Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 60

Chapter 60

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,210 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

dawo ya iske ni a gidan ba a cewarta ba ta yarda da ni ba ta san zan iya zagayawa na ci amanarta ta hanyar keɓewa da mijinta. Duk kwantar da kai da rantsuwar da na yi mata bai ɗaɗata da ƙasa ba haka ta koro ni ta ba ni wasu kuɗaɗe wanda da su na yi kuɗin mota na dawo garin nan". Sosai na jinjina girman iftila'i da masifar da ta faɗa, na cira kai ina kallon ta sai dai kafin na yi magana ta ri ga ni. "Har yanzu ina mamakin yadda aka yi ƴan uwan Saddam suka san mu na tare da shi a cikin otel ɗin nan, har suka zo suka yi mana tijara. Bayan kuma shii da kansa ya ba ni tabbacin bai sanar da kowa cewar ya shigo ƙasar ba ciki kuwa har da matarsa uwar ƴaƴansa". Na ja dogon numfashi na fesar ina jikina gabaɗaya ya yi sanyi ƙalau tamkar kazar da aka jefa da ruwan gishiri. Lokacin sallan magrib da ya kawo kai shi ya tursasa mini tashi na fita na je na yi alwala na dawo na gabatar da sallan, ban tashi daga wajen ba sai da na yi sallan isha'i. A lokacin Zinariya ta jawo ledar da ta dawo da shi ta ɗauko wayar ta kunna ta, kamar jira ake yi ta kunna sai kuwa ga ƙira ya shigo ta. Ta ɗaga tare da sanya ta a amsa-kuwwa ta kwanta akan bayanta ta ɗaura wayar akan ruwan cikinta yayin da ta lumshe idanunta. "Yau ina kika shiga ne kwana da kwanaki? Ina ta ƙiran layinki ba ya tafiya. Ko dai wani harkar kika saita ne kika juya mana baya? Don na san halinki kamar yadda na san yunwar cikina". A taƙaice ta ce"wannan wani dogon labari ne mai zaman kansa. Amma dai yanzu fara sanar da ni dalilin neman da kake yi min". "Malamin da kuke son ganin yanzu haka maganar da nake yi miki yana cikin otel ɗin mu. Ya zo shi bikin ƴar gidan mataimakin gwamna da za a yi don na ji a wata majiya mai tushe cewar shi zai ba ta auren yarinya, ma'ana shi ne waliyinta. Ku na da damar da za ku iya ganinsa daga nan har zuwa ranar da za a ɗaura auren". Babu shiri ta tashi ta zauna tare da buɗe idanunta"Oga Deeno mu bar wasa shin da gaske kake wannan maganar?". Ta ja wata doguwar tsakin haushi da takaicin ta da ɗura masa kafin ya ce"ta yaya zan yi miki wasa da irin wannan zancen? Na yi miki abin da kike so yanzu ni ma lokaci ya yi da za a rama wa kura aniyarta". Dariya ta fashe da shi"kar ka damu Oga zan zo takanas na same ka". Da hakan suka yi sallama ta katse ƙiran ta zo ta ƙanƙame ni. "Burinki ya kusa cika Amatullah. Sheikh ya zo cikin garin nan kuma ina da tabbacin Oga Deeno zai share mana duk wani hanyar da zai sada mu da ganinsa". Wani sanyi na ji a cikin zuciyata na ji tamkar an warware mini ƙullin da ya tokare mini ƙirjina ban san lokacin da na ɓanɓare ta daga jikina, na kai goshina ƙasa na yi sujudul shukur ga Ubangijina ba ina hawayen farin ciki. [12/15, 5:32 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam _______________________________________ Page 7️⃣0️⃣ Duk yadda na so tsayar da hawayen da suke sarrafa kansu wajen zuba daga cikin koramar idanuna, na kasa samun wannan damar. Sosai nake kukan irin kukan da na daɗe ban yi makamancinsa ba, sai dai na yarda hakan yana da nasaba da abubuwan da suka taru suka yi wa zuciyata ƙawanya. Ban san sama zarafin zubar da ƙwallar ba sai yanzu ta dalili ya yi dalili. Zinariya ta tsaya ta yi sakeke tana kallona. Ta kai hannunta tana share mini hawayen da suka ɓata mini fuska. "Ke kuwa mene ne abin kuka? Wannan ai abin farin ciki ne da ya kamata ki tashi ki yi tsalle har ma ki tada rawa tun da daman buƙatar maji hajji ai salla ne". Ban iya tanka mata da kalmomin da baki kan iya furtawa ba illa murmushin da na yi ƙoƙarin sakar mata ita ma ta mayar mini. Na rungume ta tsam a jikin ina ta faman jeranta mata godiya wani na bin wani kai ka ce kyautar kujerar hajjin bana ta ba ni a lokacin nake tsanani da buƙatar hakan. "Ba kuka ya kamata ki yi ba Amatullah murna da murmushi ne ya dace da fuskarki a irin wannan lokacin na tsananin farin ciki da taka tsanin cikar buri da muradin da ya daɗe a cikin farfajiyar ƙirjinki. Ki goge idanunki ki nutsu mu tsara yadda abubuwa za su kasance har su tafi daidai da tsarinmu. Ba tare da an sama wani matsala ba". Numfashi mai nauyi na furzar daga bakina tare da gyara zamana ina fuskantarta kafin na yi magana ta tari numfashina ta hanyar faɗin"to yanzu me ne tsarinmu na gaba?". Na ɗan yi jim tamkar mai nazarin kafin na ce"idan na gan sama ganinsa to dukkanin burina ya cika sannan haƙata ta cimma ruwa". Ta yi mini wani kallon da na kasa fahimtar inda ta dosa. "Me ye hakan yake nufi ke nan? In kika gan shi kawai shi kenan komai ya zo ƙarshe? Babu wani abun da za ki yi? Kin san ba shi ma ba zai zauna haka nan dole ne ya kasance da shirinsa na ko ta kwana". "Ba a suffar Amatullah ɗin da kika sani zan je masa, zan je masa ne a suffar irin matan da yake harka da su duk da cewar kuwa duniya ba ta san wannan ɓoyayyan halin nasan ba". Ta yi caraf ta amshe zancen"ta ya ya za ki yi hakan?". Ta murmusa kana na ce"Allah ya kai mu gobe idan muka je cikin otel ɗin za ki ga ne wa idanunki. Bayan mun haɗu da shi mun zanta zan naɗi sautin muryarsa sannan ban shayar da shi abin maye ta yarda zai fita daga cikin hayyacinsa. Hakan ne zai ba ni damar yin abin da na yi niyya zan ɗauki hotona da shi, wanda su zan riƙe a matsayin makaman da zan yaƙe sa da su. Har na kawo ƙarshen baƙi hali da mungun nufin da yake yaɗawa a tsakanin al'umma a ɓoye". "Kuma ki na ganin bayan faruwar hakan ba zai sa a bazama nemanki ba ruwa a jallo?". "Idan ya yi hakan to shi ne kuskuren farko da zai yi da zai yi silar tonuwar aisirinsa ga duniya gabaɗaya. Sai dai ya yi hakan ma akwai ɓoyayyar hanyar da zan ɓullo masa". Ajiyar zuciya mai nauyi da sauti ta saka yayin da take bi na da kallo, ko ba ta furta mini ba na fahimta kuma na kallon shakku game da maganan da na furta kwance a cikin idanunta da suka ƙanƙance. Na riƙo dukka hannayenta na sanya cikin nawa ina murzawa a hankali. "Ki kwantar da hankalinki in sha Allah ina ji a jikina Allah zai ba mu nasara akan wannan abun. Kamar jahadi ne fa za mu yi wajen tona asirin abin da yake aikatawa a ɓoye wanda haramci ne hakan". "In sha Allah zan kasance da

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});