Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 129

Chapter 129

A Rubuce Take Book 1 Complete Hausa Novel – Widad and the Secret of House 1,312 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

babu wadda kejin dadin mu'amala da ita,idan sunzo gidan sai dole,kamar haihuwa da sauransu. Dukka hannayensa ya bude mata,yana mata alamar ta taho,saita tsaya daga bakin qofar ta noqe kafada tana tura baki gaba,tana tuna azabar da tasha daren jiya a hannunsa "C'mon mana baby doll,nayi alqawari fa bazan sake ba har sai kin yarda" "Promise?" Kai ya jinjina yana murmushi sannan yace "Amma kada ki manta,kema kinyi alqawarin zaki barni nayi komai banda wannan abun dai....." Yadda yayi maganar a narke shi kansa zaka dauka yarone dan shekara tara ko goma,abun ya bata kunya sosai,ta sanya zara zaran fararen yatsunta ta lullube fuskarta tana dariya,sannan ta fara takowa a hankali zuwa gabansa,yayin da shi kuma ya kafeta da ido yana jiran ta qaraso,bugun zuciyarsa na daduwa,yanajin kamar tana ja masa aji ne,kamar bata sauri. Taku biyu ya qara ya cimmata a hanya,ya durqusa gabanta ya lullubeta cikin ingarman qirjinsa dake cike da muscles da gargasa suka yiwa tufa,haka qirar jikinsa yake tun asali,wannan ya qara masa interest na shiga aikin police. Cikin abinda baifi second goma da shiga jikinsa ba dukka jikin nasa ya dauki rawa,ya cusa kansa a wuyanta yana shaqar qamshinta da har yanzu bai sake jin wani qamshi da yake burgeshi kamarsa ba,yadda bugun zuciyarsa ya qaru haka speed na fitar numfashinsa,banda girman alqawarin daya dauka babu abinda zai hanashi karyashi. Tayi lamo a jikinsa ita kanta,tana jin yadda numfashinsa ke kewaye fatarta yana ratsata har cikin qashi,ko qwaqwaran motsi batayi ba,wani yanayi yana sauka a jikinta,har ya haqura don kansa,ya daga kansa a hankali zuwa ga fuskarta yana riqe da fuskartata a tsakanin hannuwansa "Ki rage tsoro don Allah baby.....i love you" murmushi ta saka a kunyace tana son sake boye kanta,sai ya miqe yana cewa "Nooo.....wannan kwalliyar na siyeta har fuskar,zan biya.....don Allah a barni na kalla" cak ya dagata ya azata saman madubin,ya jawo dressing chair ya zauna akai ya buda lotion dinsa ya fara shafawa,yana shafawar yana duban fuskarta hadi da tsokanarta ta hanyar tuna mata da abinda ya faru daren jiya. Kukan shagwaba ta sakar masa tana bubbuga qafafunta "Nidai Allah uncle......Allah.....Allah" dariya ta dinga cinsa,irin abinda bata taba gani ya sake haka yana dariya ba "Shikenan.....wasa nake miki,na daina,amma bakiji bane?,nima fa na kira hajiya har bansan adadi ba,na dauka mutuwa zanyi,yarinyar nan haka kike da......" Ba tare data shirya ba ta saka hannunta ta rufe masa baki idanunta dukka a waje,tana jin kamar qasa ta tsage ta shige,sai kawai ta nemi silmiyowa daga saman madubin,cikin zafin nama ya tareta da cinyoyinta,sai gata zaune sosai a samansu "Yarinya kin kawo kanki" ya fada a tausashe murmushi na kubce masa. °°°°°°°°°Karfe goma na safe suka fito shi da ita,kallo daya zakayi musu kaji sunyi mugun burgeka,kamar hadin baki,shi da itan duka shigar sky blue sukayi,shi shadda ainihin gezner ya saka,ita kuma wani lace ne cotton mara nauyi. Yau din bai nema wani dan rakiya ba,shi da kansa yayi driving nasu daga kadunan zuwa bauchi,duk da jirgi ma yaso subi,amma sai yaji yana da muradin awannin da zasuyi a tare cikin motar waje guda kafin su isa kadunan,don yasan dole kuma ya bawa hafsan lokaci kodon fita hakki,amma for now ya fara tunanin yadda zai dinga raba musu kwana duk lokacin da suka je bauchi,musamman idan zaiyi kwanakin da yafi biyu. *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 85 Yau din tunda suka tashi daga kaduna basu tsaya ba,don bata jima ba bacci ya dauketa,don dama yawanci saboda ita yakan tsaya din,ya samar mata wani abun da zataci,to har suka je inda yakan tsaya din suyi sallah da sauransu tana baccinta,don haka ya wuce abinsa kai tsaye,lokaci lokaci yana waiwayawa ya kalleta,yana monitoring baccin nata. Bata farka ba sai da suka shiga unguwarsu,tadan kalleshi,suka hada ido,yasan me takeson cewa,gidan hajiya takeson zuwa,to amma bayajin zai iya barinta,tunda duka duka kwana hudu zasuyi su juya,suya saki murmushi kawai ya shafi gefan fuskarta "Ba kwana gidan hajiya wannan karon,i need you by my side" shuru tayi kawai,ta langabar da kanta gefe guda ba tare data ce komai ba,duk da ba haka taso ba cikin ranta. Yana gama parking kusa da motar hafsat din data dauki qura mimi na shigowa ita dame daukota daga makaranta,ganin motar babanta ya sanyata tahowa da gudunta tana kiran sunansa,ya dagata ya rungumeta yayi kissing dinta,saita zame daga jikinsa ta koma wajen widad. Ta yima widad din nauyi,amma saita riqe hannunta tana tsokanarta hadi dayi mata waqar 'yar makaranta,tana ta dariya,dadi ya cika yarinyar,ko banza tana samun nishadi kulawa da kuma canjin rayuwa a duk sanda baban nata da antyn nata sukazo. Kamar sama sama take jiyo muryar mimi din tana kiran sunan baban nata,sai taja tsaki ta share,a ranta tana jin haushin yadda yarinyar keda qulafucin ubanta,tana tsoron gaba kadan ma zaiyi wahala idan batafi sonta akan uban ba,saita ci gaba da lissafin kudinta,amma kuma jin shiru bata ji motsin mimin ba,saita ajjiye wayarta da take lissafin a ciki ta miqe tana gyara daurin zaninta,ta sako kai zuwa harabar gidan. Dai dai sanda sale ke cire kayansu a booth din motar,abbas din yana gaya masa kada yayi nisa zai kaishi kasuwa. Cikin wani mugun mutuwar jiki ta sauke hannuwanta data tokare bakin qofa dasu "Kanbun bal bala'in bala'i!" Bakinta ya furta duk da batasan yaushe hakan ta faru ba,daga inda take tsaye tana iya hangen widad wadda ke riqe da hannun mimi,fuskarta kwance da murmushin daya qarawa fuskar tata kyau da kuma kwarjini "Wanne irin girma ne haka cikin wata guda kacal?" Ta tambayi kanta da kanta,har yanzu idanunta na saman fuskar widad din,ko sau daya ma bata waiwayi inda abbas din yake ba. Takawa ta soma yi zuwa inda suke tsaye a hankali tanason sake gasgata abinda idanunta ke nuna mata,saidai duk taku daya idan tayi bugun zuciyarta sai ya qaru,kyau da yadda girma ya fara nunawa a jikin widad din suka soma bata mamaki. Qaramar jakarta abbas ya dora mata saman mota bayan ya kulle motar "Keda mimin banga marabarku ba" yayi maganar yana kafeta da idanu hannayensa duka biyun cikin aljihun rigarsa. Dariya ya bata,tadan juya ido cikin irin nuna mamakin nan,saidai hakan batasan mugun kyan da ya qara mata ba "Uncle kace na girma fa?" Har tsakiyar zuciyarsa ta aike da saqo,bayason yayi saurin bada kai tun yanzun,tunda dai nan ba kaduna bace "Yes.....amma ga jakarki nan,ki dauka sai mu gani" ya fada tsadajjen murmushin nan nasa yana fita daga fuskarsa. "Uncle itama wannan din da nauyi don Allah....." Widad ta fada cikin shagwabar data saba yi masa "Ya salam" ya fada yana miqa hannu hadi da dauke jakar,yayin da hafsat taji tana shirin faduwa,sai takai hannu tana neman abinda zata riqe gudun faduwa,hannunta ya sauka kan kyakkyawar luggage din widad guda daya da tayi saura sale bai dauke ba. Hannunta ta janye,mamaki yana sake kasheta,gata kusa da wajen amma cikinsu ba wanda yama lura da wanzuwarta a wajen,wani tunani yazo mata,tayi qoqarin saita kanta ta hanyar yin gyaran murya kadan,abinda yasa duk suka waiwayo "Sannu da zuwa,saukar yaushe?" Tayi maganar tana tsare gida hadi dayin kicin kicin da fuska,sannan ta miqa hannu tana son karbar jakar widad dake hannunsa a zuwan tasa ce "Yanzu ne,ko kayanma ba'a gama daukewa

Table of Contents

Chapters

155 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});