Chapter 79
Chapter 79
min tarin laifukan da na yi mata, amma duk da hakan soyayyar da take yi min ko kaɗan bai sauya domin ina ganin hakan a cikin idanunta". A raunane ya ƙare zancen tamkar wanda yake shirin fashewa da kuka. "Mun riga da mun yi magana da ita in sha Allah komai ya wuce da yardan Allah. Ina fata da addu'ar Allah ya dawwamar da zaman lafiya a cikin gidan aurenki, ya albarkace ku da zuri'a ɗayyaba". "Amin ya hayyu ya ƙayyum". Suka haɗe baki wajen amsa wa cike da jin daɗin addu'ar, haka muka yi sallama da Amira ba don raina ya so ba ina tsaye a wajen har sai da na ga sun ɓace wa ganina kana na koma ciki. Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya lokaci yana gudu yayin da kwanakinmu na duniya yake ƙarewa, wasa-wasa muna ƙara kusantar mutuwarmu ba tare da mun farga ba balle mu tanadin kuzurin tafiya. A cikin wannan yanayin har Umma ta cika kwanaki arba'in da barin duniya, a kullum kwanan duniya Anty Sawwama da ƴaƴanta ba su da wani burin da ya wuce su faranta mini ta hanyar samar mini da duk wasu abubuwan da zan buƙata, cikin ƙanƙanin lokaci suka sauya mini rayuwata daga duhu zuwa bayyanan nan haske. Na sama dukkan wani kulawan da nake buƙata tare da tattali. Ranar da na cika wata uku a cikin gidan a wani rana bayan sallan isha'i na shirya na je ɗakin Yaya Alhassan, a ranar na yi yunƙurin sanar da shi komai dangane da dalilin zuwa na otel a wannan ranar da suke je nemana. Yana zaune aka kujerar zaman mutum ɗaya da yake cikin ɗakin na yi sallama ya amsa mini na shigo sai kuma na tsaya a ƙofar ɗakin ya ɗago ido muka haɗa ido hakan ya sanya sa fahimtar dalilin da ya hana ni ƙarisowa. Ya tashi ya ɗauki rigarsa ya saka a jikinsa kafin na shigo cikin ɗakin. "To yanzu kam sai ki shigo ko". A hankali na tako na shigo na zauna ina gaishe shi ya amsa tare da zarce wa da faɗin"akwai wani matsala ne?". "A'a daman na zo mu yi wani magana". Ya gyara zamansa yana fuskanta da kyau kafin ya ce"ina sauraronki". "Ka bar sauraron wannan tukunna". Na yi zancen ina kunna masa sautin muryar da muka naɗa, ya amsa wayar ya na saurara sai da ya gama ji tsaf ya ga hotunan nan kana ya ɗago kai yana duba na cikin wani irin mungun yanayin muryarsa a ƙashe ya ce"waɗannan hotunan fa?". Jikina ya ɗauki rawa sa boda yanayin da ya furzo zancen take tsoro ya mamaye mini raunananniyar ƙalbina sai dai hakan bai hana bakina sanar da shi ragowar bayanin ba. Ban ƙarisa ba na ji ya ɗauke ni da wani irin mungun mari duk da ina zaune sai da na ji wani irin yana ɗauka na, marin da ya sauƙe mini har sai da bakina ya fashe ya soma zubar da jini. Cikin zafin rai ya miƙe tsaye yana nuna ni da ɗan yatsansa idanunsa sun yi jajir tamkar wanda aka watsa wa tsakin barkono, sai dai bakinsa ya gaza cewa komai. [12/23, 2:43 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam __________________________________ Page 7️⃣7️⃣ Mun ɗauki tsawon wasu mintuna kafin ya furzo takaicin da na yi silar cusa masa"me ye ya kai ki aikata wannan ɗanyen aikin Amatullah? Me yasa za ki jefa kanki cikin bala'in, fitina da kuma tashin hankali da zai zama ruwan dafa kanki wataƙila har ya ƙona ki? Kin san girma da martaba wannan mutumin kuwa a idanuna jama'a?". Cikin ƙarajin kukan da sautinsa ba ya fita na furta"Yaya Alhassan mutumin ba mutumin kirki ba ne kamar yadda yake nuna hakan a idanun jama'a, ka na jin abin da yake furta wa ba. Ya yi silan lalata rayuwar ƴaƴa mata masu yawan gaske ta hanyar amfani da ƙarfin ikon da yake da shi a cikin jama'arsa". Bai bar ni dire zancen ba ya doka mini wani gigitaccen tsawan da ya tursasa mini haɗiye ragowar zancen har ina ƙoƙarin datse harshena. "Ban taɓa tantama akan tabbacin cikar hankali da tunaninki har ma da ƙalubalantan ilminki ba sai yau Amatullah, me yasa hankalinki ya gushe har kika kai kanki cikin wannan bala'in? Har da bayyana fuskarki ki ɗauki hoto da shi, dole sai ta wannan hanyar za ki fallasa asirinsa ga duniya kowa ya san halin da yake ciki? Ai idan ba kya iya kama ɓarawo ba sai ɓarawo ya kama ka kuma ka rasa hanyar da za ka kuɓutar da kanka". Tun da ya soma zancen na yi shuru tare da sadda kaina ƙasa ina sharar ƙwalla tare da ci gaba da sauraron zancen da ya ɗago da shi cikin zafin rai. "Yanzu idan wannan hotunan suka fita suka watso a dunia ki na tunanin mutumci kika ja wa kanki ko kuwa rashinsa?" Ya dafa kansa cike da damuwar da ta bayyana ƙarara a fuskarsa har zuwa cikin muryarsa ya koma mazauninsa ya zauna ya sassauta amon muryarsa kafin ya soma faɗin"yanzu me ke kike so a yi da kika zo min da wannan zancen?". Na ji shuru tamkar wacce ruwa ya ci ta, sai da ya ƙara maimata mini zancen a karo na biyu kafin na yi ƙarfin halin magana. "So nake yi a san yadda za a yi a fitar da sautin duniya su ji, ina so asirinsa ya tono duk wani abun da yake ɓoye wa ya fito fili". "Amatullah wai ina hankalinki ne ya yi aure ya tare ne? Yanzu idan aka ce miki ki fitar da wannan sautin muryar sai ki fitar da shi? Sanin kanki ne fa mutumin yana da ƙarfin iko, yana kusa da Sarakuna, gwamnoni da kuma masu riƙe da madafan iko fitar da wannan sirrin daidai yake da rushewan rayuka da dama da tarwatsewar dukkan ginin da aka yi na rayuwa. Tun da har Allah ya rufa mana asiri bai sama nasara akan ki ba ina so ki goge dukkan hotuna da sautin muryar nan, ki manta da kin ma taɓa sanin wani mai kama da shi a cikin rayuwarki balle har ki tuna wani zancen da ya shiga tsakaninku da shi". Ya ƙare zancen yana miƙo mini wayar cikin sanyin jiki na kai hannuna na amsa ina jin wasu hawaye suna zarya tsananin kuncina da kuma saman haɓata. "Amatullah ki cire damuwar komai daga cikin ranki. Alƙawarin Allah cewar dukkan wani azzalumi ba ya tare da shi kuma sai ya kunyata tun a nan cikin duniya a sai an je ga lahira ba. Mussamman ma masu ci da addini ko kuma masu fakewa da sunan addini suka ha'intan bayin Allah. Don Allah ki cire damuwar komai daga cikin ranki, idan halinsa hakan ko ba ka ma ki ba daɗe sai asirinsa ya tono a duniya sai Allah ya buɗe sirrinsa ga duniya kowa ya ji kuma ya gani sai ya tozartasa irin tozarcin da bai taɓa zato ba". Kaina na jinjina da ƙyar na furta"to in sha Allah". Sai da na yi masa sai da safe kafin na tashi na tafi ɗakina ina shiga na zube akan katifar ina kuka mai ci rai, gabaɗaya jikina ya yi la'asar na rasa gane abin da yake
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98