Chapter 76
Chapter 76
ƙafa da ƙafa ya zo shi har cikin gidan nan don kawai ya yi mana gaisuwa to mu mutunta juna. Su yi abin da ya kawo su mu watse". Hawaye ne kawai yake ta ambaliya a fuskana ina faɗin"Anty a duniya babu mutumin da ya taɓa gayyaya mini baƙaƙan maganganuna, ya suffanta ni da abin da ko kusa ban aikata shi ba kamar wannan mutumin. Har yanzu idan na rufe idanuna ina tuna munanan kalamansa gare ni". Shuru ya biyo bayan zancena na ƙarshe har na tsawon wani lokaci kafin can na tsinkayo muryar Saif ya sauƙa a cikin kunnuwana. "Tabbas duk abin da kika faɗa haka ne babu kuskure ko ƙage a cikinsa, na aikata miki abubuwa da dama na zarge akan abin da ba ki aikata ba. Sannan akan idona aka wulaƙanta ki na kasa cewa komai. Sai dai duk da hakan ke ce mace ta farko da ta fara kawo mana ɗauki a cikin rayuwarmu ta warware mana wani babban ƙullin da duk ba mu san shi ba. Ranar da kika sanar da mu wannan abun washe gari na tafi garin Abuja na sauƙa a wannan otel ɗin da kika ba mu bayanansa, haƙiƙa na gane wa idanuna abun mamaki don da idona na kama Yaya Saddam da karuwa su na kwance a cikin ɗakin otel ɗin. An yi rikici sosai har sai daga bisani Anty Muhibbat ta ji komai ta bi mu can Abujan sai dai ga mamakina ko kaɗan ba ta ga laifin Yaya Saddam ba sai ma ƙoƙarin ba shi kariya da take yi ta ko wacce fuska. Hakan ya jefa ni cikin tunanin da na baza ma nemon gaskiyar da yake ƙunshe ƙasan kalaman kariyar da take ba wa Yaya Saddam. Nan na gano cewar kafin aurensu ita ɗin budurwan marigayi abokinsa ne watau Yaya Usman da suka yi wa junansu alƙawarin aure tun suna jami'a, wannan dalilin ya sanya suka mayar da kansu tamkar miji da mata ta hanyar biyawa junansu buƙata ba tare da shakkan kowa da komai ba. A lokacin Yaya Saddam ya san komai aka tsaka da wannan lamarin Allah ya karɓi rayuwar Yaya Usman a lokacin Anty Muhibbat tana ɗauke da cikinsa, a sa'ilin da ta sanar da Yaya Saddam da ake ciki ya shiga cikin matuƙar tashin hankali ya nema a zubar da cikin amma ta nuna hakan ba zai taɓa yiyuwa hasalima ko dai ya aure ta ya rufa mata asiri ko kuma ta je ta bayyanawa ita mahaifiyar Yaya Usman ɗin halin da ake ciki". Ya dakata ta hanyar jan dogon numfashi ya fesar kafin ya ɗaura daga inda ya tsaya"idan akwai wanda mahaifiyar Yaya Usman ta yarda da shi ta kuma aminta da shi to a bayan Yaya Saddam yake. Wannan matar ta taka rawan gani a cikin rayuwarmu gabaɗaya, a gidanta ya yi karatu ba ta taɓa nuna masa bambamci tsakaninsa da ƴaƴan da ta haifa ba, hatta ni ta nuna min so da ƙauna lokacin da iyayenmu suka rasu ta ja mu a jikinta ta maye mana gurbin duk wani abun da muke jin cewar mun yi rashinsa. Wannan dalilin Yaya Saddam ya dubae har ya abin ce da auren Anty Muhibbat bayan sun yi yarjejeniyar za a zubar da jikin da take ɗauke da shi. Ba na mance kukan farin cikin da mahaifiyar Yaya Usman ta yi lokacin da ta ji cewar Yaya Saddam ne zai auri Matar da Yaya Usman ya so aura Allah bai yi ba. Ta yi hidima sosai a bikin har Allah ya ƙaddara musu kasancewa a matsayin mata da miji har da rabon haihuwar Aryan da Ayan. Sun yi auren ne kawai amma Anty Muhibbat ta san cewa babu ko da ɗigon soyayyarta a cikin zuciyarsa, tun daga wannan lokacin zuciyarta take ayyana mata cewar za ta jure komai daga gare sa don dai kawai wannan sirrin da suke rufe bai fito duniya kowa ya ji ba. Don ya kasa yarda da ita duk da kuwa mutuwar Yaya Usman ya sanya ta sauya". Al'ajabi da mamaki suka taru suka hana mu magana daga ni har ragowar mutanen da suke zaune a cikin falon. Anty Sawwama ta yi ta jinjina lamarin tare da yi mana nasiha mai ratsa jini da jijiya ta ƙarƙare da jan hankulanmu akan mu ji tsoron Allah a cikin dukkan abin da za mu aika. Har aka gama komai ban ɗago kaina ba balle na ce wani abu aka gabatar da addu'ar neman gafara da rahama ga Ummata kana suka fara haramar tafiya. Ko cira kai ban yi na dube su ba sai jin Muhammad Taufik na yi tana magana da Yaya Alhassan cikin girmamawa. "Yallaɓai idan babu damuwa mu na son magana da Amatullah a waje". Ba tare da nazari ko dogon tunanina ba Yaya Alhassan ya furta"ba komai ai, mu je daga wajen sai ta fito". Daga haka suka fuce. Anty Sawwama ta dafo kaina da na kwantar jikin ƙafafunta"tashi ki je ki ji abin da za su gaya miki". "Me ye kuma za su ce mini Anty? Duk abin da za su faɗa ai sun faɗe shi a cikin falon nan. Gaisuwar rasuwa suka zo yi kuma sun yi mene ne kuma ya yi saura?". Cikin lallashi ta ce"ki yi haƙuri ki tashi ki je ki ji abin da za su ce da ke kin ji Uwata?". Ba don raina ya so ba na tashi na nufi wajen ina goge guntun ƙwallan da yake ƙoƙ zubowa daga cikin idanuna. A ƙofan gida na iske su tare da Yaya Alhassan da Amir na iso wajen bakina ɗauke da sallamar da suka haɗe baki wajen amsawa. Yaya Alhassan da Amir suka yi musu sallama ta hanyar yin musabaha kana suka koma cikin gidan suka bar ni tsaye da su. Kusan mintuna biyu cikinmu babu wanda ya yi magana kafin can Saif ya ce"daman godiya nake so na yi miki sannan kuma na ba ki haƙuri akan duk abubuwan da suka faru, haƙiƙa na aikata miki ba daidai ba". Ban bar shi ya ƙarisa ba na ɗaga masa hannu alamar ya dakata. "Kamar yadda tun a ciki aka buƙaci na manta da duk abin da ya faru, to ka ƙaddara cewa komai ya wuce". Ya sadda kansa ƙasa yana murza zoben dake saƙala a ƴatsun hannunsa kafin ya ce"na gode". "Amatullah". Muhammad Taufik ya furta a karo na farko tun bayan da na fito waje, na ɗaga idona ina kallonsa yayin da shi ɗin ma ni yake kallo, take na ji wasu hawaye su na bin kuncina ba zan iya juran irin kallon da yake yi mini ba don haka na juya na shige cikin gida da hanzari, kai tsaye ɗaki na wuce ina shiga na faɗa kan katifa ina kuka marar sauti. Haka na wuni a cikin ɗakin in a fito waje to alwala zan yi ina yi nake koma wa cikin ɗakin. Washe da safe bayan mun yi karin kumallo ina zaune a ɗaki kawai na ji an yi sallama, idanuna a lumshe na amsa sallamar da hakan ya ke daida da ba ta iznin shigo wa. "Amatullah". Take na wartsake na tashi na miƙe tsam sa boda amon muryar ba ta kasance baƙuwa ga kunnuwana ba. Na ware idanuna akan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98