Chapter 24
Chapter 24
sannan ta magantu "Wai kayan tafiyar kake hadawa?" "sune" ya bata amsa a taqaice "Allah yasa a koma a sa'a,mudin ko weekend ma dinga zuwar maka,kaga bazai shafi karatun mimi ba" ta fada har qasan ranta tana jin ta fada ne kawai don ta wanke kanta,bawai don zata iya wannan jigilar ba "Yayi" ya amsa mata a taqaice kawai,don baison doguwar magana. Shuru ya sake ratsa tsakani,tana ta tauna yadda zata gaya masa zancan motar,don so take kafin bikin qawarta din nan ya sauya mata,taje a hajiyar ta da sabuwar mota,ba wannan qaramar motar da kowa ya sanya da ita ba "Nace ba" ta fada a darare "Uhmmm,kikace me?" "don Allah ba.....abban mimi motata...wallahi matsala take ta bani,sannan ma tayi tsufa da yawa,kada kunya na dinga shigarta bayan mutane sunsan matsayinka" shuru kamar bazai amsata ba,yaci gaba da cin abincinsa,yayin data kasa ta tsare ta kafeshi da idanu tana jiran ta cewarsa,har sai data gaji da jiran amsa ta sake magantuwa "Bakace komai ba abban mimi" plate din hannunsa ya ajjiye,ya waiwayo ya dubeta "Bani da kudi a yanzu" fuska ta dan bata "Abban mimi baka da kudi fa kake fada?,ko allowance dinka ya isa ka canza min babbar mota bama qarama bafa" "Kudina a yanzun bana canza mota bane,ina da abu me muhimmanci da ya fishi" daga haka ya miqe yaci gaba da aikinsa hankali kwance,cikin bacin rai taci gaba da zama wajen,tana ta baqin rai ita kadai,zantukan yayarta take tunawa "Kada fa kiga mijina ya canzamin mota ki dauka kema wannan mijin naki me ra'ayin riqau zai canza miki mota ta sauqi,mafi kyau ki haqura da maganar zancan mota yanzun,nasan halinsa sarai ba canza mikin zaiyi ba" a sannan baki ta tabe tana dan kada qafarta "Kiyi haquri umman walida,amma banjin yadda abbas ke kashemin kudi da yadda yakeji dani kina samun haka wajen baban walida....." "Ke kinga dakata,karki gayamin baqa mana" ta dakatar da ita,duk da cikin wasa suke maganar "Kowa ya san abbas yana jiqaki,amma kuma duk cikinmu babu wadda juya miji ke mata wahala irinki koba haka bane?" Ta fada tana duban sauran sisters dinta dake wajen,dariya suka danyi suna gasgata maganar maman walida din da suke kira da anty balaraba,wannan ya hasalata,ta kuma ci musu alwashin kawo sabuwar mota don ta nuna musu ta isa da mijinta kamar kowacce mace. Har yaci qarfin aikinsa tana zaune a wajen bata sake tofa tata ba,ta tattara fushin duniya ta azama ranta,me yasa koda yaushe abbas din sai ya kunyatata yakejin dadi?,kafin ya kammala aikin ta tattare tabar masa wajen,sai kawai tayi komawarta sashenta,tayi kwanciyarta acan. Shima daya gama komai kwanciyarsa yayi,bai wani tsaya bi ta kanta ba,bayason rainin wayo da kuma rashin hankali,ta kuma fi kowa sani abinda baya tolerating kenan. Washegari haka tayita kumbure kumburenta,sai ya nuna baisan ma abinda takeyi ba,ayi masa laifi kuma a fishi fushi?,yayita hidimarsa da yaransa,yana kuma yin breakfast ya shirya zai fita,mimi ta maqale masa sai ta bishi,ya kaita gidan hajiya,hafsat din nata danqara masa mata harara amma yarinyar batasan tana yi ba,ya shiga dakinsu ya shiryata da kyau cikin sabbin kayanta dake danqare a cupboard ba'a sanya musu,baisan uban me takeyi da kayan ba,yasan dai wani lokaci takan diba ta rabar,duk cikin fariya da alfaharin shi din wuyansa ya isa yankan da yake danqaro musu suttura ya ajjiye. Yana fita ta bishi da tsaki ta kuma miqe abinta saman doguwar kujera tana gunaguni,duk yadda take sonshi yana sanyawa yana fita a ranta gaba daya,bata isa ta sashi yayi abu ba sai abinda yayi niyya ya kuma tsarama kansa,kallo ta kunna abinta tana daga kwance,nawwara da yau suka samu albarkar wanka tun safe tana ta kaikawo tana wasanta qasan carfet,har bacci ya dauketa ta bingire a nan. Har biyu ta buga tana kwance tana kallo bata da niyyar tashi ta kintsa gidan,sai da taji sallama daga qofar falo sannan ta miqe tana sauke qafafunta qasa. "Anty ummee,ni banma dauki murya ba wallahi" "Ina zaki dauka kin tasa tv a gaba" ta fadi tana duqawa ta dauke nawwara daga qasa ta maidata saman kujera sannan ta zauna daga gefanta tana cewa "Yanzun da banzo ba a qasa zaki barta har tayi barcinta ta tashi" baki ta tabe,bacin ranta da ya dan lafa yana motsa mata "Hmmm,a qufule nake anty ummee,ubanta yaja mata,shi ya qunsan takaici" "Ke kam damuwarki da abbas bata qarewa,gashi dai baki rasa komai ba amma ko yaushe cikin complain?" "Na rasa ya zanyi dashi anty ummee,dan bada umarnin nan da mata kewa miji ni bansanshi ba" baki ta tabe tana jingina sosai da kujera "Ke kikaso hafsa" bata motsa daga wajen ba ta zayyanewa anty ummee din komai,itace wadda take bi a dakinsu,uwarsu daya ubansu daya,sai data gama tas sannan ta dubeta "A cikin banza ma ke banza ce wallahi hafsat,ke ko asiri kike fa saikin hada da kissa da kisisina yake ci maka yadda kakeso,ke dan makircin nan na mata ma ace baki iya ba?,ko da yake ko an doraki ma sauka kike" ta qarashe maganar tana yaada kanta gefe cike da takaicin 'yar uwartata. Matsowa tayi sosai kusa da ita "Zanyi wallahi anty ummeee" sai data qare mata kallo sannan ta zauna sosai tace da ita "Ki tattara kayanki ki bishi kaduna kamar yadda yakeso,yaran idan ta kama ko gida ko hannun hajiyarsa basai ki barsu ba?,bama mimi bace ita kadai?,idan kuka tafi can daga ke saishi,ba 'yan uwansa akusa ba 'yan sanya idanu,Allah ne kadai yasan nawa zaki tatsa daga jikinsa,masu aikin damarar nan fa ba qaramin iya soyayya sukayi ba,amma ke gaba daya komai naki a rikice?ki bishi ki kwantar da kai,dadin yadda kika faranta masa ma wallahi baisan sanda zai sauya miki motar ba babu wanda yaji ba wanda ya gani" Fuska ta bata,don ta dauka wata mafitar zata bata ba wannan ba,sai itama anty ummee din ta zuba mata idanu tana dubanta "Ba zakije ba kenan?" Cikin tsuke fuska tace "Ni anty ummee,kaduna fa wa na sani wa ya sanni?" "To ai shikenan saikiyita zama bauchi ki tsanana uwar da zaki tsinana" ta fada tana buga cinya. Shuru tayi na wasu sakanni tana nazari,yayin da anty ummee ke qarewa qawataccen falon nata kallo yadda ta barshi komai a zaune da duwawunsa,babu tsari bare kintsi "Shikenan anty ummee,an gwada aiki da shawarar taki,zanje" "Yadaifi miki" ta bata amsa sannan ta maido dubanta kanta "Yanzu kika tashi a barci ne wai?" Kai ta girgiza tana dubanta "A'ah,me kike gani?" "Bakiji bashi bashin da jikinki yakeyi ba?,sannan wannan uwar bolar da kika barwa falonki ta mece?" Shinshina jikinta ta soma yi,sannan ta bata fuska,don ita bataji komai ba "Ni ba abinda jikina yakeyi,hancinki ne dai,falo kuma wallahi yara ne suka bata su da ubansu kafin su fita,don jiya da daddare fes na shareshi kafin na kwanta,yanzu kuma ina shirin tashi na sake gyarawa kika shigo" "Allah ya sawwaqe" kawai tace da ita,tasan halinta ba yau ba ba jiya ba,koda ta tsaya gaya mata qarancin tsaftarta ma uzurin yara zata yita kawo mata,kamar ita tafi kowa haihuwa a duniya. Suna taba hira tana gyara falon har ta gama,ta shiga kitchen tana tunanin me zata dafa harda abbas din,don ba zata iya girki biyu ba,tayi yanzu tazo tayi musu na dare?,sai kawai ta dora.taliya da miya,suka
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155