Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 33

Chapter 33

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,208 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kare ba zai ci ba. Zan tozarta ki irin tozarcin da za ki ƙwammace ina ma uwarki ba ta haifo ki kin zo cikin duniyar na ba. Zan muzanta ki irin muzancin da za ki zaɓi mutuwarki sau dubu akan rayuwarki. Zan jefa rayuwarki cikin ƙunci da takura da har sai kin daina jin daɗin rayuwar duniya sai kin ji a cikin ranki wanda yake kwance a cikin kabari ma ya fi ki ƴanci da walwala". Ba tare da wani tunani ko dogon nazari ba na amsa da faɗin"ma yarda da duk wasu sharruɗan da za ki gindaya mini. In sha Allah sai na jawo hankalinsa". "Kuma babu wanda zai taimaka miki ke kaɗai za ki yi wannan yaƙin. In ma ki ci in ma ki sha ƙasa". Na haɗiye wani miyau mai kauri daga maƙoshina da ya bushe tamkar ƙasar sahara a lokacin zafi. "Na yarda da dukkan sharruɗanki Hajiya". "Tashi ki je na sallame ki" Ban ce da ita komai ba na tashi na bar cikin ɗakin na koma ɗakinmu, na zauna na buga wani uban tagumi ina jin gabaɗaya duniyar ta yi mini zafi na ja numfashi na furzar ya fi sau shurin masaƙi. Hawayen idanuna sun kafe ƙaf tamkar rijiyar da ruwan cikin ta ya kafe na tsawon shekaru masu yawan gaske, sai yanzu ma yarda tabbas wani tashin hankalin ya wuce a yi masa hawaye sai dai kukan zuci wanda ya fi ciwo gami da raɗaɗi. A firgice Anty Sawwama ta farka daga baccin da ya cikakken ɓarawo har ya yi nasarar sace ta duk da girman tashin hankali da damuwar da yake cikin ƙalbinta da ta gama raunana. A tare Yaya Alhassan da Umar suka shigo cikin ɗakin, Umar ya kunna wutan lantarki take haske ya gauraye ko'ina. "Umma lafiya kuwa me ye yake faruwa?". Kasa magana ta yi illa zuffan da ta ci gaba da haɗa wa tamkar wacce aka sheƙa wa ruwa ya yi mata jilif. "Umar samu ruwa yanzu-yanzu". Da sauri Umar ya fita ya je ya ɗebo ruwan ya dawo ya miƙa wa Yaya Alhassan ya karɓa ya yi tufin wasu addu'o'i a cikin ya ba ta ta sha sannan ya shafa mata ragowar a fuskarta, take ta soma sauƙe ajiyar zuciya wani na bin wani. Umar ya riƙo hannunta ya sanya cikin nasa yana murza wa a hankali. "Umma lafiya kike? Ki na jin abin da muke faɗa?". Kanta ta gyaɗa alamar e tana zarce wa da faɗin"lafiya ƙalau wani mafarki kawai na yi da ya tsora ni ainun". "Wani irin mafarki ne haka Umma?". "Umar mafarkin nan dai da na saba yi a duk sa'ilin da na kwantar da haƙarƙarina da sunan bacci". Cike da damuwa Yaya Alhassan ya ce"mafarki kike yi da Kawu Manniru ya zo yana tambayarki amanar Amatullah da ya ba ki ko?". Cikin sanyin jiki ta gyaɗa kanta"ƙwarai kuwa har ta kai ta kawo ba na ƙaunar na kwanta bacci ko da kuwa na minti ɗaya ne. Ban san ina zan je da girman alƙawarin da Manniru ya bar min ba, Amatullah ina kika shiga ne a cikin duniyar?". "Umma don Allah ki rufa mana asiri ki cire wannan damuwar daga cikin ranki kar wani jinyar ya same ki a dalilin hakan. In Sha Allah Amatullah za ta dawo gare mu cikin aminci da yardan Allah, ina ji a jikina duk inda take tana hannu mai kyau kuma ba za ta taɓa aikata abin da Allah zai yi fushi da ita ba, don duk cikinmu babu wanda bai yarda da tarbiyyan Amatullah ba. Ƙaddarar ta ce kawai ta zo a irin wannan sigar wanda babu yanda muka iya ba za mu iya guje mata ba balle mu sauya mata fasali. Har yau ba mu fasa neman ta ba ina da yaƙinin duk wani mai nema watarana zai dace Umma don haka ki kwantar da hankalinki komai zai zo ƙarshe". Numfashi mai zafi ya ja ta furzar daga bakinta kafin ta sama lasisin faɗin"hakan nake fata da buri Alhassan. Allah ya yi muku albarka ya jiɓanci lamuranku yadda kuke ƙoƙarin yi min biyayya ku ma Allah ya azurta ku da ƴaƴan da za su yi muku fiye da haka". Cike da jin daɗin furucinta suka amsa da amin, Yaya Alhassan ya sa Umar ya zuba mata ruwa a cikin buta ta je ta yi alwala kana su ma suka je duk suka yi alwalan, Yaya Alhassan ya ja su limanci suka gabatar da sallan raka'a biyu na nafila suka miƙa ƙoƙon baran su zuwa ga sarkin da ba shi da abokin tarayya, Sarkin da ba ya ce a roƙo zai amsa. Ba su bar cikin ɗakin ba har sai da bacci ya ɗauke ta suka kunna karatun alƙur'ani a waya suka ajiye a cikin ɗakin. Yaya Alhassan ya tisa ta a gaba yana kallon ta tamkar bai taɓa ganin ta ba. Umar ya dafo kafaɗarsa cike da kulawa yake faɗin"Yaya Alhassan ka kwantar da hankalinka komai zai wuce kamar bai taɓa faruwa ba. Watarana sai dai labari". "Umar idan na ce ba na cikin damuwa haƙiƙa ma yi ƙarya mai girma, tun ranar da Amatullah ta ɓace ban ƙara samun kwanciyar hankali ba, ban ƙasa kasancewa cikin daidaitacciyar nutsuwa ba. Kullum a cikin fargana nake da fatan Allah ya sa tana cikin hannu mai aminci". "In Sha Allah za ta dawo gare mu cikin aminci. Ina ji a jikina Amatullah ba za ta taɓa sauƙa daga kan turban da muka san sa ta ba". "Allah ya amsa". "Amin ya Allah yaya Alhassan". Kashe wutar ɗakin suka yi suka koma nasu ɗakin cikin jimami da tarin damuwar da yake danƙare a cikin zuciyoyinsu. [12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam __________________________________________ Page 5️⃣7️⃣ Haka kawai na wayi gari ina ji na cikin wani irin karsashi a jikina, wanda na danganta hakan da karatun alƙur'anin da na yi ta yi bayan na yi sallan asubahi. Na tisa haddan da yake kaina sosai har sai da na ji wani nutsuwa ya lulluɓe mini rai da ruhina. Sai da na ɗebo ruwa na yi wanka na mayar da kayan da yake jikina na duba ko'ina na rasa abin da zan tauna a cikin ɗakin, na gama cinye duk siyayyar da Hajiya Muhibbat ta yi mini kat. Numfashi na ja na fesar kafin na yi shirin tafiya wajen aikin zan fita na ji sautin da ya tirsasa mini tsayawa. "Madam fita za ki yi ne?". Na waigo na yi mata kallo guda tana kwance akan katifarta da ban ma san sa'ilin da ta dawo ba daren jiya sai wayen gari na yi na gan ta cikin ɗakin. "E ko na tsaya za ki aike ni ne?". "To ikon Allah wai na zaune ya faɗi. Abin ai bai kai haka ba, dama na ga muna zaune a ɗaki ɗaya ne akwai haƙƙin maƙwabta a kanmu ai ko?". Na bi ta da wani kallo don har yanzu ban manta zafafan kalaman da ta yaɓa mini ba ranar farko da ta zo cikin ɗakin. "Tambaya kike yi ko neman sani?". "Duk wanda kika ɗauka daga cikin biyun daidai ne". Ban amsa mata ba na ja tsaki na fice daga cikin ɗakin ina jin haushin abin da ta yi mini har

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});