Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 6

Chapter 6

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,214 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kafin san haramcin abun a addinance nake jin tsanarsa a cikin raina. Mutane da yawa sun sha kawo min farmaƙi Allah yana kuɓutar da ni, da kuma taimakon Ummata don ita ma ba ta yarda na yi irin rayuwar da take yi ba tana ba n tsaro da kariya ta kowacce fuska". Ƙirjina ya yi mini nauyin gaske da na kasa cewa komai illa bin ta da ido nake yi, ganin yanayin da na shiga ya sa ta sauya maganan. "Ina ta suturu ma na mance ba na nuna miki wuraren". Na saki taƙaitaccen murmushi da hakan ya ba ta damar ɗaura daga inda ta tsaya"kin ga layin nan shi ne layin na isa. Duk wanda kika gani ya fito daga cikin layin nan to ya ci ya tada kai ne, don duk wanda ya zo ya gina muhalli a cikin layin wani ƙusa ne daga gwamnatin ko kuma wani hamshaƙin ɗan kasuwa, ko kuwa irin wanda iyayensu suke sato kuɗin gwamnatin su tara musu idan aka rasa abin da a yi da shi sai a zo nan a gidan gidaje da shi, ana zuwa hutawa duk ranakun ƙarshen mako mafi yawan ƴan matan gidanmu nan suke zuwa suna sheƙe ayarsu da zaran yamma ta kawo kai za ki ga kowacce yarinya mai ji da kanta ta ci kwalliya ta zo bakin layin nan ta tsaya daidai lokacin da masu gidajen suke dawowa daga aiki, idan kin kasance cikin masu rabo daga nan sai ki dace wani Alhajin ya yi wuf da ke shikenan kakarki ta yanke saƙa". Na sauƙe numfashi mai nauyi ina ƙarewa faɗin layin kallo sai da na ƙare masa kallon tsaf kafin na furta"Lalle kuwa layin na isa, ga tankama-tankaman gidaje da shimfiɗaɗɗun tituna". "Sai ma kin ga cikin gidansu aljannar duniya kenan, ga faffaɗan filin tsakar gida ya kai rabin wani unguwan". "To su ina matayensu da suke cin karensu babu babbaka, ko ba su da iyali ne?". "Su na da su wasu sun su ma har da ƴaƴansu. Sai dai mataye da ƴaƴansu duk suna can Abuja birnin tarayya wasu ma ba sa ƙasar gabaɗaya. Nan gidan kawai wajen shaƙatawa ne da more rayuwar duniya". Na ji shuru ina ƙara bin layin da kallo shuru yake ko'ina babu hayaniyar kowa da alama kowa yana cikin gidajensu ba sa fitowa sai da wani dalili mai ƙwari. Muka ci gaba da tafiya ina ta kallon layin da manyan gidajensu, haka muka karaɗe dukkan girman layin daga nan suka gargaɗa har cikin kasuwa ta nuna mini wurare da yawa, ba mu dawo ba sai da gari ta soma duhu daga yanayin duhun garin na tabbatar da cewa an yi ƙiran sallan magrib. Muna dawowa gidan muka iske manyan motoci a ƙofan gidan tamkar ana gudanar da gagarumin biki ko kuma walima. Ga mutane maza da mata tsaye cirko-cirko a ƙofar gidan, maza kama daga kan samari, tsaka tsakiya da kuma dattawa babban wani abin takaici har wa manyan mutane da aƙalla za su kai sa'an Abbana a shekaru. Sai da muka rarraɓe kafin muka sama hanyar shiga cikin gidan kowacce budurwa ta ci wanka ta caɓa ado kamar za su tafi gasar kyau na duniya. Kowacce ta tsuke cikin ɗamammun kayan da ba su tamaika da komai wacce rufe tsiraicinsu ba, ga ƙarin gashi da farata rututu a hannayensu kamar masu cin moshe. Na buɗe ƙofar ɗakina na shiga na hango wasu baƙaƙen ledodi guda biyu na saki hamdala don na kwaso yunwa kamar zan ci babu, na zauna na jawo ledar ina buɗe wa biredi ne da wainar fulawa guda biyar a leda sai kuma ruwan shayi ƙulle a leda, gefe guda kuma ga can ledar pure water an jingine a gefe. Na san babu wanda zai kawo mini wannan abun face Aminu don haka ban yi wata-wata na ɓula ruwan shayin na tsoma zuƙa ina haɗawa da buredi ina danne wa da wainar fulawan sai da na ci wainar guda uku na zuƙe ruwan shayin na ɗaura da ruwan pure water ɗaya na yi hamdala na tashi na ɗauri pure water ɗaya na zuba a buta na fito na yi alwala na koma ciki. Sallan magrib na yi ban tashi daga wajen ba har sai da na yi sallan isha'i, na zauna na zabga tagumi tamkar wacce aka aikowa da saƙon mutuwar uwa da ubanta. Tunani barkatai suka dinga yi mini yawa a cikin kaina suna kai kawo a cikin kwanyata. Tunanin gida da ƴan uwana suka faɗo mini a raina tamkar faɗuwar aradu, ban san sa'ilin da hawaye suka fara kwaranyo mini daga idanuna ba kamar da bakin ƙwarya. "Anty Sawwama ki gafarce ni babu yadda zan yi ne ba ni da wani mafita saman da wannan. Ya zama dole ne na yi nisa da ku ko don kwanciyar hankalinku da nawa rayuwata ta gama tarwatsewa don haka ba zan zama matsala a cikin taku rayuwar ba". A bayyane na yi maganar wasu hawayen suna rige-rigen fitowa daga idanuna suna wanke mini fuska yayin da suke sauƙa har izuwa tudun wuyana, na daɗe ina kukan da dukkan ƙarfina har sai da numfashina ya soma sarkafewa kafin na zame na kwanta akan bayana ina kallon rufin ɗakin da ya zama shamaki tsakanina da sararin samaniya. Kamar daga sama na ji sauƙar muryan La'aniyatu a na'urar naɗan sautina. "Har kin kwanta ne?". Na tashi na zauna"a'a yaushe kika shigo ban ji ko sallamarki ba?". Ba ta amsa mini ba har sai da ta nema waje ta zauna kana ta ce"ban yi sallamar ba ne, daman na zo ne mu yi hira don Ummata ta yi baƙi daga wata ƙasa daban sun tafi otel za su gana". Na waro idanuna waje cike da mamaki"a cikin daren nan?". Ta riƙe haɓa"yo mai ma aka yi da maza? Ai duk wani taron da za a yi wanda manyan mutane za su halarce shi to cikin duhun daren yin sa tare da taƙaitattun mutane". Na jinjina kai tare da kawar da zancen ta hanyar faɗin"ina so na nema aikin da zan yi na dinga rufawa kaina asiri, ni wallahi ko wankau ne ma ko surfe zan yi". Ta bi ni da wani irin kallo kwatankwacin irin kallon da mai hankali yake yi wa zautacce. "Yanzu ke a layin nan kin ga alamar wanda gidan da za su kawo surfe? Ai tuni bature ya kawo sauƙi ban ƙi ba dai wankau ɗin". Na yi saurin faɗin"don Allah ina san samu wankau ɗin?". Ta ɗan yi shuru kafin ta ce"gaskiya ba na ce ba don gidajen layin nan ma ba su cika zama ba amma dai ba za a rasa ba, wataƙila sai dai ki dinga bin gida-gida ki za a dace". Jikina gabaɗaya ya yi sanyi ƙalau kamar kazar da aka watsawa ruwan gishiri na tuna rayuwata ta baya lokacin da Abba yake raye a cikin duniya, rayuwa kenan wai yau a ce nake neman aikin wankau don na ciyar da kaina, hasali a lokacin baya ba a taɓa sauƙe tukunya a cikin gidanmu sai dai ba daɗi amma tabbas za mu ci mu ƙoshi. Ko ruwan da za mu jiƙa maƙoshinmu bai taɓa yanke mana ba. Na ja dogon numfashi na fesar ina zabga tagumi. "Lafiya kuwa na ga duk

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});