Chapter 85
Chapter 85
kanki cikin wani irin yanayi da zai shafe mu daga ke har mu. Rayuwar nan fa da kike ji da gani ba ta taɓa tafiya a miƙe tsalin ƙalin dole sai an bi ta tudu da gangare sai an haɗu da ƙalubanale kala-kala, sai an yi katari da jarabawa mai sanya rauni a cikin zuciya. Ko wani Bawa da irin na shi salon ƙaddaran a cikin wannnan rayuwa. Don Allah na roƙe ki cire komai daga cikin ranki ki fawwalawa Allah dukkan lamuranki ki miƙa wuya gare shi ki sakankance cewa duk abin da ya zartar a gare ki hakan shi ne daidai, domin babu kuskure a cikin hukuncinsa". Tun da ta fara zancen na sadda kaina ƙasa ina sauraron ta ba tare da na katse ta har sai da ta kai aya. Muryata ba ta fita yadda ya kamata na ce"Anty Zulaihatu abin da nake ta ƙoƙari ke nan, na cire damuwar da ya yi kane-kane a cikin zuciyata ni ma ina so na yi rayuwa cikin walwala da annashuwa kamar yadda kowa yake yi. Sai dai wallahi ko na ɗauko aniyar aikata hakan sai na ji na kasa, ba na ma sanin lokacin da tunanin yake zuwa mini balle na ankare da sa'ilin da ruwan hawaye yake kwaranya daga koramar idanuna". A raunane na ƙarshe zancen ina jin ƙirjina ya yi mini nauyin gaske tamkar wacce aka yi wa ajiyan wani gingimemen dutse. "Haƙuri za ki yi Amatullah watarana sai na labari, komai zai zo ya wuce tamkar bai taɓa faruwa". Kaina kawai na gyaɗa mata ina kwantar da kaina a bisa kafaɗanta da hakan ya ba ta damar kai hannunta tana shafa sumar kaina a hankali. "Yanzu da na zo ni Umma take sanar da ni wani abun alkhairi da farin ciki kuma". Cike da tashin fahimtan zantukan natan na ce"wani abu ke nan?". Sai da ta murmusa kafin ta furta"ta sanar da ni cewar akwai wanda ya zo cikin gidan nan neman soyyayarki ko kuma kai tsaye na ce aure ne ya kawo sa, don bai zo da wasa. Amatullah kin ga duk mutumin da ba ya shakkan haɗuwa da magabatan yarinya to haƙiƙa wannan mutumin ɗan gidan mutunci ne kuma zai yi wahala ya yaudare ta. Ki ba shi dama ki fahimcie shi ta nan ne za ki gano cancantarsa ko kuma akasin hakan, idan har kika ji ya kwanta miki a cikin rai to kawai ki amince masa ya turo a zo a yi magana". Tun da ta soma magana na yi laƙwas ban ce komai ba har sai da ta kai aya. Cikin raunin da ya bayyana har a cikin kalaman da bakina ke furtawa na soma magana cikin rawar murya da ya haddasa rashin fitar sautina sosai. "Anty yanzu ke ma ki na goyan bayan na yi aure a cikin wannan yanayin da nake ciki? Ina buƙatar kwanciya da nutsuwa kafin a kawo mini wani maganar da ya danganci aure ko soyayya, sannan wannan mutumin ya wulaƙanta a lokutan baya ya zarge ni da abin da ban aikata shi hasalima ko kusantansa ban yi ba". "Abin da ya riga ya wuce ya wuce Amatullah ki fuskanci yau ɗinki da kuma abin da gobe za ta haifar. Rayuwa ta kan zo da abubuwan da mu ƴan Adam ba mu taɓa zato ba balle tsammanin faruwarsa. Duk wani kwanciyar hankali da nutsuwan da za ki sama ba zai kai na cikin gidan aurenki wanda za ki samu daga wajen mijinki ba". Sai da na jinkirta ba ta amsa sa boda nauyin da bakina ya yi mini kafin can na ce"Anty kin mata da cewar Yaya Alhassan ma ya taɓa zuwa gare ni da irin wannan buƙatan? Shin ina ganin na kyauta masa idan na amince wa waninsa? Ki na tunanin na yi masa adalci na kuma saka masa idan na ba wa wani da muka haɗu da shi rana tsaka kyautar zuciyata alhali shi ya san dukkan ɗawainiyya ta?". Numfashi mai ƙarfi ta fesar daga bakinta kafin ta sama zarafin faɗin"Amatullah idan aka zo batu na aure ba na duba dangantaka, ba a duba kusanci, ba a duba alaƙa daɗaɗɗiya ko kuma sabuwa, haka nan ba a yin kara balle kawaici. Fito wa ake yi a fallasa sirrin da yake cikin zuciya ko da kuwa zuƙata da yawa za su ɗanɗana romon baƙin ciki. Don shi aure da kike gani ba zaman lokaci ɗaya ba ne, ba zan wuni guda ba ne zama ne na dogon zamani da ake fatan ya ɗaure har abada, kuskure mafi girma da mace za ta yi shi ne ta zaɓa abokin rayuwa wanda bai dace da ita ba to tabbas za ta dawwama ne cikin ƙunci da baƙin ciki. Don haka ina mai ba ki shawaran ki yi addu'a ki roƙi Allah ya zaɓa miki mafi alkhairi tsakanin Yaya Alhassan ɗin da kuma wannan baƙo, duk wanda kika gabatar mana tabbas da shi za a yi mu zo mu sha biki har mu yi rawa da juyi". Maganarta ta ƙarshe ta jefa ni a cikin kunya, na yi saurin ɗauke kaina daga saman kafaɗanta na rufe fuskana da tafukan hannayena na fice daga cikin ɗakin, ina jin ta tana dariya tare a ƙiran sunana amma kuma waigowa ban yi ba balle na tanka mata. Ina fito wa falo muka yi kiciɓus da Yaya Alhassan yana shigowa take na sha jinin jikina na yi wani irin kunyarsa nauyinsa sun lulluɓe ni, na tako na iso cikin falon na gaishe shi yayin da yake zama akan ɗaya daga cikin kujerun da suke jere reras a falon. "Yaya Alhassan daman ina ta so na yi maka godiya waya, sannan kuma akwai maganar da nake so mu tattaunawa da kai". "Babu godiya tsakaninmu Amatullah kamar yadda ba zan cire kuɗi na yi wa Amir ko Umar da suke ƙannena ba tare da na yi komai a cikin raina ba, to ke ma haka nake tsintar kaina a cikin irin wannan yanayin a duk lokacin da na yi miki wani abu". Kaina na jinjina cike da gamsuwa don ni ma katan kaina shaida ce akan irin tari soyyaya da kulawan da yake nuna mini da yau na gaza samun abin da zan saka musu da shi. Sai da na sauƙe ɓoyayyan ajiyan zuciya mai nauyi kafin na zama zarafin faɗin"daman na so mu yi magana akan Saifullah da ya zo cikin gidan nan da buƙatan aurena idan har na amince". Ya yi hanzarin katse ni ba tare da na ƙarisa ba ta hanyar faɗin"wani magana za mu yi akan hakan? Ai idan har kin ji ya kwanta miki a cikin ranki to shi kenan kawai an gama magana". "Na san da haka sai dai idan ba ka manta ba kai ma ta taɓa zuwa mini da makamancinyar irin wannan buƙatan a lokacin baya, sai nake ganin.......". Ya ɗaga mini hannu alamar ba dakata hakan aka yi kuwa na yi tsit tare da sadda kaina ƙasa. "Wannan kuma wani abu ne da ya riga ya wuce bai dace ki na tuno shi a daidai irin wannan lokacin ba, na yarda duk abin da ban samu ba to haƙiƙa daman Allah bai ƙaddara cewa yana daga cikin rabona ba. Ina miki fatan samun rayuwa mai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98