Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 90

Chapter 90

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,216 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

shi kwanakin sai mafarkinki nake yi da zaran na kwanta bacci wannan ya ƙara tabbatar min da cewar akwai wani damuwa. Don Allah mene ne yake faruwa?". Maimakon na ba ta amsa sai kawai na fashe da kukan da ya yi matuƙar gigita mata tunaninta ta din ga jeranta mini tambayo ɗaya bayan ɗaya. "Subhanallahi! Hashashen zuciyata ya tabbata ke nan wai me yake faruwa ne sanar da ni idan akwai wani matsalan?". "Amira ina cikin matsala shi kenan na jefa kaina da wanda bai ji ba bai gani ba cikin matsalar da ni na yi silar ruruwanta". "Wani irin matsala ke nan?". Take na kwashe komai na yadda muka yi da Saif har da alƙawarin da na yi masa da kuma yadda ya daina ƙira na na tsawon kwanaki biyu, sannan na ƙara da faɗin"jikina ya na ba ni tabbas akwai wani matsalan tun da har na ji shi shuru na tsawon wannan lokacin, sai dai ban san abin da yake faruwa. Idan ma matsalar ce ba na fatan ta shafi kowa mussamman Saifullah da shi ne mutum na farko da ya fara ba n goyon baya kuma ya tsaya mini tsayin daka wajen ganin na cika wannan burin da ya daɗe a cikin rai. Daman sai da Yaya Alhassan ya gargaɗe ni amma na ƙi amfani da abin da ya faɗa mini har umartana ya yi akan na karya memory ɗin amma na yi kunnen uwar shegu". "Innalillahi wa inna ilahirin raji'un! Amatullah me yasa za ki aikata haka? Me yasa ke ba kya jin magana ne sannan ki na da kafiya akan abu. Na yi tunanin kin daɗe da mance wa da babin wannan mutumin a cikin rayuwarki ashe har yanzu ki na nan akan bakanki. Me yasa kike ƙoƙarin butulcewa rahamar da Ubangiji ya yi miki? Kike ta ƙoƙarin ganin kin bankaɗo sirrinki da Ubangiji ya lulluɓe ta a idon duniya?. Allah ya rufa miki asiri ya ceto ki daga rayuwar halakan da kika faɗa ya karkarto da hankalinki zuwa gida ki ka dawo rayuwa cikin ƴan uwanki, su ka rufa miki asiri suka yi miki gata suka ɗauke dukkan ɗawainiyyarki ta hanyar killace ki a cikin gida suna wadata ki da dukkanin abin buƙatun rayuwa. Daga ƙarshe Allah ya ɗaga kimarki ta hanyar yi miki tagomashi da samun mijin da yake shirye ya aure ki, duk wannan tarin ni'iman da Ubangiji ya lulluɓe ki da ita amma kike ƙoƙarin butulcewa". Izuwa yanzu kuka nake yi sosai wiwi don jikina ya gama mutuwa murus na kuma tabbatar wa cewar matsala ce ta hana Saifullah ƙira na ya sanar da ni halin da ake ciki. Sai da ta sallawantar da wasu mintuna kafin ta furta"yanzu dai ki yi haƙuri ki kwantar da hankali, ki yi addu'a Allah ya sa komai lafiya kuma shi ma yana cikin ƙoshin lafiya. Idan kin ga abun ya ci tura to ina mai ba ki shawara da ke ki ɗaga waya ki ƙira shi ki ji halin da ake ciki domin hakan ba laifi ba ne, masu iya magana su na cewa gaida mai gaishe ka ko da kuwa ba zai amsa ba". Sai da na zurfar da zafafan iska daga bakina kafin na ce da ita"na ƙira shi kuma?". Ta katse ni"to hakan laifi ne ko kuma haramun ne aikata hakan? Kin ga wannan jan ajin babu inda zai kai ki sai dai ya sauƙe ki a tashar nadama. Ki ɗauki waya ki ƙira shi ki ji halin da ake ciki alama ce ta nuna kin damu dashi, ko ke da nan ki na tunanin shi da yake ɗaga waya kullu yaumin ya ƙira ki shi bai san ciwon kansa da darajan kansa ba ne?". Luƙus jikina ya yi sanyi ƙalau har na kasa motsa wa daga inda nake zaune. "In sha Allah inna ga shurun ya yi yawa zan ƙira shi". Ban ƙari sa zancen ba ta katse mini hanzari"kamar ya ya? Ai yanzu ya kamata ki ƙira shi son samu m, mu na gama wayar nan ki ƙira shi". "Ki na ganin hakan ne mafita?". A kufule ta ce"ban sa ni ba, tun da ke nan zama kika yi kika miƙe ƙafa ki na jiran ƙiransa, to sai ki yi ta jira daga nan har zuwa ranar da mahadi zai bayyana". Ta gama furzar da zancen kit ta katse ƙiran ta bar ni da sauƙe tagwayen ajiyan zuciya tamkar wacce ta yi wani gagarumin aikin ƙarfi. Rumgume wayar na yi a ƙirjina tare da lumshe idanuna da ruwan hawaye yake zuba daga cikinsu ina yin zantukan na Amira suna yi mini amsa-kuwwa a cikin na'urar naɗan sautina tamkar a lokacin take furta mini su daki-daki. Wani sashin zuciyata ta gaskata abun da Amira ta ce da ni, don haka na ɗauki wayar na lalumo lambarsa na dannan masa ƙira sai dai ƙiran ba ya tafiya, a jere a jere sai da na yi masa ƙira uku amma duk ba ya tafiya. Dole ƙanwar na ƙi na haƙura na ajiye wayar na kwanta ina ta fama da tunani kala daban-daban bacci sai da ya cika cikakken ɓarawo kafin ya iya ɗauka na sai da na makara tashi sallan asubahi, ko da na iddar da sallan sai da na ƙara gwada layin Saif amma har yanzu ba ya tafi, ganin tunanin yana neman ya yi rikita mini kwanyata ya sanya ni ɗauko alƙur'ani na buɗe na soma karanta ban gushe ina yi ba har sai da na ji zuciyata ta sama nutsuwa wani sanyi ya ziyarci sashin ruhina. Ko da na gama karatun zama na yi a wajen na zabga wani uban tagumi. Ban san lokacin da Yaya Alhassan ya shigo cikin ɗakin ba har sai da saurin muryarsa ta ratsa dodon kunnuwana. "Tunanin me ye kike yi haka?". Na yi figigi na dawo cikin hayyacina"na'am ka ce me ye?". Ya kafe ni da ido kafin ya furta"tunanin me ye kike yi?". Na sadda kaina ƙasa"babu komai". "Koma dai mene ne tabbas kawai abin da yake damun ki, ki yi ƙoƙarin yaƙar duk damuwar da yake damunki a cikin ranki". "In sha Allah Yaya na gode sosai". Naira duhu uku ya zaro daga cikin aljihunsa ya ajiye mini a gabana tare da faɗin"ga wannan ki rage wani buƙatunki da shi, babu yawa ki yi maneji da shi". Wani daɗi na ji ya cika mini rai da ruhina har sai da ya haddasa mini tsiyayar da ƙwalla zan yi magana ya dakatar da ni ta hanyar ɗaga nuni hannu alamar ba ya son jin komai daga gare ni. "Ki yi abin da na ce miki kawai". Na buɗe baki zan yi godiya ya kuma katse ni"ba na son wannan godiyan nakin da ba shi da iyaka. Duk abin da na yi miki ki sa a ranki cewar haka daman wani nauyi ne da ya rataya a kaina na sauƙe shi". Kaina kawai na jinjina masa kafin na furta"Allah ya saka da alkhairi ya ƙara buɗi da azurki mai amfani". "Amin" ya Allah ya amsa da shi yayin da yake tashi ya miƙe tsaye haɗe da ƙara faɗin"babu wata matsalar ina fatan dai ko?". "E babu komai Yaya Alhassan, tabbas a zamana da ku kun wadata ni da komai babu abin da na

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});