Chapter 111
Chapter 111
ta yaba,a yanzun kuma sai ta sake gani ya mata fresh sosai "Yadai...." Ya fada yana dage mata girarsa cikin salon tsokana,murmushi ya subuce mata, kunyarsa ta kamata wanda a 'yan kwanakin nan haka take ji a kansa "Ba komai......"sai ta saka hannu ta bude murfin motar ta fito zuwa harabar gidan. Iska ta shaqa tana duban harabar gidan,daga tafiyarsu last two weeks harabar gidan har ta canza,akwai datti da qura sosai,ita ke sawa a gyara duk sanda sukazo din,bayan ta karba hidimar sassan hafsat data tabbatar ko a yanzun akwai aiki jingim yana jiranta,a yanzun zuwa bauchin ya fara fita mata a ka saboda wannan dan uban aikin bautar da hafsat ke hadata dashi. Waiwayawa tayi zuwa inda yake tsaye,ya fitar musu da kayansu daga booth "Shikenan?,i have done?" Ya fada yana dubanta,narke fuska tayi sannan ta marairaice masa "Uncle taimako please,ka qarasa min da luggage din mana" yadda tayi maganar a mugun shagwabe yayi masifar taba ransa,tun daga wancan ranar data dawo daga gudun hijirar da tayi,ba abinda ya sake bari ya hadasu,ko riqe hannunta,wannan yasa ta sake abinta sukaci gaba da mu'amalarsu,amma ya zuwa yanzun yadda kullum taketa canzawa da koyar abubuwa masu yawa ya sanya yaji ta fara taba zuciyarsa. Kansa ya gyada,ya kama hannun jakar zuwa sassanta tana biye dashi tana masa hira. Sai daya bude mata ya saka.mata jakar yana duban sashen nata da.har abada badai kaga datti ba saidai qura "Can you help me?" "Dame uncle?" "Idan kin gama gyara sassanki please" murmushi ta saki,ko bai qarasa ba tasan me.yake nufi,kuma tana da wannan nufin a wannan karon,saboda magana da hajjaaa tayi mata tun wancan zuwa sun tsaka da waya "Za'a yi in sha Allah uncle" "Thank you" murmushi ya subuce mata,komai.qanqantar abu idan kayi masa sai ya gode maka,tana kallonsa ya juya a hankali ya fice,yabar mata sauran qamshin turarensa data zuqa da kyau ta fesar tana sake sakin murmushi,sannan ta taka zuwa cikin falon nata tana kallon ko ina,tare da tsara yadda zata fara aikin. Sassan hafsat din ya wuce kai tsaye,yana son saur nauyin alqawarin sweet daya daukarma su mimi. Yana dosar sashen yana jin dan tashin hayaniya,sai abun ya daure masa kai,saboda iya saninsa ita din bamai sakewa mutane bace,bata da fuskar da za'a zo gidanta a zauna ana hira haka,suma mutanen kowa ya gane don haka zaiyi wuya kaga tayi baqo. Yana sake dosar sashen yana fahimtar tashin sautin maganganun ba na arziqi bane,yanayinsa yadan canza kadan da fargabar abinda yake faruwa,a haka ya isa qofar falon,ya tura ya shiga da sallama,dai dai lokacin da matar dake tsaye take cewa "Yanzu dai ki fito da shinkafa kawai,tunda ke waye yazo gidanki ma bare ya dauka" ta buda baki zata bata amsa maganar tata ta maqale a maqoshi,tana tsaye tsakar falon,fuskarta har maiqo takeyi,kayan jikinta wari da wari ne na rigar wani lace nata da har ya fara tashi tashi saboda dadewa,sai zanin atamfa,ta yane jikinta da wani tsohon mayafinta milk color "Sannu da zuwa" ta fada muryarta tana dan rawa,itama matar dake tsaye dauke da wata babbar roba blue ta miqa masa tata sannu da zuwan,duka ya hada ya amsa musu,sai ya wuce zuwa dakin hafsat din kai tsaye. *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 73 A dan tsorace ta kalli matar,ganin kuma ita take kalla saita dake,don ita bata yarda ta fadi ba ako menene "Bazan bayar bafa,ladan wahalar aikin da mukayi mata,nima idan tawa haihuwar tazo duka biyun haka takeyimin" dubanta matar ta sakeyi sosai,cikin bacin rai da daga harshe tace "Haka ake taya aiki a kwashe maka abincin suna?,cooler guda saboda dan ke kafadai akayi girkin?,ku haka kukeyi?,don kun taya aiki sai kowa yace anan zaici abincin rana?" "Sai kuma kiyita yi,don Allah ki fita kiban waje,mijina ya dawo" "Au haka kika ce?,to wallahi saikin fito da abincin nan kuwa" nan sa'insa ta barke a tsakaninsu,tun sunayi iyasu har hayaniyarsu ta kaiwa abbas dake tsaye yana nazartar dakin hafsat din,yadda likkafara qazantarta taci gaba,ko ina pampers din nawwara da aka cire an kasa kirashi dust bin,ga zanin gadon dake saman gadonta a iya saninsa sanda ya siyoshi milk color ne mai kyau,amma yanzun ya tasamma zama ash color,naira dub ashirin da biyar ya siyeshi,kyansa da taushinsa ne ma ya burgeshi ya siya din,amma bazai iya tuna wani amfanarsa da yayi ba. Jin hayaniyar tana yawa ya sanya dole ya ajjiye bag din hannunsa dake dauke da sweet din,ya juya zai fita a dakin yaga me yake faruwa,sai cabal qafarsa ya taka wani abu,yaja baya da sauri tsigar jikinsa tana tashi ya duba meye a qasan, kashi ne harda fitsari,yaja tsaki yana girgiza kai,dole ya juya akalarsa zuwa vabdakinta saboda ya wanke qafar tasa. Da qyar ya samu ya hadiye yawu a bandakin,saboda urun bidirin daya gani,zarni tako ina,ga uban kashi cike cikin toilet din ba'ayi flushing ba, zuciyarsa ta fara tashi,yaji nadamae shiga bandakin,saboda qazantar bandaki tana daya daga cikin qazantar dake damunsa,baya qaunarta sam,haka ya wanke qafar ya fito yana qoqarin controlling kansa saboda sosai zuciyarsa take tashi. Dif hafsat din ta dauke wuta sanda suka hada idanu bayan ya fito,baibi ta kanta ba,ya maida dubansa ga matar "Me yake faruwa ne?" "Yallabai,shinkafar suna ce,bayan sun gama aiki ta kwasota da yawa ta taho da ita,mutane nata zuwa babu,shine na biyota nace tadan rage a samu a sallami wasu, shikenan fa......." "Okay,shikenan" ya dakatar da matar daga rattabo masa bayanin da takeyi,shi kadai yasan abinda ya tsaye masa a wuya,bacin ran ya nuna har idanunsa "Ina abincin?" Ya jefa mata tambayar murya a kausashe cike fal da bacin rai,muryarta a cushe tana ayyana irin rashin mutuncin da zata yiwa maqociyar tata tace "Yana kitchen" baice komai ba ya juya akalarsa zuwa kitchen din. Nan ma uban wanke wanke ne jibge a sink dinta,har wani tsami sukeyi,ya laluba da qyar ya gano wata warmer,ya janyo ya budeta saiga qudundunanniyar shinkafar a cuccure irin ta gidan suna tayi fuska abinta,ya daga warmer din ya juyashi,nasa ne da ake zuba masa abinci,wato tana nufin shi ta dibarwa?,shi zaici?,abincin gidan wani?,abincin da wani ya nemo a gidansa?,ba zata iya zama ta girka masa ba kenan saboda tsabar qwarewa a qyuya da kuma iya cin fuska?,ransa ya baci sosai,waye yasan tun yaushe take haka?,waye yasan irin b'arar masa da mutuncin da tayi,haka maqota suke kallonsa kenan tsirara?,ya jawo warmer din ya fito da ita. A tsaye ya samesu matar na riqe da qugu,wani bacin rai ya sake tokareshi,shinkafar da ko masu aiki cikin gidansa sunfi qarfinta yau saboda ita aka shigo masa cikin gidan ake wanna tijarar "Gashi" ya miqa.mata gaba daya,ta karba tana qoqarin juyewa ya daga mata hannu "Jeki kawai" "Flask din naku ba" "Tafi dashi" sai ta saka flask din cikin robar ta juya tana bari wajen. Ganin da gaske tafi mata zatayi da warmer dinta me tsada saita yunqura zatayi mata magana kan ta dakata ta juye ta bata abarta,wani kallo ya watsa mata wanda ya sakata dawowa da baya,ta kuma yi laqwas babu shiri "Ina yarana?" "Naga fa warmer din nan me tsada ne,sai kacw tatafi da ita?,idan kuma taje ta bata fa,kasan gidan suna" ta shigar masa da qorafinta a maimakon amsa masa tambayarsa "Ina yarana nace?"
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155