lokacin da hawaye suka zarya a kan fuskata ba sai jin ɗumin su na yi akan fatan fuskana da har yanzu yake yi mini zogi sa boda da na sha a hannun Altine. Na ɗago kaina ina ƙarewa girman filin tsakar gidan kallo da Altine ta yi mini umarnin sharewa. Babu shiri na sauƙe wani shirgegen ajiyan zuciya don a girman filin ko tun ƙarfe shidan safe na fara sharan akwai yiyuwar na wuni ina yi ba tare da na kammala ba. Na taɓa kayan jikina na ji ya bushe ƙarau na tashi na ji jiri yana ƙoƙarin nanani da ƙasa babu shiri na koma na zauna na dafe kaina da yake juyawa, ina karanto duk wani addu'ar da ya zo bakina a sa'ilin. Ji da na yi zafin ranar yana takura ni ya tilasta mini tashi daga wajen na je wajen rumfar ajiye motoci kasancewar wajen intalok ne aka layyale ko'ina da shi, na shimfiɗa ɗan kwalina na kwanta a kai ina ta rawar sanyi ban san lokacin da baccin wahala ya yi gaba da ni ba. Sai jin wani gigitaccen ƙara na yi a cikin kunnena da ya tursasa mini tashi ba tare da na shirya wa hakan ba. Sai da na daina jin sauti da motsin komai na tsawon wasu mintuna sa boda yadda ƙaran ya kiɗima ni. Kallon shi kawai nake yi yayin da ya fito daga cikin motan ya zo gabana ya tsaya tare da zura dukkan hannayensa cikin aljihun wandonsa. Bai yi mana ba na tabbatar da hakan ne sa boda ko kaɗan laɓɓansa ba su motsawa. Na kasa motsawa balle na yi yunƙurin tashi daga wajen da hakan zai ba shi daman shigo wa da motar ma'ajinta. Daidai lokacin da jina ya dawo na ji ya saki wani tsaki mai dogon zango kana ya juya ya bar wajen. Da ƙyar na iya tashi tsaye na tsaya akan ƙafafuna da suke rawa da alamta gajiyar su ga jimirin ɗaukar nauyin saƙararren gangar jikina. Na mayar da ɗankwalina kaina na saka na soma tafiya, hanyar gate na nufi don a yadda nake jin jikina ba na tunanin zan iya tsinana komai na zaɓi na koma gida akan na ci gaba da zama a nan. Na yi sa'a ban tarar da Baba Mai gadi a ƙofan ba balle ya hana ni tafiya ko kuma ya tsare ni da tambayoyi me ye yake faruwa. Kai tsaye na fita na soma tafiya ina haɗa hanya tamkar wacce ta yi tatil da kayan maye cikin wannan yanayin har na isa gida lokacin idanuna har wani dishi-dishi suke kallon abubuwan. Na ji wani daɗi a cikin raina da na hango ƙofar ɗakin a buɗe don tsayawa buɗe ta ma galabaitar da ni zai ƙara ni sosai. Kai tsaye na afka cikin ɗakin sai dai abin da na gan ya sanya ni dole na ja na tsaya. Wata budurwa na tarar a cikin ɗakin tana sauya kaya, gefe guda kuma an saka katifa, akwati da ragowar sauran kayan amfanin yau da kullum. "Wace ce ke kuma? Me ye kike yi a nan?". Na watsa mata tambayoyin a tare, ta bi ni da wani malalacin kallo kafin ta ce"ko ke ce Amatullah ɗin?". Na gyaɗa mata kaina alamar e da hakan ya ba ta damar ci gaba da maganar. "Yanzu wannan ɗakin ba mallakinki ba ne mallakinmu ne ni da ke". "Ban gane abin da kike son faɗa ba". Ta yi fari da idonta kafin ta furta"kamar yadda kika ji na faɗa wannan ɗakunan mallakinmu ne ni dake. Tare za mu rayu a cikinsa na kama hayar rabin ɗakin kamar yadda idanunki suke nuna miki". A kufule na ce"hakan ba mai yiyuwa ba ne, don duk ɗakunan cikin gidan nan ai mutum ɗaɗɗaya ne a cikinsa". Ta galla mini harara"ba kya buƙatar sai na ba ki amsa da kalmomin baki tun ga shi idanunki sun ga ne miki zahiri". [12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ________________________________________ Page 5️⃣4️⃣ Na yi tsaye mamaki da al'ajabi ya na yi motsawa daga inda nake tsaye kamar gunkin ƙasar india. Na ja dogon numfashi na fesar daga bakina ina jin wani abu yana tasowa tun daga ƙasan ƙirjina har zuwa tsakiyar kaina. Ban kuma cewa da ita komai ba na ja ƙafafuna da suka sake na isa kan taburmana na zauna na ɗaura kaina a bisa gwiwoyina ina mayar da numfashi kamar wacce ta yi gudun ceton rai, ji nake yi kamar ɗakin yana juyawa na lumshe idanuna ina cije leɓena haɗe da sauƙe wani gauron ajiyar zuciya mai matuƙar sauti. Kaina wani irin ciwo yake yi kamar zai faɗo ƙasa na zame na kwanta akan bayana ina kallon rufin ɗakin ina karanto suratul Yusuf daga cikin kaina, ban yi nisa ina yi ba na ji an kunna sauti an ƙure sauti a cikin ɗakin. Sai da na firgita na tashi na zauna gaba ɗaya na manta da cewar yanzu ba ni kaɗai ba ce a cikin ɗakin, har cikin tsakiyar kaina nake jin sautin yana

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});