Chapter 51
Chapter 51
yadda za ku dinga haɗuwa har aikin ya ci". Na jijjiga kaina"ba na son na jawo hankalinsa ta hanyar asiri. In dai kawai in akwai hanyar da za ki yi ki taimaka mini ki yi amma ba wannan ba". Ta yi shuru na tsawon mintuna har sai da na karaya kafin can ta ce"na san otel ɗin da tawagarsa suke sauƙa idan suka zo gabatar da wa'azi a ciki garin nan, sai dai in daga nan za mu sama ƙarin bayani. Don na taɓa ganinsa sau ɗaya a otel ɗin lokacin da ya zo gabatar da wa'azi a cikin tsakiyar watan Ramadana. A lokacin an ce babu yadda mai martaba Sarki bai yi da shi ba akan ya sauƙa a can masarautar amma ya ƙi a lokacin har Gwamma sai da ya saka ba ki amma bai amince ba, dalilin hakan ranar aka yi kora a otel ɗin babu wanda aka ba wa ɗaki sai shi da tawagarsa". Na sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya ina hamdala a cikin zuciyata. Farin ciki ƙarara ya bayyana a bisa fuskata da har sai da na kasa magana. Sai da na yi da gaske na sama zarafin faɗin"to yanzu yaushe za mu je mu tambaya masu otel ɗin?". "Mu je ina otel? Ce miki aka yi haka siddan ake zuwa otel ɗin a soma tambayan ma'aikatansu bayanan kwastomominsu? Ai hakan ya saɓawa ƙa'idar ko wani irin aiki kawai taɓarɓarewar ƙasar nan ya jawo haka. Yanzu dai akwai wani da na sani ma'aikaci ne a otel zan tuntuɓe mu ji abin da zai ce". "Na gode sosai Allah ya saka da alkhairi". Na yi zancen ina rumgume ta tsam a jikina tsabar murnar da ta soma ni a cikinsa kacokam. Mun ɗan tattaunawa da ita kafin mu farga har aka yi ƙiran sallan magrib hakan ya tursasa masa haƙura da zuwa kasuwan sai gobe. Har na tashi zan fita na ce"yau na girki ne?". Ta murmusa kafin ta ba ni amsa da faɗin"yau ina da fitan dare shi yasa ban yi girki ba". "Fita zuwa ina ke nan?". Ta yi fari da idanuna kana ta furta"na yi wani sabon kamu ne ina so na je mu ƙarƙare ta da shi. Na fi so na gama da kowa kafin na yi wannan gyara jikin don idan na yi san na fi son Ogana ya fara shan romonsa". Na bi ta da kallo ina mamaki da juyayin furucinta. "Ai kuwa ba ki yi masa mai kyau ba a Ogan nakin, tun da kin kasa killace masa kanki a shi kaɗai". Ina gama zancen na fice daga cikin ɗakin ina jin dariyar zancen nawan da ta fashe da shi yayin da nake fita daga cikin ɗakin. Sai da na yi alawan sallan magrib kafin na shiga ɗaki, na gabatar da sallan cikin nutsuwa da daidaituwa bayan na iddar na ɗaga hannuna sama da zummar zan yi addu'a ina buɗe bakina kawai na ji wani kuma ya ƙwace mini. Jikina har wani karkarwa yake yi tamkar ana jona mini wutar lantarki, na haɗa kaina da gwiwa ina rero kukan don na gaza samun ikon sarrafa kaina. Sosai nake kukan har sai da gabaɗaya jikina ya ɗauki zafi gau. "Indan kin gama kukan sai ki tashi je Hajiya Babban tana ƙiran ki da gaggawa". Na tsinkayo muryar an yi zancen cikin ɗaga amo, ko da na ɗaga ido har an juya an fita daga cikin ɗakin, da ƙyar na tashi na tsaya akan ƙafafuna sa boda rawar da ilahirin gaɓoɓin jikina yake yi. Haka kawai na ji ƙirjina yana buga wa sa boda na san babu alkhairi a cikin dukkan ƙiran da Hajiya Babba za ta yi maka. [12/11, 3:18 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam _______________________________________ Page 6️⃣6️⃣ Jikina a sanyaye tamkar wacce aka zare wa laka daga cikin jikinta. Muryata can ƙasa na yi sallamar yayin da nake shiga cikin ɗakin Hajiya Babba sai da na yi baki huɗu ana biyar ɗin aka amsa mini tare da ba ni iznin shigowa, na shiga na zauna a ƙasa yayin da ita take bisa kujera tana latsa wayarta na gashe ta a amsa mini ba tare da ɗago kai ta kalle ni ba. "Hajiya an ce kina nema na". Sai da ta salwantar da wasu mintuna kafin ta ce"e daman ƙiranki na yi na yi inda muka kwana da zancen nan nakin. Ya kamata zuwa yanzu mu san matsayar mu mu kuma san inda za mu ɗaura idan muka tashi". Sai da na sauƙe tagwayen ajiyan zuciya mai nauyi kafin na sama zarafin faɗin"Hajiya in sha Allah kwana kusan nan zan zo miki da magana mai ƙarfi. Ina ta yin iya ƙoƙarina ganin ban ba ki kunya ba...". Tun kafin na rufe bakina ta doka mini tsawan da sai da ta tursasa mini runtse idanuna. "Ki rufe min baki ba dogon surutu na ƙira ki ki yi min ba, na ba ki nan da wata biyu idan kika gaza aiwatar da abin da furta. A iya wa'adin wannan lokacin kike da damar da za ki yi duk wani abin da za ki yi idan kika wuce hakan ko da da awa guda ne tabbas sai na wulaƙanta ki kuma na wulaƙanci fiye da zatonki. Sannan na haɗa miki kayanki ki bar min cikin gidana". Cike da yarda da kaina na furta"in sha Allah ina sa ran kafin wannan lokacin ma na gama haɗa komai". Ta galla mini wani uban harara kana ta soma furzar da zancen da yake cikinta"ya rage na ki ki yi duk abin da kika ga ya fi dacewa da tsari da ginin rayuwarki. Ni dai na riga da na tsayar da magana a matsayina na mai gida kuma mai cikakken iko. Don ba zai yiyu na gina ɗakuna sa boda kasuwanci kuma ke ki zo ki tare a cikinsa ba tare da ki na tsinana komai ba". Cike da girmamawa na ce"in sha Allah". Ta ɗaga mini hannu alamar na tashi na ba ta waje haka na yi mata fatan tashi lafiya, jikina a matuƙar sanyaye na dawo cikin ɗakina kamar ruwa hakan na zube akan tabarmata ina mayar da numfashi tamkar wacce ta yi gudun ceton rai. Tunanai marasa kan gado da tushe suka soma ziyarta cikin kwamyanta da ta toshe wajen guda. Ji na yi ba zan iya jiran safiya ta yi ba sa boda yadda nake tsananin son magana da Zinariya, wannan dalilin ya tilasta mini tashi daga inda nake kwance na fito da zummar zuwa ɗakin Zinariya sai dai na hango ƙofar an garƙame shi da kwaɗo, murmushi mai nauyi na ja na fesar daga bakina tunawa da na yi cewar ta sanar mini za ta fita ba za ta kwana a gida ba. Dole ƙanwar naƙi na koma cikin ɗakin na kwanta ina ta tunanin mafita da hanya mai ɓullewa a gare ni, a haka har wani bacci mai nauyin gaske ya yi nasarar ɗaukarta. Sanyin asubahin da ake busawa shi ya na ratsa cikin jikina shi ya yi nasarar farkar da ni daga nauyayyen baccin da ya kwashe na tashi da ƙyar na je na yi alwala na zo na gabatar da sallan, nan inda na yi sallan na zauna na zabga wani uban tagumi yayin da tunani
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98