Chapter 19
Chapter 19
ajiye kulan na shiga banɗakin dake cikin ɗakin na wanke hannuna na fito. "To Anty ni zan tafi, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu". Kamar wacce aka yi wa dole ta ce"Allah ya tashi mai gaskiya". Na saki taƙaitaccen murmushi kana na ce"Amin ya Allah". Na bar cikin ɗakin na iske Hajiya a inda muka bar ta har yanzu tana latsa wayarta ta saka wani waƙan yaren turanci tana bi tamkar tare da mawaƙin suka rera waƙar tsabar ƙwarewar bin dukkan baitukan waƙan da ta yi. Na iso na durƙusa a gaban ta"Hajiya na fito zan tafi". "To ki gaida gida, ga wannan sai ki yi kuɗin mota da shi". Ta ƙarƙashin zancen tana miƙo mini naira ɗari biyar na kuɗin ƙasata Nigeria. "Na gode sosai Hajiya amma ba zan iya karɓan wannan kyautar ba ba kuma don na raina ba. Zan fi so duk ƙarshen wata a ba ni haƙƙina na yi amfani da shi, ina ga kamar hakan zai fi amma idan maganganuna sun ɓata miki rai to ina mai ba ki haƙuri". Kafin ta ce wani abu Aryan da Ayan suka shigo da gudu suna rige-rigen isowa gare ta, ta buɗe hannayenta suka faɗo jikinta suka ƙyalƙyalewa da dariya. Ina ɗago kaina muka haɗa ido da shi yana shigowa hannunsa riƙe da wasu manyan ledodi guda biyu, na yi hanzarin rusunar da ƙwayoyin idanuna ƙasa. Ya shigo ya zauna kafin ya yi magana Hajiya ta riga sa"ina kuka je ne haka?". "Kun fita wani waje ne". "Wajen bai da suna?". Kafin ya yi magana Aryan ya karɓe zancen"Ammi wajen wasan yara muke ce, daga nan muke je muka ci abinci sannan ya kai mu ya yi mana siyayya, muka tsaya a masallaci muka yi salla kafin muka dawo gida". "To kin ji amsa daga bakin uban masu gidan". Dariya duk su biyun suka yi kafin ya miƙe"sai da safenku ni kam zan wuce sashina". "Kafin nan ga Amatullah ka mayar da ita gida na ga dare ya yi za ta sha wahala kafin ta sama abin hawa. Daga nan ma sai ka gano gidansu ko don gaba". Ya tsaya sakeke kafin ya furta"wace ce kuma Amatullah?". "Ga ta". Ta amsa masa tana masa nuni da inda nake durƙushe, ya ɗan shafo sumar kansa kana ya ce"har yanzu fa akwai ababen hawa suna hada-hadan su, tana fita za ta samo har ƙofan gidan". Cikin kakkauran murya da tsare gida Hajiya ta ce"Saifullah in ba za ka yi ka fito fili ka sanar da ni, ba sai ka yi wani kwana-kwana ba". Ya sunkuyar da kansa ƙasa ciki-ciki ya ce"ina jiranta a waje". Tana gama faɗin haka ya juya ya fice daga cikin falon. "Tashi ki je yana jiran ki". Na ɗago kaina zan yi magana ta tari numfashina"kar ki ce komai, idan ba hakan zai zama takura a gare ku ba ne to kawai ki je ya kai ki". Jikina a sanyaye na tashi na yi mata sai da safe na fita, ina fitowa na hango sa tsaye a jikin mota yana danna waya muna haɗa ido da shi ya buɗe ƙofar motar ya shiga. A hankali na iso na buɗe ƙofan motar zan shiga ya dakatar da ni ta hanyar cewa"gidan gaba za ki shiga". Na mayar da ƙofan na rufe na buɗe na mai zaman banza na shiga na zauna, ina rufe ƙofan ya ja motar tunin daman mai gadi ya wangale gate ɗin, a hankali yake tafiya akan shimfiɗaɗɗan titin da babu cunkoson ababen hawa balle hayaniya. A ƙalla ya yi tafiyan da ya kai na mintuna ashirin ba tare da ya tambaye ni ina unguwanmu ko kuma inda zai ajiye ni ba. Gabaɗaya na ƙagu da zaman ga wani tarin gajiyan da nake ji a cikin jikina kamar an yi mini dukan tsiya, muryata cike da tarin tsoron da ya yi mini dabaibayi na ce"idan ka sama waje zan sauƙa". Kamar ba zai amsa ba sai kuma ya ce"har mun iso gidan nakun ke nan?". "A'a zan ƙarisa nan ne ba wani nisa ba ne sosai". Yana kayar kwana ya ce"akan idonki amma aka ce na kai ki gida, na ga gidan gudun watarana". Daga nan ban ƙara cewa da shi komai na zuba masa idanuna domin na ga gudun ruwansa, haka ya ci gaba da tafiyan har gyagyaɗi ya soma ɗeba ba. Hawayen takaici da dana-d shiga motarsa da na yi suka kwaranyo mini. Na kai hannu na goge su ina jin zuciyata tana tafasa kamar talge na ji ya taka birki motar ta tsaya. "Fita". Na yi ya furta muryarsa babu alamar wasa balle wargi, na ɗago ido domin ganin inda ya tsaya. Da mamakina ina ɗago ido na hango ƙofar gidan Hajiya Babba da ya cika ya yi maƙi da samari da ƴan mata suna sheƙe ayarsu tare da cin karensu babu babbaka. "Ki fita mana. Ko ba nan ba ne ƙofar gidan?". Na sadda kaina ƙasa"nan ne, na gode". "Ki gode wa Allah". Ban iya amsa wa saboda mamakin da ya shayar da ni. Na fito na tsaya na kasa gaba na kasa baya idanuna akan motan har sai da ya ɓace wa ganina. Na sauƙe tagwayen ajiyan zuciya tare da jefa wa kaina tambayar da na kasa amsa wa. Ya ya aka yi ya san cewa a cikin gidan nan nake rayuwa, har ya kawo ni?. [12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ___________________________________________ Page 5️⃣0️⃣ Na daɗe tsaye a wajen ina saƙa da warwara a cikin raina, kafin na ja ƙafafuna na bar wajen sai da na raɓa tamkar zan shige cikin gini kafin na sama hanyar da zan wuce saboda kuncoson da yake ƙofar gidan, mutane kamar ana kaɗa ƙararrawa suna fitowa sun cika wajen sun yi maƙil. Ga wanda bai sa ni ba sai yi tunani da zaton wani gagarumin taro ake yi a wajen. Har cikin tsakar gidan da mutane kamar ba dare ba ina shigowa na hango La'aniyatu zaune a ƙofan ɗakinsu, na isa kusa da ita na zauna ina kafa hannayena wajen guda da hakan ya ba da wani ɗan sautin da ya dawo da ita cikin hayyacinta daga tunanin da ta yi nisan kiwo a cikinsa. "Yaushe kika dawo?". "Lokacin da kika yi nisa cikin tunanin da kike yi na shigo". Ta miƙe ba tare da ta ce komai ba ta shiga cikin ɗakinsu babu jima wa ta dawo ta miƙo mini ɗan makulina. Na karɓa ba tare da mun ce da juna ko kanzil ba na je na buɗe ƙofana na shiga buta na ɗauka na fito na yi alwala kana na koma ciki na gabatar da sallan isha'i, ban gusa daga inda na yi sallan ba na zabga uban tagumi ina tunanin abubuwan da suka wakana a cikin wunin yau gabaɗaya. Babu shiri na sauƙe numfashi mai zafi ina cije naman leɓena. Ban san sa'ilin da hawaye suka fara tsere a bisa fuskana ba suna sauƙa har izuwa saman haɓana tare da zarcewa zuwa tudun wuyana, ban share su ba kamar yadda ban yi wani yunƙurin hana su kwaranya ba don na yi imanin zubar da su ne kawai zai sanya na ji sanyin tafasar da zuciyata take yi mini da kuma ɗacin da nake
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98