Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 74

Chapter 74

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,207 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ya dawo ya ga tsantsar nadama da dana-sanin da yake kwance a cikin idanun Umma, zan zo ya dawo ya ga yadda ta yi kewarsa a duniya yayin da ta soma amfani da tarin nasihohin da yake yi mata, Allah mai iko wai yau bakin Umma yake furta mini kalmar Allah ya yi miki albarka. Ban iya runtsawa a wannan daren ba har aka ƙiran sannan asubahi na tashi na yi alwala na yi sallan, sannan na zo zan tashi Umma don na yi mata alwala ta yi na ta sallan na ji shiru, na soma ƙiran sunanta ina bubbuga matashin da kanta yake kai nan ma ba ta tanka mini ba. Nan fa ido ya raina fata na soma jijjiga ta ina ci gaba da ƙiran sunanta amma har yanzu shuru. "Innalillahi wa inna ilahirin raji'un! Umma don girman Allah kar ki yi mini haka. Ki yi wa Allah ki buɗe idanunki". Na yi furucin cikin tsananin kiɗima da ruɗewa, ganin zaman ba zai haifar mini da ɗa mai ido ba ya sa na na baza ma waje, ɗakin Umman Amira na nufa ina buga mata ƙofa tare da ƙiran sunanta amma ba ta amsa wa, babu abin da nake iya furtawa illa kalmar innalillahi wa inna ilahirin raji'un. Na daɗe buga ƙofan kafin Baba Habu mijinta ya shigo da alama daga masallaci yake. "Ke lafiya?". Ya watsa mini tambayar cikin zafin rai. "Daman jikin Ummata ne ya tashi shi ne na zo ƙiran Umman Amira, ta taimaka ta zo mu je ta duba ta". "Wani irin ta duba ta? Likita ce ita ɗin ko kuma da na ilmin sanin jinya? Warin da yake fita daga jikin Hafsatu da matata ta shaƙa jiya shi kaɗai ma sai da ya haddas mata cuta, daren jiya ba mu runtsa ba. Haka ina zaman zamana aka sa ni kashe ƴar dubu uku ta na sayo mata magunguna shi ne fa har ta sha ta kwanta yanzu da zan fita Masallaci. Don haka ba za ta je ko'ina ba idan jikin ya yi tsanani ki ɗauke ta ki kaita asibiti likitoci su duba ta". Cike da mamaki na ce"Baba ni ce Amatullahi, ko ba ga shaida fuskata ba ne?". "Na shaida ki tsaf fuskarki ai ba ɓoyayyiyar fuska ba ce a cikin unguwan nan, na gane ki sarai ko ba Amatullah ɗiyar ba ce Malam Manniru da ta yi cikin shege har hakan ya yi sanadiyar mutuwarsa ba, sannan ko kwanaki arba'in bai cika a ƙasa ba kika sanya ƙafafunki ki ka gudu daga gida kika bi Saurayin da ya yi miki cikin ku ka je can ku ka ci gaba da baɗalarku ba". Yana gama zancen ya zo ya buɗe ƙofar ɗakin ba ko kusa ban yi tunanin a buɗe take ba ya shige abin sa. Har ƙasa na durƙushe akan gwiwoyina ina ta wani irin haki tamkar wacce ta fafata a gasar tseren gudu a matakin duniya gabaɗaya. Ina cikin wannan halin Ustazu Abdulwahab ya shigo cikin gida ya dawo daga masallacin sallan asuba, ya tambaye ni me ke faruwa? Cikin sanyin amo na zayyana masa komai ya ce mu je ya duba ta. Na yi gaba ya na bi na a baya muka ka isa wajen Umma. Ya kai minti biyu yana kallon fuskarta sa boda tun da na tashi na kunna hasken wayata na ajiye. Sai can ya tsuguna a gabansa tare da kai hannunsa daidai hancinta hakan bai yi masa ba sai da ya riƙo tsintsiyar hannunta na ɗan danna yatsansa kafin na ga ya jijjiga kansa. "Don Allah me yake samun ta? Tun ɗazu fa ban ga ta yi motsi ba. Shi yasa tun jiya nake ta ce mata mu je mu asibiti". Ya ɗan yi jim kana ya ce"Amatullah ko da kun je asibiti babu abin da zai sauya daga abin da Allah ya rubuta zai hare ta". Da hanzari na tari numfashinsa"me ye kake nufi?". "Sai dai haƙuri don ita kam ta riga mu gidan gaskiya, ta riga da ta amsa ƙiran Ubangijinta". Ji na yi komai na duniyar ya tsaya mini cak haka na zube akan gwiwoyina ki hawaye na kasa yi illa kafe Umma da na yi ido jikina ya na rawa, ƙasa-ƙasa nake ji yo sautin muryar Ustazu Abdulwahab sai dai ba na iya tantance abin da yake bakinsa yake furtawa balle har na fahimta. Ina nan kamar gunki na kasa motswa har izuwa lokacin da ya fita ya je ya ƙira matarsa suka dawo tare. Ita ta riƙe ni sa boda yadda jikina yake rawa ina ga ni Ustazu Abdulwahab ya rufe wa Umma idanunta da suka kafe sannan ya lulluɓe ta da zanin da ta lulluɓu da shi. Ɗakinta ta kai ni ta zaunar da ni sai na kasa yin komai, ba na iya yi ki da magana ba balle kuka. Idanuna ne kawai suke motsawa. Ban san adadin awannin da na ɗauka zaune a wajen ba har zuwa lokacin da Anty Sawwama da Anty Zulaihatu suka zo su. Duk kukan da na mutane suna yi akan gawan Umma ni ko hawaye na kasa yi. Duk wanda ya zo ya ji labarin cewa na dawo gida ni yake tausayawa akan mutuwar Umma, sai dai ni kuma Allah cikin ikonsa ya saka mini wani nutsuwa na mussamman duk abin da ake faɗa ina ji sai dai ba na iya mayarwa. Har aka shirya Umma na je na yi mata addu'a ban yi kuka ba, sai da na ga an fito da ita za a fitar da ita waje don a yi mata salla. Ana ɗaga makarar na yanke jiki na faɗi, sai farkawa na yi na ganni a cikin ɗakin Anty Sawwama sai dai har zuwa wannan lokacin maganata ba ta dawo ba. Har aka yi kwanaki bakwai ba na iya yin magana ba na iya yin bacci ba na komai illa na zauna waje guda na yi shuru ni ba tunani nake yi ba, haka nan ni ba nazari ba. Ranar da aka yi sadakan bakwai ina zaune Yaya Alhassan ya shigo ya same ni. Ya zauna kusa da ni yana kallona yayin da na yi ƙasa da idanuna. "Amatullah". Ya ƙira sunan cikin sanyin murya mai cike da damuwa, kamar ya kunna wuta haka na ji hawaye suna zuba daga idona bakina ya fara rawa ina ta ƙoƙarin yin magana amma na kasa, sai da na ja dogon numfashi na fesar kafin na yi nasaran faɗin"Yaya Alhassan shi kenan Umma ma ta tafi ta bar ni? Ba za mu sake gana wa ba? Me yasa Allah yake jarabta na da rasa dukkan mutanen da nake so? Allah na tuba na tuba ka yafe mini". Cikin wani irin cushewan amo na yi zancen ina ci gaba da fitar da hawayen da na shafe tsawon kwanaki ba tare da na yi su, bai hana ni yin kukan ba kamar yadda bai dakatar da ni ba illa idanun da ya zuba mini. [12/21, 12:04 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam _______________________________________ Page 7️⃣5️⃣ Na daɗe ina kukan har sai da na ji numfashina yana sama yana ƙasa tamkar wacce aka sanya igiyan kirtani aka zarge min wuyana da shi. Haƙwarana suna karafɗiya da ruwa tamkar sabuwar haihuwar kazan da

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});