Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 99

Chapter 99

A Rubuce Take Book 1 Complete Hausa Novel – Widad and the Secret of House 1,338 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

wayar "Ba kiranki akeyi ba ki daga" fuska ta kwabe sannan ta girgiza kanta,bai sake cewa komai ba ya matsa wajen kujerar da yakan zauna yayi karatu da asuba ya jawota ya zauna,sai widad din ta miqe a hankali ta nade abun sallar nata,ta nufi qofar fita a dakin "Ina zuwa?" Waiwayowa tayi "Xanje gaida hajiya" sai ya gyada mata kai kawai. Daga inda yake zaunen yana hangen hasken da wayar taketa yi,yadda aketa kira ba qaqqautawa ya bashi mamaki,ba tare daya shirya ba ya miqe,ya isa ga wayar ya dauko,sai yaga sunan mommy hafsat,abun ya daure masa kai,ya juya yana duba wayarsa waiko zaiga miscall dinta,may be ta kirashi ne baya kusa bai daga ba,wani abun kuma ya faru,amma sai yaga babu kiranta ko daya,ya daga wayar ya kara a kunnensa tare da yin sallama. Jin muryarsa ya qarasa fadar mata da gaba,jikinta gaba daya yayi laushi,ta saki abun sallar a qasa,da gaske suna tare,tare suka kwana,kasa motsawa bakinta yayi,ta riga data samu amsar abinda take nema,don haka ta kashe wayar tare da sulalewa a wajen ta saki wani irin kuka mai tsananin zafi da cin rai,shikenan,ta faru ts qare. Jin alamun an katse ya sashi daga wayar ya kalli screen din wayar,sai yadan tabe baki ya maida wayar ya ajjiye,har ya taka zai bar wajen sai hoton fuskar wayar ya dauki hankalinsa,ya koma ya sake dauka,ya koma saman kujerar ya zauna,ya buda gallery ya soma kallon pictures din a hankali har baisan sanda murmushi ya dinga kubcewa daga fuskarsa ba,kowanne hoto da kalar quruciyar da za'a nuna a jiki. Hannunsa ya miqa,ya dauki wayarsa ya buda,yayi marking wasu daga ciki ya tura. Ranar kaf qin yarda tayi ta sake komawa dakinsa,ko hanya qin yarda tayi su hada dashi,tana tsakanin dakin hajiya da kitchen,bayan sun hada breakfast ita da muneera suka shirya komai a falo,tare sukayi break din har hajiyan,sunayi ana taba hira,da suka gama suka sake gyare gidan tare,shi da hajiyan suna dai falo suna hira,a nan sukaci abincin ranar tare da hajiyan,sannan ya koma daki ya shirya ya fice. A daren ranar yana zaune daga bakin gadon sa,qaramin littafin addu'o'i ne a hannunsa yana karantawa,ya gama komai,kammala addu'arka ne kawai ya rage masa,amma sam baiji motsinta ba,lokaci lokaci yana daga kai ya kalli bakin qofar dakin nasa a haka har ya kammala addu'ar,ya aje littafin gefen bedside ya zuro qafafunsa ya zura bedroom slippers dinsa ya miqe a hankali ya fito daga dakin. Babu kowa a falon,amma yaga dakinta a bude,yasan suna ciki,yayi gaba zuwa dakin,ya tura qofar bakinsa dauke da sallama. Dukkansu suka amsa,hajiya na zaune gefan gado,muneera da widad na saman qaramin carpet din dake shimfide qasan dakin,muneeran na maidawa weedad kalbar kanta da santsin kan ya sanya ta ware kamar ba'a taba yinta ba,bataso a taba mata kai tana ta qorafi muneeran na fadin saita yi mata,hajiya na goyuwa da bayan weedad din. Kadan ya kalli sashen da suke,ya qaraso ciki,ya samu gefan hajiya ya zauna "Bakiyi bacci ba hajiya?" Sai tayi murmushi "Banyi ba,ina dai shiri" "to yayi kyau,kin hada komai naki waje daya ko?, saboda gobe sha biyu zamu fita" "Komai a kammale yake" "Ma sha Allah.....shikenan,dama zuwa nayi nai miki sallama,sai da safe" "To Allah ya bamu alkhairi ya tashemu lafiya" sai ya juya yana ficewa a dakin,minti biyu hajiyan ta kalli widad "Maza tashi ki tafi ki kwanta kin baro mijinki,nikam sai da safenku" dif widad tayi,don ita gaba daya ta gama tsarin kwana a nan din,ta dan dubi muneera taga itama ta fara shirin kwanciyar,dole ta miqe,ta dauki siririn gyalen abayarta ta dora saman kanta,ta bude closet dinta ta dauki rigar bacci tayi musu sai da safe ta fita. A sanyaye ta tura qofar dakin tashiga da sallama,yana zaune daga bakin gado yana amsa waya,haka kawai yaji sanyi har cikin ransa sanda yaga ta shigo din,bandaki ta wuce,ta fidda kayan jikinta tayi wanka,don zuwa yanzu tayi mugun sabo da wankan dare,ta shirya cikin kayan baccin ta fito. Dim light ne a dakin,yana iya hangen sanda ta fito da kuma hawanta saman gadon,taja duvet ta kwanta ba tare data ce komai ba,qaramin murmushi ya saki,abinda ya faru jiya yana dawo masa,sai ya samu kansa da janyo wayarsa,ya duba wajen music ya lalubo kukan magen jiya ya saka. Curewa tayi waje daya,tun tana iya ganin zata jure harta kasa,sannu sannu sai gata cikin jikinsa ta cukuikuye shi,ya saki murmushin nasara ya sanya hannunsa ya lullubeta cikin qirjinsa yana sakin murmushi,ita kuna tayi lamo tana sauraren bugun zuciyarsa da nata da kowannensu ke fita da sauri da sauri. *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 65 "Tom.....zamu tafi" abbas ya fada yana duban qwayar idanun widad din,hannunsa zube a aljihun wandon lallausan yadinsa da aka yiwa wani irin dinkin girma. Daga kai tayi da nufin kallonsa,duk yadda taso ya hadiye abinda takeji a qasan ranta amma ta kasa,dole haka ta saka qwayar idanunta a tasa,dai dai sanda hawayen da take riqewa ya sulmiyo daga idanunta,maganar da zatayi ta riqe mata a maqoshi,sai ta saki kuka sosai,abind aya tilasta mata saka tafukan hannayenta duka biyun ta lullube fuskarta dasu. Duka idanunsa ya fiddo,ya ciro hannayensa yana matsowa inda take tsaye "What's happening weedad?" Kai ta girgiza masa,saidai kukan take har yanxu "Noo....noo,kada muyi haka dake mana uhnnn?" Ya fadi a tausashe,sai ya sake matsawa gabanta,ya saka duka hannuwansa ya zare nata tafukan hannayen daga fuskar tata yana kallonta "I will be back in sha Allah.....ki daina kukan nan,yana qona ni,zuciyata tana zafi.....ko kinaso nima nayi kukan?" Ya fadi yana jin wani irin rauni da bai taba jin kamarsa ba,kanta ta girgiza amma ta gaza tsaida hawayen "It's okay,i promise you bazamu dade ba,shikenan?"saita sake jinjina masa kai,haka kawai takeji wani tashin hankali da rashin sukuni a tattare da ita,sai takejin kamar zai tafi ya barta,kamar bazai dawo ba,tana jin kamar an dauke wani muhimmin sashe ne a jikinta,batasan wanne irin feeling bane wannan,tsahon rayuwarta bata taba fuskantar irinsa ba. Tas yasa soft handkerchief dinsa ya goge mata hawayen,sannan ya bude tafin hannunta ya saka mata shi,ya maida ya dunqule hannun nata cikin nasa,sai yaja da baya kadan yana gyara zaman rigarsa data cukuikuye yana kallonta,cikin ransa yakejin wani shauqi yana saukar masa,ganin wani yana kewarka.....ya shiga damuwa saboda zaiyi rashinka a kusa dashi......wani irin dadi kima da daraja gareshi a zuciya,wani irin yanayi da bazaice ga lokaci na qarshe daya ganshi tattare da matarsa ba,sai ya buda dukkanin hannayensa yana kallonta da idanunsa masu girma da zuwa yanzu suka rusuna,girmansu ya ragu "Oya.... give me a hug" jiqaqqun idanunta ta daga ta kalleshi,qaramin miskilin murmushinta ya subuce zuwa saman labbanta,a yau din sai taji bata shakkar yin hakan,ta fara takawa a hankali kamar wadda aka sakawa wani kida na musamman,yayin da idanunsa yaji sun fara narkewa a kallonta,cat walking takeyi,irin tafiyar da sai wance da wance cikin isassun mata,bai taba lura da hakan ba sai yau,ya qaraso gareshi a hankali,ta shige jikinsa kuwa gaba daya,harda qoqarin saka hannuwanta ta zagayo dasu ta bayansa,sai ya tallafa mata,ya durquso ya sakata sosai a jikin nasa,yana jin kamar ya maidata cikinsa. Sun jima sosai a haka kafin ta fara janye jikinta,ya danyi baya jikinsa a mugun mace yana maida numfashi,kusan minti

Table of Contents

Chapters

155 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});