Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 80

Chapter 80

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,210 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

damuna haka na kwana idanuna biyu ba tare da na runtsa ba. Washe garin ranar na tashi tamkar majinyaci komai cikin sanyin jiki da rashin kuzari nake aiwatar da shi. Ina zaune a waje na tisa kwanon karin kumallo a gaba na ka sa kai ko da loma guda cikin bakina, Anty Sawwama ta fito har ta tsaya a kaina ban sani ba har sai da ta yi magana kafin na dawo cikin hayyacina daga karatun wasiƙan jakin da nake yi. "Amatu lafiya kuwa? Kin tisa abinci a gabanki tun ɗazu kin kasa ci. Ke ba ki ci ba ke ba ki tashi ba". Sai na haɗo jarumta na yaɓawa kaina kafin na iya raba tsakanin leɓena na ce"babu wani damuwa Anty". Daidai lokacin da Yaya Alhassan da Amir suka suka fito daga cikin ɗakin kwanansu duk da kaina ya na ƙasa hakan bai hana jikina ba ni tabbacin cewa idanunsa suna kaina ni yake kallo har zuwa lokacin da suka durƙusa suka gaishe da Anty Sawwama ta amsa musu cikin sakin fuska da kuma tarin albarka gare su. "Alhassan ka zo ina son magana da kai". Anty Sawwama ta yi zancen idanunta akan Yaya Alhassan da ya amsa da to yana tashi ya bi ta suka shiga ciki. Zaman da Amir ya yi kusa da ni yana jan kunne abincin gabansa shi ya tursasa mini ɗago kaina ina kallonsa fuskarsa ɗauke da murmushi ya ce"abincin ne bai yi miki ba, ko kuma dai yanayin ne kawai?". Sai da na tsame hannuna daga cikin kwanon abincin kafin a taƙaice na furta"na ƙoshi ne". "Me kika ci da har kika ƙoshi? Za ki zage ki ci abincin nan ko kuma sai na yi ɗura miki da ƙarfin tsiya". Na ɗago kai muka haɗa ido ya kashe mini ido guda yana yalwata fuskarsa da kyakykyawan murmushin da har sai da dake tsakanin haƙwaransa suka bayyana. Murmushin dole na sakar masa ina tsoma hannuna a cikin abincin muka soma ci tare da shi mu na ci yana ja na da hirar da amsana ba ya wuce uhm ko hmm haka har muka gama cin abincin na ɗauki kwano na je na wanke na dawo na zauna. Ina zama Yaya Alhassan ya fito daga ganawan da suka da Anty Sawwama na bi shi da kallo na ga idanunsa gabaɗaya sun haɗa sun yi jajir gabaɗaya yanayinsa ya sauya haka ya fice daga cikin gidan ba tare da ya yi mana kallo azurki ba balle ya ce da mu wani abun. Muka taka shi da kallo daga ni har Amir har ya fice kafin Amir ya furta"an ya lafiya kuwa? Na ga ya fito duk yanayinsa ya sauya". Na ɗage kafaɗuna alamar ban sani ba. "Bari ki ga na bi shi na ji ko lafiya". Ya yi zancen yana miƙe wa ya bi bayan Yaya Alhassan, numfashi mai nauyi na sauƙe ina ɗan lumshe idanuna. Haka aka yi sati biyu a jere ba ranar da za ta fito ta faɗi Yaya Alhassan bai tambaye ni akan na goge sautin murya da hotunan nan ba, na kan ce da shi na yi hakan duk da kuwa har zuwa wannan lokacin na gaza goge su. Ba na manta wata ranar juma'a wanda daga wannan ranar tubalin baƙin ƙaddarar rayuwata ta soma, da yammacin ranar Anty Zulaihatu ta zo ta gidan tare da mijinta Mu'azzam domin duba Anty Sawwama kasancewar ba ta ji daɗi a cikin kwanaki, ina ɗaki na ji shigowarsu na fito na gaishe su. Tun da na fito na lura da wani kallon ƙyaman da Yaya Mu'azzam yake yi mini har wani taɓe baki yake yi tamkar wanda ya yi arba da kashi, haka kawai na ji gabaɗaya jikina ya mutu murus har ya tashi ya fita akan zai je da dare ya dawo ya ɗauki Anty Zulaihatu na kasa ɗaga kaina. Zuwan Anty Zulaihatu ya ɗebe mini kewan da nake cikinsa sa boda ba na fita ko nan da can kullum ina cikin ɗakin. Bayan sallan magrib Yaya Mu'azzam ya ƙira ta yana sanar da ita ba zai sama daman zuwa ya ɗauke ta ba, ta hau adaidaita kawai ta koma gida. Ƙarfe takwas saura na dare na fito na raka ta domin ta hau adaidaita muna tafe muna ɗan taɓa hira har sai da muka iso bakin titi kana ta sama abin hawa, muka yi sallama tare da yi mata alƙawarin zuwa gidanta cikin kwanan nan. Sai da na ga wucewan mai adaidaitan kafin na juyo domin komawa gida. A hankali nake tafiyar kaina a ƙasa tamkar wacce take neman wani abu a ƙasan haka har na iso ƙofar gida ina ɗago kaina na ga an dalle mini ido da hasken mota har sai da ya kai munzalin da na kai tafukan hannuna na kafe idanuna. Sai da aka kashe hasken na ga motar ta nufo inda nake na cira kaina ina kallonta sai dai na kasa gane inda na san motar. Hakan ya sa ni soma tafiya zan shiga cikin gida na ji an ambaci sunana cikin sakakkiyar murya. "Amatullah". Da hanzari na juya don tabbatar da mamallakin muryar take idanuna suka sauƙa akan fuskar Saifullah da yake tsaye jikin motan yana kallo na kamar yadda ni ma na zuba masa idanuna. Ya tako ya iso inda nake tsaye. "Kin wuni lafiya?". Bambarakwai na ji tambayar tasan wai na miji da suna Hajara, na ja dogon numfashi na fesar a ƙoƙarin daidaita nutsuwata kafin na ce"idan wajen Yaya Alhassan ka zo to bai dawo gida ba tun da ya fita sallan isha'i". Tun kafin na dire zancen ya katse ni"wajen ki na zo". "Waje na kuma?". Na maimaita zancen ina yi masa nuni da kaina. "Ƙwarai kuwa wajenki na zo ni Amatullah, idan da hali ma magana nake so mu yi mai matuƙar muhimmanci. So samu ma mu nema waje mu zauna". "Ka faɗi duk abin da za ka faɗa, ina sauraronka". "Ki yi haƙuri mu shiga cikin mota sai mu yi maganar". Na ɗaga masa hannuna"ka gaggauta faɗin abin da ya kawo ka, idan kuma ba ka shirya to ni zan koma ciki don ina da abin yi". Ina iya jiyo sautin ajiyan zuciyan da ya sauƙe kafin ya ce"Amatullah ban san yanda za ki ɗauki maganar da zan furta miki a yanzu ba, amma ina so ki sani duk abin da zai fito a bakina a yanzu to daga ƙasan zuciyata yake fitowa kai tsaye kuma iya tsagwaron gaskiyata nake sanar da ke. Tun ranar da na san wace ce ina nufin asalinki da kuma tarihin rayuwarki tausayinki ya maƙale a cikin raina, a duk san da na zauna ba na komai to tunaninki ne da irin abubuwan da na aikata miki yake addaban raina. Yau na zo ne don na furta miki kalmar da ban taɓa furtawa wata ƴa mace ba tun da nake a rayuwata". Cike da ƙosawa da sauraronsa na ce"ka tafi kai tsaye ga zancen da kake son furta wa". Ya ɗan yi jim tare da sadda kansa ƙasa yana murza zoben azurfan da yake saƙale a ɗan yatsan hannunsa kafin can ya ce"Amatullah ina sonki, ina fata da burin ki kasance mata a gare ni sannan uwa ga ƴaƴana". Tun da ya soma maganar na

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});