Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 55

Chapter 55

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,207 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

da na tashi na tsaya tsam akan ƙafafuna ba, ban ko kalla inda yake ba balle na tanka masa na ɗauki abubuwan da na yi amfani da su na koma kicin ɗin na fita ta ƙofar baya na shanya tsumman akan igiya kana na dawo na fito. Idanuna har wani baƙin duhu suke gano mini da ƙyar na kai kaina cikin ɗakin Altine ina tura ƙofa na hange ta tsaye ta riƙe ƙugu tana fuskantar ƙofar shigo wa. Ban bi ta kan ta na ɗauki sallaya zan shimfiɗa don na kwantar sa boda ciwon kai da jirin da nake ji, ta yi wuf ta wafce sallayan daga hannuna. "Allah ya kiyaye Karuwa wacce take zaman kanta ta ɗaura wani sashin jikinta, akan sallayan da nake yin ibada a kansa". Na yi ƙuri da ido ina kallonta sai dai bai ko kaɗan ban yi mamakin furucinta ba, don ina da tabbacin in dai tana cikin gidan ɗazun dole ta ji kuma ta san abin da ya faru. Waje na nema zan zauna a ƙasa na ji an ture ni har sai da kaina ya bugu da jikin ginin ɗakin, wani zafi ya ratsa har cikin kwanyata. Na cira kai ina duban ta tare da sauraron zantukan da ta ɗaura da faɗinsu. "Kin yi asara kin ji kunyar duniya da kuma lahira. Ashe duk kallon da ake yi miki kura ce lulluɓe da fatar akuya, ashe lumbu-lumbu ne wutar ƙaiƙayi. Wallahi kin yi asara har yawon otel-otel kike yi da ƙartin maza, in sha Allah daga rana mai kamar ta yau zamanki a cikin gidan nan ya zo ƙarshe don sai na tone asirin da kika haƙa rami kika burne shi a gaban Hajiya da kowa da kowa a cikin gidan nan". "Allah ya ba ki sa'a". Na furta a taƙaice sa boda ba zan iya dogon magana ba balle na sama ƙwarin gwiwa, nutsuwa da kuma kuzarin yi mata bayani sala-sala. Na zauna tare da kifa kaina da gwiwa ina sauƙe ajiyar numfashi akai-akai, ban yi aune ba na ji a finciko hannuna tamkar za ta tsinke sa daga jikin gangar jikina. Cak ta miƙa da ni akan ƙafafuna ta finciko ni zuwa waje ja na take yi tamkar dabba duk da ina cijewa tare da turjewa lamarin ya fi ƙarfina. Ba ta sake ni ba har sai da ta fito da ni harabar gidan ta yi jifa da ni gefe guda na faɗi ƙasa akan gwiwan hannuna. Daidai lokacin da motar Hajiya Muhibbat ta shigo cikin gidan, har ta gama daidaita parking ban ɗago kaina ba sa boda azabar zafin buguwar da na yi a hannuna har na ji hannun ya sake sosai, ina jin shi tamkar bai kasance ɗaya daga cikin wani ɓangaren gaɓoɓin jikina ba. "Altine lafiya na gan ku a nan?". Muryar Hajiya ya ratsa ƙofofin kunnuwana da hakan ya ba ni damar ɗago kaina, kafin Altine ta ba ta amsa Saif ya iso wajen a hanzarce. "Me ye yake faru wa?". "Ina ka ga yanzu shigo wa ta na tarar da su a haka. Me yake faru wa Altine ki yi mana bayani me ye Amatullah ɗin ta yi na ga kin jawo ta waje haka? Wani abun ta ɗauka ko kuma kama ta kika yi laifin ha'inci?". "Hajiya ai gwara sata akan munin abin da ta aika". "Me ye ta aikata?". "Hajiya ashe wannan yarinar karuwa ce, a cikin gidan karuwai da ƴan daudu tambaɗaɗɗun mutane da suka kwashe kayansu daga zauren Ma'aiki take rayuwa". Cike da mamaki Hajiya ta ce"Karuwa kuma Amatullah ɗin?". "Ƙwarai kuwa ranki ya daɗe, ai ba a ƙarya kusa da gida ga ta nan ki tambaye ta idan ƙarya nake yi mata ko kuma na yi kuskure cikin maganganuna". Altine ta yi furucin cike da ƙwarin gwiwar da ya gauraye da karfin hali da zumuɗin bankaɗo sirrina. [12/13, 12:57 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam _____________________________________ Page 6️⃣8️⃣ Cike da ruɗu Hajiya Muhibbat ta ce"wani irin magana kike faɗa haka Altine? Anya ki na cikin hankali da hayyacinki kuwa? A ina kika ji wannan maganar?". "Hajiya ina cikin hayyacina sannan hankalina ma yana nan tare da ni har ki yi imanin cewar wai ba na cikin hayyacina. Da kunnena na ji Yallaɓai Saif yana tuhumarta akan wannan zancen, kuma shi ma ya san da wannan zancen ga shi a tsaya ki na da damar da za ki tambaye shi idan har ba ki yarda ba". "Saifullah me ye gaskiyar abin da Altine take faɗa? Shin da gaske ne Amatullah karuwa ce kuma zaman kanta take yi a cikin gidan karuwai da ƴan daudu?". Runtse idanunsa ya yi yana cije leɓansa tare da zuba hannayensa cikin ajihun wandon farin shaddan da yake jikinsa. "Kai nake sauraro Saif". Maganar da ta yi a karo na biyu ya sanya shi buɗe lumshashshun idanunsa muryarsa can ƙasan maƙoshinsa ya soma maganar a hankali. "Anty haka ne a cikin gidan karuwai take rayuwa amma akwai wani abu guda wanda ba mu san da shi ba......". Ban bar shi ya ƙarisa ba ta yi wuf na amshe zancen yayin da nake tashi tsaye daga faɗuwar da na yi akan hannuna. "Kar ki tsawaita bincike a kaina Hajiya don ina da tabbacin binciken ba zai haifar miki da ɗa mai ido ba, babu komai a cikin tarihin rayuwata face ƙunci, tashin hankali da kuma ruɗani. Ƙaddarar rayuwata ta bambanta da na ko wacce yarinya mai irin shekaruna. Tun kafin na yi girman bambamce tsakanin fari da baƙi na san mene ne baƙin ciki kuma na san ɗanɗanonsa, babu kuskure a cikin dukkan abin da Altine ta faɗa tabbas haka ne a cikin gidan karuwai nake rayuwa kuma zaman kaina nake yi ba a gaban iyayena, ƴan uwa ko dangi nake ba gashin kaina nake ji babu kwaɓa babu mai tsawartawa balle wanda zai kama hannuna ya ɗaura ni a hanyan da take daidai. Sai dai tun da nake ban taɓa aikata zina ban taɓa kusantarsa sai dai na yi imanin cewa dukkanin wani Bawa ba ta taɓa wuce ƙaddararsa". "Babu wani mai hankalin da za ki faɗa wa wannan maganganun ƙanzon kuregen nakin ya yarda da ke. Ta ya ya za a ce kin rayu a cikin tsakiyar karuwai ba tare da ki na aikata abin da suke yin ado da shi ba, to in ma haka ne ba ki aikata ba ɗin me ye kike zaman kanki?". Na runtse idanuna da hakan ya ba wa hawaye. Da sur ciki mini kurmin idaniyata damar kwaranya, ina jin wani zafi a cikin raina tamkar ana watsa mini tafashashshen ruwan dalman da ba sirka shi da komai ba a cikin farfajiyar ƙirjina. "Ban faɗa don neman yardarki ba sannan ban damu da ko wani irin kallo za ki yi mini, Abu ɗaya na sani kuma a kansa zan tsaya har ƙarshen rayuwata shi ne iya gaskiya ta na faɗa muku. Hajiya ina mai ba ki haƙuri akan ɓoye miki gaskiyar wace ce ni da na yi har tsawon wannan lokacin, haƙiƙa a ɗan zaman da na yi da ke na ga zallar ƙauna da tausayinki a gare kwance a cikin idanunki. Ban yi hakan da wani nufi ba kuma Allah shi ne shaida ta akan hakan.....".

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});