Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 67

Chapter 67

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,208 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

so. Ki na da ikon ki zartar da duk wani hukunci da kike tunanin ya fi dace wa da rayuwarki tun da mai ɗaki ai shi ya san inda yake yi masa yoyo, ga hanyar nan ki tafi duk inda kike tunani da zaton za ki sama kwanciyar hankali daman fatanmu a ko yaushe bai wuce ki yi rayuwa cikin nutsuwa ba, sai dai a duk lokacin da kika nemo mu don mu zame miki gata tabbas za mu ba ki mafaka don na yarda da wannan karin maganan da ake cewa hannun ba ya taɓa ruɓewa ka yanke ka yar. Kuma babu inda za ki je ko juyin zamanin da zai sa mu sauya ki daga kasancewarki ƴar uwa kuma jininmu. Don haka zaɓi ya rage ga mai shiga rijiya". Yana rufe bakinsa daidai lokacin da Amir ya iso wajen duk ya bi mu da kallo kafin ya ce"Yaya ya na ganku a nan a tsaye? Ko dai an sallame ta ne?". "Ba a sallame ta ba Amir ta dai sallama kanta ne, tun da har ta na ƙoƙarin guduwa". "Guduwa kuma? To in ta gudu ta je ina?" Cikin da takaicin da ya haɗe da tarin baƙin ciki Yaya Alhassan ya ɗage kafaɗunsa alamar mai sani ba a hankali ya furta"ga ka ga ita sai ka tambaye ta, ta ba ka amsa don ni kam na gama magana da ita sai dai na saurari hukuncin da za ta yanke". Yana dasa aya a zancensa ya juya ya koma cikin asibitin na lura kafin ya gama maganar har sai idanunsa suka kawo ruwan ƙwalla. Na durƙushe akan gwiwoyina sakamakon gazawar ƙafafuna yayin da na fashe da wani kuka mai rikitarwa da narkar da zuciyar mai saurare. Ina iya jiyo sautin ajiyar zuciyar da Amir ya saka kafin ya soma magana cikin sanyin jiki da na murya. "Amatullah rayuwar da kika zaɓa wa kanki ke nan kuma ki na tunanin wannan hanyar da kika kai hanya ce mai ɓullewa?. Tun ranar da muka wayi gari babu ke tun daga wannan ranar ba mu ƙara yin bacci cikin salama ba, duk ranakun duniya kanmu muke zargi akan duk wani halin da kika tsinci kanki a ciki, kan mu muke ɗaura laifi tare da lashen takobin nemo a duk inda kike a cikin duniyar nan matuƙar ki na numfashi". Shi ma ya dasa aya a zantukansa ya juya ya bi bayan Yaya Alhassan ransa a matuƙar ɓaci idanunsa sun kaɗa sun yi jajir da su tamkar wanda aka watsa masa tsakin garin niƙaƙƙen barkono a cikin idanunsa. Ji na yi kaina ya yi dum tamkar wacce aka ɗaura wa dutsen zuma. Na soma kokuwa da numfashina da yake maƙale mini a ƙirjina da na ji kamar an sanya taɓarya an tokare mini ƙirjin, jikina gabaɗaya ya ɗauki rawa dole na tashi daga wajen sa boda hanya shiga da fita da mutane suke ta zirga-zirga a wajen. A hankali na soma tafiya bayan na ɗauki hanya komawa cikin ɗakin da na fito yayin da zantukan Yaya Alhassan suke yi mini amsa-kuwwa a cikin kunnuwana tamkar a lokacin kalaman suke ratsa tsakanin leɓɓansa suka fitowa a wannan lokacin. Ko da na iso ƙofan ɗakin sai na dan yi jim ina daidaita nutsuwata kafin na turo ƙofar ɗakin na shiga bakina ɗauke da siririn sallaman da ya tsaya iya kan leɓena. Ba su amsa mini ba illa zuba mini ido da suka yi kaman yau suka fara ganina kaina na rusunar ƙasa sa boda na rasa ƙarfin gwiwan da zan iya haɗa ido da su. Jikina ya soma rawa da hakan a tursasa mini durƙushewa akan gwiwoyina ina wani kuka mai tsananin ƙarfi duk yadda na so na yi magana bakina ya ƙi haɗin kai wajen lanƙwansa harshena balle har sautin maganan ya fita ta yadda za su iya ji abin da na furta. Gabaɗayansu suka yi shuru babu sautin da yake tashi a ciki ɗakin face sautin kukan da nake yi mai matuƙar cin rai na ɗau lokaci ina kukan tamkar raina zai yi bankwana da gangar jikina kafin can na tsinkayo amon muryan Yaya Alhassan a kaurare ciki tsare gida babu alamar wasa ko kaɗan a tattare da shi. "Ki hanzarta ki sanar da mu hukuncin da kika yanke, don mu ma mu san inda dare ya yi mana". Sai da na ja dogon numfashi mai nisan zango kafin na sama zarafin raba tsakani haƙwarana da suka manne da juna tamkar waɗanda aka sanya mayen ƙarfe a tsakaninsu. Cikin raunin da yake fito wa kai tsaye daga ƙasan zuciyata ba tare da wani shamaki ba na ce"don Allah ku yi haƙuri ku yafe mini na san na baƙan zuciyoyinku....". Ya ɗaga mini hannu alamar ba ya son jin wani abu daga gare ni. "Ba wani dogon jawabi muke buƙatar ji daga gare ki ba Amatullah. Hukuncin da kika yanke kawai muke son ji shin kin zaɓa ki ci gaba da rayuwa a nan inda muka same ki, ko kuma za ki haɗa kayanki mu koma gida gaban iyayenmu mu rayu cikin farin ciki da sanyawar albarkarsu a gare mu? Don ke yanzu ba yarinya ba ce babu wanda zai yi miki dole balle har ya tursas ki ki aiwatar da abin da ba kya ra'ayinsa". A kufule ya ƙare zancen cikin zafin rai tamkar zuciyarsa za ta fito waje tsabar tafasar da take yi, lamarin da ya ƙara azalzalan ruhina hawayen da nake yi suka ƙara karfin gudu suna zuba daga cikin idanua tamkar bakin indararo. "Na amince zan bi ku mu koma gida tare". Na yi furucin muryata a shaƙe tamkar kwaɗon da aka danna kansa a cikin ruwan zafi. Duk su biyun suka yi shuru kafin can Yaya Alhassan ya ce"kin amince da hakan har cikin ranki ko kuwa dai kawai babu yadda kika iya? Don wallahi ba zan ɓoye miki ba tun da na ga kin yi ƙoƙarin guje mana daga cikin asibitin na ji gabaɗaya gwiwoyina sun yin sanyi ba na son mu yi miki tilas kuma daga baya a zo ana dana sani da cizon ɗan ƴatsa". Na zuƙe majinan kukan da ya zo mini kafin na sama damar cewa"na amince wallahi". Na ƙare zancen cikin karyewan zuciya da rashin ƙwarin jiki. Kafin su ce wani abu aka buɗo ƙofar ɗakin aka shigo tare da yin sallama da tashin farko na gano muryar Zinariya ce, duk sai da ta gaishe su kafin ta tambayi ya ya mai jiki, Amir ne ya amsa da cewar da sauƙi. Duk suka miƙe tsaye Yaya Alhassan yana faɗin"bari na je wajen Likitan ya ba mu sallama". Amir ya rufa masa baya suka fita tare suka bar ni daga ni sai Zinariya zaune a cikin ɗakin, ita ta taimaka mini na tashi na zauna daga durƙushewar da na yi na jingina bayana jikin matashin da ta sanya mini a bayana don na ji daɗin zaman, na lumshe idanuna yayin da wasu hawaye masu zafi suke fitowa daga cikin idanuna da nake jin sauƙar su bisa fatan fuskana tamkar sauƙan tafasasshen ɗanyen ruwan dalma mai turiri. "Ya ya jikin nakin?". "Da sauƙi". Na amsa da shi ba tare da na buɗe idanuna na gan ta ba. "Wallahi gabadayanmu mun tsorita da irin yanayin da

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});