Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 47

Chapter 47

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,208 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

shin addini ya haramta hakan ne da na cancanci wannan azabtarwan?". Na yi shuru ina tunanin ta inda zan fara kafin can na soma cewa"ki miƙa lamurranki zuwa ga Allah don shi kaɗai ne zai kawo miki mafita da sauƙin halin da kika tsinci kanki a ciki. Duk duniya babu wanda zai iya yaye miki damuwarki sama da wanda ya ɗaura miki. Ki yi sallan dare ki kai goshinki ƙasa ki yi Allah kuka ki sanar da shi damuwa da matsalolinki, ki roƙe sa cike da yaƙinin cewar zai amsa miki kuma ya yi miki zaɓi mafi zama alkhairi a gare ki. Ki yi azumi ki yi sadaka sannan ki yawaita karatun alƙur'ani don yana samar da nutsuwa a zuciyar da babu ita, ya haifar da kwanciyar hankali da salama a ciki ruhin da babu ita sannan ya na wanke ƙwaƙwalwa ya kuma daidata tunani". Ta sauƙe wani gauron ajiyar zuciyarta da har sai da na ji sautinsa kafin ta ce"na gode in sha Allah zan yi duk yadda kika ce. Na gode sosai da wannan shawaran". Ina ɗago kaina idanuna suka sauƙa akan Altine da take ƙarisowa inda muke ta murtuƙe fuskarta marar annurin nan tamau, da hakan ya ba ni cikakken tabbacin ta saurara duk abin da muke zanta da Hajiya. "Hajiya sannu da hutawa, daman na zo mu yi wata magana". Ta yi zancen yayin da take zauna wa kusa da ƙafafun Hajiyar. "Ina jinki". "Ki ɗan ba mu waje ko". Murmushi kawai na yi na tashi na ba su waje na koma cikin ɗakin Altine na zauna, ganin zaman ba zai kai ni ko'ina ba. Hakan ya sanya ni ɗaukar alƙur'anin da na gani ajiye dirowa na fara karantawa. Ban yi nisa ina yi ba Altine ta shigo ta amshe ƙur'anin daga hannuna ta rufe ta ajiye shi a gefe guda, ta zauna tana fuskantana tare da haɗe hannayenta wajen guda. "Amatullah kike ko?". "Ƙwarai ba ki yi kuskure Amatullah nake". Ta gyaɗa kanta"ina so na yi miki gargaɗi na farko wanda shi za kasance shi ne na ƙarshe da zan yi miki wanda matuƙar ki na ƙaunar ci gaba da zama a cikin gidan nan dole ki yi bi abin da zan gindaya miki. Kin ga wannan shishshigewan da kike yi wa Hajiya da zummar samun wajen zama babu inda zai kai ki, sai dai ma ya sauƙe ki a tashar ƙasƙanci. Na ji har wani banzan shawara kike ba ta ke a dole kin cika kin batse, to daga yau na ja miki jan layi tsakaninki da Hajiya iyakan cin ki da ita gaisuwa ce daga nan kuma sai gobe". Tun da ta fara zancen nake bin ta da kallo har ta tsaya a madakata. Ban yi mamaki don izuwa yanzu in da sabo ya ci ace na saba da halinta. Murmushi kawai na yi na ce"yadda kika ce haka za a yi ranki ya daɗe". Ina rufe bakina na tashi na je na yi alwalan sallan zuhur na zo na gabatar da salla a daɗe zaune akan sallayan har sai da na ji wani bacci-bacci ya soma ɗauka ta kana na tashi na ɗauki alƙur'anin na ci gaba da karatuna ban daga wajen ba sai da na yi sallan asr, na fita kicin na haɗa abincin rana na zo na jere shi akan dinning table lokacin Hajiya ba ta cikin falon, haka nan ban ga su Ayan ba Wanda na fi kyautata zaton ko su na can wajen Saif. Don na leƙa ta taga na ga motarsa tana cikin gidan da hakan ya ba ni tabbacin cewar bai fita ba. Sai da na ci nawa abincin kana na fito falo na kuwa yi sa'a lokacin Hajiya ta fito sai dai da alamar fita za ta yi don mayafinta yana saƙale a bisa kafaɗunta. Na duƙa na yi mata sannu ta amsa mini fuskarta babu yabo babu fallasa. "Hajiya daman mun gama duk wasu ayyuka ne shi ne nake son na je gida. Inda wani abun zuwa an jima sai na dawo". "Ba damuwa ni ma daman fita zan yi yanzu, Su Aryan suna ɗakina suna bacci sai ki sanarwa Altine ta na duba su". "To in sha Allah, a dawo lafiya". Har ta yi gaba sai kuma ya dawo da baya"an kai abincin Saif ne?". Na jijjiga mata kaina alamar a'a da hakan ya ba ta damar zarce wa da faɗin"ya kamata a kai masa sai a fito da kwanukan safen". Kaina kawai na gyaɗa mata da hakan ya ba ta damar ficewa daga cikin falon, na fita da kallo har sai da ta ɓace wa ganina kana na juya na je na haɗa masa abincin na ɗaura akan tray na nufi sashinsa. Haka kawai a duk sa'ilin da na nufi sashin nake tsintar kaina cikin matsanancin faɗuwa gaban da ban san dalilinsa ba. Sai da na ja dogon numfashi kana na sama ƙwarin gwiwar tura ƙofar falon haɗe da sallama na shiga ciki, yana nan kwance inda na same shi da safe da dukkan alamu tun da na bar shi bai gusa daga wajen ba, na ajiye abincin kana na ɗauki tray ɗin da na kawo da safe. Na ga alamun ko buɗe wa ba ayi ba balle a ci. "Ranki ya daɗe a fitar da abincin safen nan tun da ga na rana an kawo?". Na yi tambayar jikina yana rawa. Na yi shuru bai tanka mini ba hakan ya sa ni buɗe plate ɗin don gani da idona cikin rashin sa'a ya zame ya faɗi zuwa ƙasa take ya tarwatse ya yi ɗaɗɗaya. Ƙarar ya gigita ni har sai da na runtse idanuna na ajiye tray ɗin hannuna ina tattare wanda ya fashe ɗin. "Ranka ya daɗe ka yi haƙuri kuskure ba da niyya na yi ba". Tsit na ji ba a amsa mini har na gama tattarawa na zuwa a gefen tray na juyo na ga yana nan inda yake kwance bai motsa. Haka kawai na ji ƙirjina ya buga na zo na tsaya a gabansa ina ƙiran sunansa amma shuru bai ko motsa ƴatsunsa ba, balle wani gaɓa daga jikinsa. Ina janye matashin da ya rumgume a ƙirjinsa na ga hannunsa ya faɗo ƙasa jikinsa ya sake, ban san lokacin da na yi jifa da matashin ina sakin salati da sallallami ba tsabar gigicewa da kiɗimewar da na yi. [12/7, 1:15 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ______________________________________ Page 6️⃣4️⃣ Na rasa abin da ya dace na yi sai kai komo nake yi a cikin falon rumgume da hannayena a bisa ƙirjina, na rasa wanda zan je na sanar wa halin da yake ciki ga shi Hajiya ba ta nan ta fita, na zo na tsuguna a gabansa ina bubbuga hannun kujerar da yake kwance a kaina tare da ƙiran sunansa. "Ranka ya daɗe don Allah ka tashi ka buɗe idanunka". Shuru bai amsa ba kamar yadda bai motsa ko da ƴatsun hannunsa ba, hakan ya ƙara gigita dukkan nutsuwar da ya yi saura a gangar jikina da har ban san lokacin da hawaye suka ambaliya a bisa dakalin fuskata ba. Altine ce ta faɗo mini a ciki raina na yi zumbur na miƙe da nufin na je na sanar da ita halin da na

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});