Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 86

Chapter 86

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,213 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

inganci ko ki na cikin gidana ko kuma ki na cikin gidan wani daban ba ni ba, burina ki sama farin ciki da kwanciyar hankali. Don haka ina ba ki shawaran ki zaɓa wanda hankalinki ya fi samun nutsuwa da shi, kika ji ya kwanta miki a cikin ranki. Zuciyarki ta nutsu da shi". Gabaɗaya jikina ya yi sanyi ƙalau tamkar kazar da aka jefa a cikin ruwan gishiri, hawaye suka ciko mini kurmin idanuna sai dai na ƙi ba su damar da za su kwaranya har ya miƙe ban iya ɗago kaina ba balle na ce da shi wani abu, yana shirin fita daga cikin falon Anty Zulaihatu ta fito riƙe da wayata da take ta faman ruri a hannunta. "Kin ga wayarki sai ƙira ake yi tun ɗazu". Na amshi wayar cikin sanyin jiki tare da ɗaga ƙira na kara a kunnena yayin da nake koma cikin ɗakin na zauna a bakin katifan. Sallama ya yi na amsa muryata a dushashe daga haka gabaɗayanmu muka yi shuru. "Daman na ƙira ne na ji ya ya kike da kuma yadda kika wayi gari". Kamar ina gabansa na gyaɗa masa kaina kafin na ce"lafiya ƙalau". "To alhamdulillah a gaishe da mutanen gidan". "Za su ji". Ban jira abin da zai kuma cewa ba na katse ƙiran tare da ajiyar wayar na fita daga cikin ɗakin. Kowa na tunkara da zancen Saifullah magana guda yake furta min shi ne na yi addu'a sannan na bi abin da zuciyata ta nutsu akan ta. A haka har aka cinye sati guda babu ranar da za ta fito ta faɗi ba tare da Saifullah ya riƙa ni ba duk ranar juma'a kuwa sai ya niƙo gari ya zo takanas ta kano gaishe da Anty Sawwama haka za su sha hiran su kafin ya tafi. Haka kawai ranar na tashi da kewan Amira na tambayi Anty Sawwama ta yarje mini zuwa gidan Amira tun da safe na buga shirina na zauna zaman jiran Yaya Alhassan don shi zai kai ni da mashin ɗinsa, da taimakon kwantancen da ta yi mini ranar da ta zo ta muka sama gidan. A ƙofar gidan Yaya Alhassan ya tsaya na shiga ciki na yi mata magana ta fito suka gaisa kana ya tafi bayan ya shaida mini cewar bayan sallan magrib zai zo ya ɗauke ni mu koma gida. "Matar mijinta ki na sha'aninki a cikin gidan nan". Na yi zancen cikin sigar zolaya yayin da nake cire hijabina. Murmushin ta yi kafin ta ce"duk da tun da kika shigo annuri bai gushe daga kan fuskarki ba, amma hakan bai hana ni fahimtar cewar akwai abin da kike ɓoye wa a cikin ranki ba, Amatullah shin akwai wata matsalar ne?". Numfashi mai nisan zango na ja na fesar daga bakina kafin na cira kai ina kallonta na ce"Amira ke ma kin sa matsaloli ai ba ya ƙare wa, in dai da rayuwa to tabbas akwai jarabawa". Ta shimfiɗa masa tabarma a waje muka zauna kana na kwashe komai na sanar da ni don na yarda abokin kuka ba a ɓoye masa mutuwa haka nan abokin cin mushe ba ya ɓoye masa wuƙa. Ta jajanta mini sosai kafin ta ce"ni fa Amatullah ina ganin kamar ki amince masa kawai, inda gaske yake sonki ya zo a yi auren a wuce wajen. Don kin gan ni nan wallahi yanzu ba na goyan bayan dogon soyayyan nan da ake yi a waje da za a shafe shekaru ana buga wa, gwara a yi auren duk soyayya da kulawan da za a ba wa juna ku yi shi a cikin gidanku". Bushashshiyan murmushi na saka da ba shi da alaƙa da nishaɗi kafin na yi ƙarfin halin faɗin" ba na jin zan iya soyayya a yanzu haka, sai dai zan amshe shi ne kawai don cikar wani burina wanda a yanzu shi kaɗai zai iya taimaka mini". Babu shiri ta waro idanunta"wani buri ke nan?". "Me ye abin da tada hankali haka? Sanin kanki ne dai ba zan aikata abin da yake na haramci ba ko?". Kanta ta jinjina cikin sanyin jiki ta soma cewa"haka ne kam to Allah ya shige mana gaba". "Amin ya Allah" Na amsa da shi yayin da muka ci gaba hirar mu cike da kewar rayuwar da muka yi a gaba da takaicin yadda rayuwa ta yi mana atishawan tsakin barkono. Mun ba wa juna shawara akan abubuwa da yawa na rayuwar yau da kullum.Tare muka wuni da Amira da hakan ya yi mini matuƙar daɗi har na manta da tari damuwar da nake cikinsa sai da aka yi sallan magrib kafin ƙiran Yaya Alhassan ya shigo cikin wayata na ɗaga ya shaida mini cewar yana ƙofar gida, na tashi na miƙe tsaye ina faɗin"kin ga ni kam bari na wuce Yaya Alhassan yana waje yana jira na". Cikin rashin jin daɗi ta furta" ga shi har za ki tafi Mansur bai dawo ba, na so a ce ya zo ya same ki wallahi". "Ba komai kar ki wani damu ai zan dawo wataran. Yarinya ta Mansur sai na tuna irin zumuɗin da kike a da idan ya ƙira ki ya ce miki yana hanyar zuwa gida, ranar walwala da farin cikinki na daban ne. Haka ranan in muka je talle za ki ta zuba masa kamar kyauta". Ta ja numfashi ta fesar kafin ta ce"rayuwa fa ke nan ga shi yanzu komai ya wuce har ya zama labari". "Watarana mu ma haka za a tuna mu, a lokaci da muka gushe daga cikin duniyar". "Allah ya yi mana mai kyau". Ta furta yayin da take ɗaukar hijabinta ta saka muka fito, a ƙofar gidan muka iske Yaya Alhassan take ya soma faɗan me yasa zan jawo Amira ta fito raka ni alhalin na san ita ta matar aure, sai da na ba shi haƙuri kafin ya saduda ya yi sanyi. Haka muka yi sallama da Amira ba don ranmu ya so ba muka tafi bayan na yi mata alƙawarin ƙara zuwa nan ba da jima wa ba. Bayan mun koma gida har na yi shirin kwanciya na ji wayata ta soma ruri na yi caraf na ɗaga ƙiran tare da amsa sallamar da ya yi mini na ɗaura da faɗin"ko ba ka ƙira ni ba dama ina da burin ƙiranka yau". "Ko dai sakamakon jiran da aka ce na yi za a sanar min? Yanzu na tashi na je na yi alwala na zo na gabatar da salla raka'a biyu na roƙi Allah ya ba ni juriyar ɗaukar duk irin amsan da zan ji ya fito daga bakinki". Na ɗan lumshe idanuna kafin na buɗe ina faɗin"ba abin da kake tunani ba ne, daman ina son ganinka ne gobe akwai maganar da nake son mu tattaunawa da kai". "Faɗa naki cika wa nawa. In sha Allah goben zan zo ni da wuri ma kuwa". "Na gode Allah ya kai mu". "Amin". Ya amsa da shi daga muka yi shuru dukkanmu sai can na ji ya ce"Aryan da Ayan su na tambayarki". Na yi firgitit na buɗe idanuna da na lumshe su"wai kana nufin har yanzu ba su manta da ni ba?". "Ƙwarai kuwa don kusan kullum sai sun yi maganarki, tun bayan gano gaskiyan da muka yi

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});