Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 32

Chapter 32

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,221 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ba tare da na san dalili ba [12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam __________________________________________ Page 5️⃣6️⃣ Duk yadda na so na furzar da zallan mamakin da ya ganin sa ya ƙunsa mini bakina ya ƙi ba ni haɗin kai wajen aiwatar da hakan a aikatace, da ɗago idona ina kallonsa na ga ya watsa mini wani mummunan kallo da ban san sa'ilin da na rusunar da idanuna ƙasa ba. Sa boda cika ido da kwarjinin da yake da shi. "Zan jira ki a wajen motata ba zan iya tsayiwa a nan wajen ba". Yana gama maganar ya bar wajen ya nufi inda ya ajiye motar da yake can farkon layin na bi shi a baya zaƙwai-zaƙwai har muka isa ya jingina bayansa jikin motar tare da naɗe dukkan hannayensa a ƙirjinsa idanunsa a kaina ya furta"Anty ce ta ce a zo a duba ko lafiya kika tafi ba tare da kin yi mata sallama ba. Sai dai zuwan da na yi da kuma abin da idanuna suka gane min ya tabbatar min da cewar lafiya kike tun da har za iya fitowa ki gana da saurayi cikin wannan daren har da guzurin saƙo niƙi-niƙi a leda". Jikina ya yi sanyi ƙalau wasu hawaye suka kuma ciko mini idanuna sauran ƙiris su zubo na kai hannu na tare su. "Lafiya ƙalau kawai ba na jin daɗin jikina ne shi yasa na dawo. Amma ina sha Allah gobe sammako zan yi na zo.....". Tun kafin na kammala ƙarshen zancen ya tari numfashina. "Ba ma buƙatarki don haka ki yi zamanki. Idan ma ya zama dole to za a nema wata". "Ba kai ka ɗauke ni aiki ba ranka ya daɗe don haka ba ka da hurumin dakatar da ni, Hajiya ce kawai take da wannan ikon". Tabbas na hango mamakin zancena kwance a cikin idanunsa ya sauƙe numfashi da har sai da na ji sautin fitarsa. "Repeat yourself please". Duk da na fahimci abun da ya furta amma sai na sauya akalar zancen"a gaishe ta kuma a isar mata da saƙona". Ina gama furta haka na juya zan tafi na ji wata murya ta sauƙa a ƙofofin kunnuwana, muryar da ba zan taɓa manta tasirinta a cikin rayuwata ba. Muryar da ko ina gangaran mutuwa in na ji ta haƙiƙa zan gane amonta. Muryar da ta sama matsuguni ta zauna a cikin kwanyata ba tare da biyan tara ko haraji ba. Cak na tsaya jikina yana wani irin rawa tamkar wacce aka jona wa wutar lantarki haƙwarana suka datse harshena wanda ina da tabbacin har sai da ya fitar da jini. "Saif wai me ye yake faruwa ne? Ina ne nan wajen kuma?". "Ba komai Taukif shiga motar mu tafi kawai". "Wannan yarinyarta fa me ye haɗinka da ita? Na dai san ba ka zuwa ire-iren wajajen nan. Ke zo nan". Take ƙirjina ya soma dakan lugudan-lugudan tara-tara sau goma sha tara, zuffa ya soma tsantsafo mini sa'ilin da na ji takun tafiya ana kusanto inda nake tsaye har ƙamshin turaren jikinsa ya riga sa isowa gare ni. "Ke yarinya me ye kike yi a nan wajen?". "Ba-ba-ba-ba-ba babu". Na amsa masa a gajarce ina ɗaukar hanyar barin wajen cikin matuƙar sauti kamar zan tashi sama, har ƙafafuna suna haɗewa cikin doguwar rigan da ta gama jikina tsam tamkar tare aka halicce mu. Kaina tsaye na wuce ɗakina na zubu akan tabarma ko kukan na kasa yi illa kawai soyar da zuciyata take yi mini. Ƙirjina yana yi mini wani irin zafi tamkar ana watsa wa mini garwashin wuta ta yadda nake jin zafin yana ratsa wa har ta cikin nama da jijiyoyin jikina. Kan ka ce kabo gabaɗaya jikina ya ɗauki zafi har wani kakkarwa nake yi. "Innalillahi wa inna ilahirin raji'un!". Shi kaɗai na yi nasarar furta wa kafin zuciyata ta antaya cikin cakwakiyar tunani. Tabbas ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba wannan muryar Muhammad Taukif ne. Mutumin da ba zan iya mance da ranar da na far tozali da shi akan hanyata ta zuwa islamiyya da kuma kalamansa ba. Shi ne mutum na farko da na taɓa haɗuwa da shi a cikin rayuwata da zuciyata ta sama nutsuwa da kalamansa tun kafin na san halayensa da ɗabi'un balle har na kai ga sanin haƙiƙanin wane ne shi. In dai ta tabbata shi ne baƙon da na ji Saif yana batun zuwansa to ina cikin lukutin yanayi. Na yarce zuffan da ya kwanta a saman goshina kana na tashi na nufi ɗakin Hajiya Babba domin kai mata saƙon da aka bayar da sunanta. Na zauna a ƙasa ina yi mata sannu da hutawa ta amsa tare da zarce wa da faɗin"to ya ya kika gan shi ina fatan ya yi miki?". Na kawar da zancen ta hanyar faɗin"ga wannan ya ce a ba ki". Na miƙa ledodin dukka biyu ta amsa tana faɗaɗa annurin fuskarta bakinta har kunne. "Dukka wannan nawa? Amma mun yi waya da shi kafin shigowar ki ya ce ɗayan saƙon na ki ne. Don haka ga shi ke ma sai ki je ki fantama ki more wa ranki, don na san waɗanda zai ba ki gobe sai sun ci uban waɗannan". Na girgiza kaina"Hajiya ba zan ci ko naira ɗaya daga cikin kuɗinsa ba. Don bai kwanta mini a raina ba, Hajiya kamar yadda kuka sa na yi abin da kuke so ni ma ina da nawa sharaɗin da dokoki. Ba zan fara mu'amala da kowa ba sai wani mutum guda". "Wane ne wannan mutumin?". Na ɗan yi jim kafin can na ce"Sheikh Dawood Gaskiya dokin ƙarfe". Ta dafe ƙirjinta tare da waro idanunta waje"Sheikh Dawood dai da na sani mai tafsirin Alkur'ani?". Na gyaɗa mata kaina alamar e. Ta kallo ni da wutsiyar idonta tana faɗin"ke yarinyar nan watau bayan taurin kai da kafiyar tsiya tamkar kafiran farko har da hauka ma akwai a cikin kanki. Yo in ba hauka ba ta yaya kike tunanin za a iya jawo hankalin irin wannan mutumin da addini da tsoron Allah ya ratsa jini da jijiyarsa". "Ba zai yi wahalar shiga hannu ba Hajiya. Ni ko hanya ayi mini na gan shi ni kuma na yi miki alƙawarin sai na jawo hankalinsa cikin ɗan ƙanƙanin lokaci" Ta yi mini wani irin kallo irin kallon da mai hankali yake yi wa zautacce ta ja tsaki ta tofar tana mayar da hankalinta kan abin da take yi ta furta"bari Aminu ya damu mu yi magana tabbas akwai wani abu da yake yawo a cikin wannan kan nakin". Na cira kai na kalle cike da ƙwarin gwiwa na ce"babu komai a cikin kaina Hajiya, ki ba dama ni kuma na yi miki alƙawarin zan jawo shi har ya shigo hannu. Idan na gaza aikata abin da na furta na yarda ki haɗa mini kayana ki ɗaura mini a kaina ki kora ni daga cikin gidan nan sannan ki haɗa mini da ko wani irin wulaƙancin da kika yi niyya". "Kin san me ye kika faɗa kuwa?". "Ƙwarai kuwa Hajiya". Ta ɗan yi jim kafin can ta ce"shi kenan na ba ki dama amma idan kika kasa jan hankalinsa tabbas zan yaga miki rigar rashin mutumcin a bainar nasi, zan wulaƙanki irin wulaƙancin da ko

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});