Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 36

Chapter 36

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,209 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tana zaune tana shan shayi na iske ta jifa-jifa tana latsa wayarta, na yi mata sannu kana na wuce ɗakin Altine bakina ɗauke da sallamar da ban sama amsa daga gare ta ba illa kallon banzan da ta bi ni da shi har na isa na zauna a bakin katifar. "Ga can abinci a kula ki ɗauka". Kaina kawai na gyaɗa mata na jawo hular da ta yi mini nuni da shi. Ina buɗe wa na ci karo da farar shinkafa da ta gama shan iska ta bushe ƙararau ga wani ɗan yajin da aka yafa a gefen tamkar wanda aka roƙo daga maƙota. "Abincin waye wannan ɗin? Ko a karnuka za a ba wa?". "Tun da kike zuwa gidan nan kin taɓa ganin kare ne?". "To na sani abu a duhu. Don wannan abincin kam ai ɗan Adam dai mai rai da numfashi ba zai iya cin sa ya kwana lafiya ba sai dai dabbobin. Hasalima ai na ga ba wannan nau'in abincin aka girka ba". Tun kafin na rufe bakina take bi na da wani irin kallo tamkar za ta rufe ni da duka. Sai da ta tashi ta zauna daga kishingiɗewar da ta yi kafin ta soma amayar da balbalin wutar zancen da yake cikinta. "Ke har kin isa ki tisa ni a gaba ki na tuhumata akan abin da kika gani a cikin ƙwaryan tuwonki?. Ina da karfin iko a cikin gidan nan fiye da duk yadda kike tunani da hashashe, idan har kika bari na juyo kanki na saka miki ƙahon zuƙa billahillazi hatta numfashi mai kyau ma sai a gagare yi a cikin gidan balle kuma wasu abubuwan". Na lanƙwasar da murya kafin na furta"tuba nake yi ranki ya daɗe. Ai ni ban isa na sa kafar wando ɗaya dake ba wane ni ubana dillalin Kashi. A yi mini aikin gafara". Wani tsaki mai dogon zango ta saka tana jifa na wani irin mungun kallo kwatankwacin irin kallon da mai dukiya yake yi wa ƙasƙantacce. Na sakar mata da wani lausassan murmushin da har sai da haƙwarana suka bayyana na jawo kulan abincin gabana na sa hannu na soma ci. Duk da yanda shinkafan yake sukan wuyana ina jin suna tsayiwa a maƙoƙarona hakan bai hana ci ci gaba da tura abincin ba. Na fahimci matuƙar ina son na cimma buri da muradina akan ta sai na kwantar da kai na yi mata biyyaya domin sunkuyawa gwada bai taɓa zama gajiya wa ba. Sai da na cinye abincin tas na ɗauki kular na fito waje na kai ta kicin inda a nan na sama ruwa na kwankwaɗa na sama sauƙin tsayuwar ƙayan kifin da shinkafar ta yi mini a hanyar wuya. Na ji wani abu ya taso mini cikina ya murɗa tae na ji amai ya taso mini da hanzari na fita ta ƙofar baya na dinga kwarara amai tamkar zan amayar da dukkan kayan cikina. Sai da na gama na tashi na je na kwance baki da fuskana na zo na gyara wajen da na yi amai ɗin, gabaɗaya jikina babu ƙwari haka na baro cikin kicin ɗin na dawo ɗakin Altine ban iske ta a cikin ɗakin ba hakan ya ba ni daman kwanciya akan katifar ina mayar da numfashi jin jikina nake yi gabaɗaya ya mutu tamkar wacce aka yi wa ɗan banzan duka. Muryar Taufik da na ji ɗazu a sashin Saif ya soma dawo mini cikin kwanyata tiryan-tiryan na lumshe idanuna da hakan ya ba wa hawaye da suka ciko mini koramar idanuna damar kwaranya a bisa fuskana. Wata zuciyar tana raya mini ina ma da na tsaya na laɓe na ga ko da fuskarsa ce, duk da muryarsa ma kaɗai ta tabbatar mini da cewa shi ɗin ne dai, na ja dogon numfashi na fesar kafin na gyara kwanciyata na kwanta akan gadon bayana ina kallon rufin ɗakin da ya zama mini shamaki tsakanina da sararin samaniya. Na yi nisa a cikin tunanin nake yi da har ban san lokacin da Altine ta shigo cikin ɗakin ba balle tsayiwar da ta yi a kaina kamar wacce ta haɗiye taɓarya babu alamar ranƙwafawa a tattare da ita. "Kwanciyar me ye kike yi a nan ɗin?". Na cira kai ina dubanta kafin na ce"jikina ne gabaɗaya yake yi mini ciwo shi ne na zo na ɗan kwanta ko zan ji dama-dama". "Ai kuwa kwanciya ba ta kama ki ba ke da kika fito neman kuɗi. Ki tashi ki je Hajiya tana ƙiranki". Ban ce da ita komai ba na tashi ina cije leɓe na fita na je ƙiran Hajiyar na iske ta tare da wasu mutane uku biyu maza ɗaya mace gefe guda ga tulin turamen atamfa an jibge su da lesuka, suna ta buga lissafi gami da rubuce-rubuce. Na durƙusa na gaishe su suka amsa mini fuskarsu babu yabo babu fallasa kafin na ce"Hajiya ga ni an ce ki na ƙirana". "E sashin Saifullah za ki je ki gyara masa sun fita tare da baƙonsa. Ki gyara kafin ya dawo". Gabana ya faɗi ya yi ras na ɗan saci kallonta kafin na kai ga faɗin"Hajiya shi ya buƙaci hakan? Don na ga kamar ba ya jin daɗin zuwa cikin sashinsa da nake yi". "Ba shi ya buƙata ni ce dai kawai na ga dacewar hakan, na san halin Saif sarai yana da wuyar sha'ani amma da zaran kin fahimci wane ne shi za ki gano tana da daɗin zama da tarin hayalen ƙwarai". Kaina kawai na jinjina na ce"to". Na tashi na nufi sashin ƙirjina yana tsananta bugu da harbawa. Na isa cikin sashin ban dawo cikin ainihin nutsuwata ba, na soma tattare falon da ko kwanunkan da aka ci abinci da kofuna yi tea ɗin ba a kwashe ba. A bayyane na tsirtar da wani tsiririn tsaki na takaicin da ya taru ya yi mini yawa, ina ƙara yarda da maganar nan da ake cewa na duk na mijin da ka gani a hanya tsaf tsaf kar ka yi saurin bakin furta yana da tsafta ɗari bisa ɗari, har sai ka ga makwancinsa sannan ka yanke hukunci. Na ɗauko tsintsiya na share ko'ina na yi mopping na mayar da komai a cikin muhallinsa. Wasu takardun addinin da suke kan kujera na ɗauka zan mayar da su kan teburi na yi tuntuni da bakin kafet takardun suka zube daga hannuna, na runtse idanuna sa boda zafin da na ji ya ratsa har ciki kwayata, na tashi na ina tattare takardun da suka watsa na ci karo da wani hoto, na ɗauka zan mayar da shi cikin takardan tautsayi ya sanya idanuna sauƙa akan hoton. Take numfashina ya ɗauke na wucen gadi na sanƙare a wajen na gaza motsa ko da gaɓa ɗaya daga cikin jikina, illa idanun da na ƙura wa hoton jikina yan rawa tamkar an jona mini wutar lantarki. Hoton Sheikh Dawood Gaskiya dokin ƙarfe na gani tare da Muhammad Taufik cikin shiga riga ɗaga, ga wani ƙaramin yaron da ba zai haura shekaru uku a duniya ba. Hoton ya yi bala'in kyau tare da fito da su suka yi tar da su, fuskokinsu washe da maɗaukakin farin cikin da ya bayyana ƙarara. Jikina gabaɗaya ya soma rawa da har ban san sa'ilin da na zame na

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});