Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 30

Chapter 30

A Rubuce Take Book 1 Complete Hausa Novel – Widad and the Secret of House 1,310 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

mayi maganar,Allah ya tsare". Tsahon lokaci suka dauka shi da suraj din,saboda kwana biyu basu hadu ba,yanayin ayyuka da canjin muqamai da abbas din ke samu a kufi a kufi,anan suraj din ya samu damar masa qorafin "Naji mamaki sanda naji ka ajjiye appointment dinka,dama cefa da 'yan sanda da yawa suke jira" kansa ya shafo kadan yana duban suraj din "Nafi nutsuwa da hakanne suraj" "To kuma gashi sun biyoka da asp ba" "Gwara wannan kam,qarin matsayi ne,a tayamu da addu'a Allah ya bamu wuyan dauka da saukewa" "Ameen ya rahman". Bayan sun idar da magariba suka sake fita da suraj din a mota ya rakashi wani waje,a hanya ya tsaya qofan wani suya spot yana kashe motar "Kadan rakani ciki na yima hajiya siyayya mana" "Ba damuwa muje mana",tare suka jera xuwa cikin,suna tafe suna hira har suka isa,suka wuce kai tsaye inda zasu bada order din abinda sukazo siya din. Sun samu 'yammata biyu tsaye gaban kantar,wanna yasa abbas din ya bada taqi a tsakaninsu,ya tsaya daga baya baya suna ci gaba da magana da suraj din,irin hirar da ta shafesu. Tunda suka tsaya din gaba daya hankalinta ya karkata a kansa,ba qaramun daukan hankalinta abbas din yayi ba,shigar qananun kayan dake jikinsa sun taimaka wajen fidda surarshi ta qaqqarfan namiji,har suka gama biyan abinda zasu siya din,saita bude da duba wayarta tadan matsa gefe kadan tana cewa qawarta "Ina zuwa". Hankalinsa nakan suraj yana saurarensa yana saka order din abinda yakeso,har yaso yayi mistake ma saida waiter din yayi masa magana,aka hada masa komai ya irga kudin cikin wallet dinsa ya aje musu,saidai garin daukan ledan bai ankara ba ya dauki tata ledar,tana sane ta barshi har sai da isa gaban motarsa sannan yaji ana fadi cikin siririyar muryarta dake nuna zallar yauqi da gwalli "Hi.....hi,ranka ya dade" cak ya tsaya,don har ya bude murfin motar,ya waiwayo don ganin ko dashi ake. Da murmushi ta dinga jifansa har ta iso,cikin tausasa muryarta tace "Yallabai ledata ka dauke" ledar hannun nasa ya daga ya kalla,sai sannan ya lura,ya sauketa gami da miqa mata yana cewa "Sorry" "Ba laifi ai,hakan yayimun,kaga ko babu komai leda zata qulla mana zumunci" bai amsa mata ba illa amsar tasa ledar da yayi "Sunana rafi'ah" tayi saurin fada ganin yana shirin shigewa motarsa "Good,thank you ko" matsowa ta sakeyi don fa fuskanci rufewa zaiyi "Ko zan samu digits naka?" "Am sorry to say no" ya fada yana maida murfin motar a hankali ya rufe,sannan ya tashi motar yayi reverse suka fice daga wajen. "Har yanxu kana lokaci mutumina,bansan me yake fusgar hankalinsu ba haka,adan bani sirrin mana" ya fuskanci sarai abinda suraj yake fada,fuskarsa kadaram kadaham ya waiwayo kadan ya dubeshi sannan ya maida kansa ga titi "Kai har yanzu baka girma na suraj,ana ta neman na abincin da za'a kaiwa iyali kuma wa yake ta wannan" ya fada yana shafar habarsa dake zagaye da gemun daya samu wadataccen tsafta da gyara "Banga alama ba,don duk sanda muka fito irin haka sai wata ta taya" "To ai sai suyita yi,ta gidanma ya ka cika da ita bare ka sake daukan wata,kayita hadama kanka rigima da zafi,bazan iya daukan wannan ba" "Fada dai kake,bari ayi katari da wadda zata sace maka zuciya" "Haka kake gani" abbas ya maida masa amsa,hankali da idanunsa naga titi. Dariya kawai Suraj yayi,bai sake cewa komai ba suka shiga wata hirar. Sai daya fara sauke suraj a gida bayan ya hadashi da tashi ledar sannan ya koma gidan hajiyan. Bayan isha'i ya zauna sukaci abinci,kusan tare da hajiyan,saidai kowa kwanonsa daban,bayan sun kammala ya dauke kwanukan da kansa ya tattare wajen sannan ya dawo ya zauna yana fuskantar hajiyan "Hajiya kince zamuyi magana ko?" Gyara zamanta tayi sosai "Eh tabbas" "To ina jinki,Allah yasa ba wani laifi nayi ba" murmushi ta sake "Laifi abbas?,a'ah ko kadan,wani alkhairi na hango maka,na kumayi karambanin zartar maka dashi ba tare dana tuntube ka ba" qaramin murmushi ya saki "Hajiya...ai kinfi qarfin ki yiwa rayuwata karambani,kome kika ga dama ki zartar dashi kanki tsaye kawai" kai ta dan jinjina sannan tace "Aure na nema maka,'yar uwa ko 'yar muhsin" sosai gabansa ya fadi,abinda ya jima baiji irinsa ba tsahon rayuwarsa "Hajiya nujood?" Ya fada cikin fargaba,don ko da ya kasance itace bazai iya musawa hajiyan ba,haka zai auretan,yarinyar dake kallonsa a mazaunin ubanta "A'ah,widad" ajiyar zuciya ya sauke,sai yaji tashin hankalin da yake ciki din ya ragu,ya samu 'yar nutsuwa,duk da fahimci wa take nufi din ba,amma dai ya fahimci wata ce daban ba nujood ba "Inason kaje ka ganta,duk da ina zaton zuwansu gidan nan kamar ka taba ganinta,amma wannan zuwa ne na musamman,kaje ka gabatar mata da kanka" kai yadan sunkui qasa "In sha Allah hajiya zan saka rana sai na sanarwa muhsin din sai naje" har cikin ranta ta sake qaunar abbas din,tasan dama bashi da matsala kome kuwa tace yayi,saidai ta dauka zaiyi jayayya ko ya qalubalanci wannan danyan hukuncin nata. Duk yadda yaso ya fidda damuwa ya zauna suyi hira sosai amma ya kasa,jiki da zuciyarsa dukka a takure suke,dole bayan qarfe tara ya yiwa hajiyan sallama ya wuce gidansa. A kan hanya yana tuqi amma tunani ne fal kwanyarsa,aure?,wacece widad din ma?,oho shi bai ganeta ba,amma me hajiya ta hango masa?,sai Allah,bazai iya mata wannan tambayar titsiyen ba,da wannan damuwar da kuma tunanin ya isa gida. Bashi da hadi da sassan hafsa,don haka sassansa ya wuce,yabude ya shiga yana tsaye tsakar falon kamar maison tuna abinda ya kamata yayi wayarsa ta dauki sassanyan busar sarewar dake a mazaunin ringtone dinsa,don bayason ringtone mai hayaniya da yawa,mafi yawan lokutta ma yafi barin wayar tasa a vibration. Cikin wata kasala da gajiya da maganar hajiya ta saukar masa ya zaro wayar yana duba me kiran,hafsat dince,sai ya daga kiran yana neman kujera daya cikin falon ya zauna "Ina ka shiga ne inata kira baka daga ba" ta fada muryarta a tsaye carrr,alamun qagauta da son samun mutum,shuru yayi yana nazartar muryarta "Lafiya?" Ya fada da nutsatsiyar muryarsa mai nauyi,wadda ta dawo da hafsat din cikin nutsuwarta kadan,ta kuma fuskanci yanayin data masa magana baiyi dai dai ba,kishi ne keta cin ranta,har idanunta suka so rufewa,gani take kamar yana tare da wata ne shi yasa yaqi daga wayarta, "Ah....uhmm lafiya qalau,kawai hankalina ya dan tashi da naga inata kira baka daga ba" "Oh.....am fine,kufa?" "Lafiya qalau muke,yara gaba daya sunyi kewarka" "That's my babies.....kefa?" Ya fada yana danne damuwarsa,murmushi ta saki wanda ya jiyo sautinsa "To nima nayi" ta fada tana danjin nauyi,idanunsa ya lumshe yana kuma budesu,she's not romantic woman at all,ya rasa yadda zai canzata,kamar irin matan da soyayya bata damesu ba sam,dai dai da greetings cards da yake siya mata time to time,musamman idan yayi tafiya ya dawo bata wani daukar abun da muhimmanci,wani lokaci ma idan ya kawo cards din bata ko budesu bare ta karanta,karba take ta ajjiye bayan ta bishi da SANNU. "I miss you more than you can imagine" ya fada with softness,wanda har sai data ji tsigar jikinta ta tashi,wani abu ya tsarga mata,amma sai tace "Allah ya qara zumunci" "Zumunci dai?" Ya maimaita a ransa,even kalmomin da zatayi appreciating nasa bata dasu,har ya fara sabawa. Shurun da ya gilma tayi

Table of Contents

Chapters

155 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});