Chapter 64
Chapter 64
hannunsa jikina daga inda yake zaune na zame wa ina tashi tsaye na tsaya "Burin da nake da shi akan kowacce yarinyar da na ƙyalla idanuna akanta". "Wane ne Muhammad Taukif ake yi wa alaƙabi da Sultan, shin shi ɗin jininka?". Ya ɗan yi jim yana ɗan bubbuga goshinsa a ƙoƙarin hana idanunsa rufe wa kafin ya furta"Sultan yaron kirki ne ba, shi ɗin jinina ne kuma ɗa miji ɗaya tal a gare ni tamkar rai, ina son shi har cikin raina musamman yadda na lura ya na hazaƙa da basira a bangarorin da suka shafi addininsa. Yaro ne mai nutsuwa da sanin ya kamata haka nan akwai shi da girmamawa duk wani wanda yake gaba da shi uwa uba ga tausayi da jin ƙai. Sai dai na ɓoye ainihin wane ne shi a gare a duniya mutane ƙalilan ne suka san hakan yayin da wasu suke ɗaukar sa a matsayin ɗan ɗan uwana, wasu ma su kan ce ma yaran nan ne kawai da nake taimakawa wajen inganta rayuwarsu. Sai dai shi ɗin ɗana ne jinina yake yawo a cikin jikinsa sai dai ba ta hanyar aure aka haife ba ma'ana shege ko kuma na ce ɗan gaba da fatiha". Na waro idanuna waje cike da son tabbatar da sahihancin abin da kunnuwana suke ji yo mini. Cikin ruɗani na ce"shege kuma?". Kamar jira yake yi na yi tambayar ya yi caraf ya ba ni cikakken amsa"e shege don ba ta hanyar aure aka same shi ba sai dai wannan wani sirri ne da duk duniya babu wanda ya san shi cikin kuwa har da iyalina da shi kansa Sultan ɗin. Mahaifiyarsa ba musulma ba ce sai dai kin sa ko a cikin ƙabilan ma kawai masu tarbiyya da ilmin sanin addininsu, ƴar asalin ƙasar Ghana mun haɗu da ita lokacin da muka je gabatar da wa'azi muka keɓe ta ita a wannan lokacin Allahu Mulƙussamawati ya ƙaddara samuwar Sultan a cikin cikinta, bayan na dawo ƙasa Najeriya na sa a ci gaba da bibiyanta har zuwa lokacin da ta haihu ko da na ji ɗa na miji ta haifa sai na saka aka sato min shi ta ɓoyayyar hanyar da har abada ba za ta taɓa tunanin ni na yi wannan aikin ba. Na kai shi cikin gidan na damƙa sa a hannun mai ɗakina Hajiya Halima wanda a lokacin ita ta haihu amma yarinyar ba ta zo da rai da ba, ita ta shayar da shi ta kuma raine shi har ya zama mutum ta nuna masa ƙauna da kulawa don na ce da ita tsintar sa aka yi a cikin bola an yasar da shi shi ne dalilin da ya sa na ɗauke. Kusancin da yake da shi da ni da iyalina da kuma ƴancin da yake da shi a cikin gidan nan babu wanda za a gaya wa cewar ba ni na haife shi ba ya yarda". Take jikina gabaɗaya ya soma rawa sa boda ban taɓa tunanin amsar da zai furta ba ke nan, tabbas sai yanzu na ƙara tabbatar da cewar sanin ainihin halin mutum sai Ubangijin da ya halicce sa, muryarsa ce ta dawo da ni cikin duniyar zahiri daga na tunanin da na yi nisan kiwo a cikinsa. "Zo ki zauna a nan gefena mana ƴan mata". Rawan da jikina yake ya ƙara tsananta ba ni da wani mafita illa na yi abin da ya ce mussamman da na lura babu wani ƙarfi a jikinsa hatta maganar da yake yi ƙarfin hali ne kawai da taurin rai gami da kaifin da linzamin bakinsa yake da shi. A hankali na soma tako wa ina ɗaga ƙafata har na iso inda yake zaune zan zauna ke nan ya damƙo tulin gashin kaina da na tufke shi ta bayan wuyana ya riƙe tamau tamkar zai cire su. "Me ye kika sa min a cikin shayin da na sha?". Ya jefa mini tambayar da ta haifar mini da rawan jiki da harbawan zuciya fiye da kima a kimiyyance. Na yi ƙarfin halin faɗin"ni babu abin da na saka maka, ka sakar mini gashina". Ya riƙe mini gashi tamau har sai da na ji kaina kamar kaina zai faɗo ƙasa, duk jijiyoyin kaina na ci sun riƙe har sai da idanuna suka soma rufe ba, numfashi yana ta sama da ƙasa sai da ya yi yin sa ya hankaɗa ni gefe na faɗi sai a lokacin na samu na kwace kaina, na tashi na koma can ƙarshen ɗakin ina kallonsa, yayin da ya zame ya kwanta akan kujerar ƙafafunsa suna reto ya soma wani nauyayyen bacci da hakan ya haifar mini da sauƙe wasu wahalallun ajiyan zuciya masu nauyin gaske. Na ɗan matso inda yake a tsorace na tabbatar da cewar ya yi nisa a baccin da ya yi. Na durƙushe akan gwiwoyina yayin da wani kuka mai ƙarfi yake kufɓe mini ji nake yi raina gabaɗaya yana tugunzuma, sai a lokacin na raruma wayar na kashe naɗar sautin da nake yi. Sosai nake kukan kamar raina zai fita daga cikin gangar jikina yayin da kalaman da Sheik suke yi mini amsa-kuwwa a cikin naƙurar naɗar sautina ji nake yi tamkar a lokacin yake furzo zantukan. Ƙirjina ya yi mini nauyin gaske tamkar wacce aka yi mini ajiyar dutsen dala ba gammo haka na kwana ina kuka wajajen ƙarfe uku da rabi na daren na ji an buɗo ƙofar ɗakin na yi zumbur na tashi tsaye. Deeno ne da Zinariya suka shigo cikin ɗakin muna haɗa ido da ita na tafi da hanzarina na je na rumgume ta tsam a jikina ban san sa'ilin da wani kukan ya kuma ƙwace mini a karo na barkatai. Ta ɗago ni daga jikinta ta na share mini hawayen fuskana"Ina fatan komai ya tafi yadda muka tsara ko?". Na gyaɗa mata kaina alamar e yayin da wasu hawayen suke ta ambaliya a bisa dandamalin fuskana. Ta riƙo hannuna muka tattare kayan da na shigo da shi muka mayar cikin jakar muka fice daga cikin ɗakin, na shiga banɗaki na wanko fuskana na zo na gyara ta na zauna akan hannun kujerar da yake kwance a kai na ɗan ranƙwafo kaina daidai fuskarsa Zinariya ta kafta mana hoto, sai da na sauya wurare aƙalla sau uku ta na ɗauka mana hoton kana muka fita daga cikin ɗakin. Sai da muka sauƙa ƙasa muka shiga wani ɗan madaidaicin ɗaki da ki rabin wancan bai kai a girma ba balle kuma a zo batun kayan alatun da suke jibge a cikinsa, muna shiga ciki na zube akan gadon tamkar wacce ba ta san ciwon jikinta ba na ci gaba da reron kukan. Ɗaukar wayar Zinariya ta yi ta kunna sautin da na naɗa tana sauraro ita da Deen yayin da duk suka tattara hankulansu a wajen guda, ba su tsagaita ba har sai da suka saurara tsaf. "Tabbas wannan abun babban lamari ne. Hakiƙa kin yi abin da ya dace a yaba miki". Deeno ya yi zancen cikin jinjin girman ƙoƙarin da na yi. Zinariya ta ɗago ni daga kwancen da nake na zauna kana ta zuba mini ido muryarta cike da rauni ta ce"Amatullah da gaske a rayuwarki ta baya kin taɓa zubar da ciki? Sannan baƙin cikinki ne ya yi sanadiyyar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98