Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 114

Chapter 114

A Rubuce Take Book 1 Complete Hausa Novel – Widad and the Secret of House 1,321 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ta fada ya zauna,kowa juyashi take a cikin gidan ta ruwan sanyi. "Gaskiya banajin a yanzu ina da buqatar wani malamin tsubbu hajiya,saidai ban sani ba ko nan gaba bana ma fata" jinjina kai kawai hahiya habiba tayi,tana ganin ta gaya mata iya abinda zata gaya mata,sauran dabara ta rage game shiga rijiya "Yanzun nawa ne balance dina a hannunki?" Hafsat din ta dawo dasu kan maganar kudi,abinda tafi qauna kenan. Gaba daya ta dinga jin sassan kamar a kanta yake,sai taji batason qara koda minti biyar a cikinsa,akwai tambayoyin da take da buqatar amsoshinsu,saboda haka sauri sauri ta gama mata duk abinda zatayin ta fito,sai mimi ta maqale zata bita,dama neman kai hafsat din take dasu tace su bita,amma sai nawwara taqi bin nata "Sai kiyita zama ai"ta fadi tana jifan yarinyar da harara,so take tadan samu ta dafa ma abbas wani abun,kafin yazo yahau kanta da qorafi. Ruwa me zafi ta hada tayi wanka,ta yiwa mimi ma,take walwalar yarinyar ta qaru,don har gashin kanta ta wanke mata. Cikin abaya ta shirya kamar yadda take zabinta,zataso shiga kitchen ta dafama yarinyar wani abu,to amma a gajiye take jinta,sai ta fidda snacks din da tayi ta zubo a jaka,ta zuba mata ta hada mata da lemo,sai gashi tana ci hannu baka hannu qwarya,don yafi mata indomie din da ta zame musu 'yar kullum safe rana dare,sai randa Allah ya cishesu suka fita unguwa ko taso ta dafa wani abun. Snacks kuwa irin haka ba samunsa sukeyi ba,muddin ba daddyn nasu bane yazo bauchin ya fita dasu wasu gureren ba. Tana saman kujera a zaune tana sauraren hirar da mimi ke mata,gaba daya kuzarin jikinta babushi,sunayen da hajiya habiba ta kirata dasu su suketa mata yawo akai "Kishiya/'yar aiki",so take yamma ta qarayi ta kira anty deena ko anty madeena ko hajjaa tayi musu tambaya. Tare da sallama ya tura qofar falon nata ya shigo,ya canza shiga zuwa wasu qananun kaya da sukayi masifar karbarsa,suka kuma fidda zatinsa sosai. Idanunsa a kanta sanda mimi ta kamo hannunsa tana cewa "Daddy zo muci,anty ce ta bani,yayi dadi sosai daddy,kace mommy ta dinga yi mana irinsa" biyewa yarinyar yayi,yaje ya tsugunna gaban plate din ya dauka ya gutsura yana yaba dadinsa,wasa wasa sai gashi yana ta ci,ya daga kai ya kalli widad dake zaune gefe tana kallonsu "Ya akayi?,yau babu sakalcinne?" Ya tambayeta da sigar tsokana, murmushi ya kubce mata,itadai batasan me yasa yake mata kallon quruciya sosai da sosai ba,itakam tana gani zuwa yanzun ma ai ta isa mace "Ga wayarki da kika manta" ya.miqa mata wayar yana kallonta,hannu biyu tasa ta karba,tama manta da ita "Adan qara mana snacks din mana baby doll" sunan da ya fara kiranta dashi kenan,tun last week da akayi wani taro na matan police,rose ta kawo me kwalliya har gida tayi mata,ya dinga tsokanarta wai ta zama kamar 'yar tsana,da wayo da wayo ma ya hanata zuwa taron,yace tayi kyau da yawa,bazai barta taje ba,data saka masa kukan shagwabarta sai yace "Wa yace kiyi kyau haka?,bazan iya barinki ba kije,but i promised you zan fita dake anjima kiga gari" da wannan ya fanshi kansa. Koda ta zuba musu snack din ta dawo zama tayi shuru,baice mata komai ba amma yaci gaba da karantar ta cikin qwarewa ta gefan idanu,ya fahimci kamar damuwa ce da ita,sannan tana yawan taba yatsarta "Me ya samu hannun?" Ya tambayeta a tausashe bayan ya miqe yana kallonta,kai ta girgiza da sauri "Ba komai" ta amsa masa tana dunqule hannun nata,baice komai,ya taka a hankali ya isa gabanta,ya kama yatsan yana dubawa,yanka ne,ga wajen yayi ja abinka da farar fata,sai ya daga kai ya kalleta "A ina kikaji wannan?" Shuru ta danyi sannan a hankali tace "Kitchen" "Me ya kaiki kitchen daga dawowarki?" Rasa amsar da zata bashi tayi,saita zabi tayi shuru "But na shigo sau biyu ban sameki ba kina wajen maman mimi" "Eh na dan shiga ne" shuru yayi yana tattara maganganunta guri guda,ya fahimci tana yawan zama a wajen hafsat din,to amma a idanunsa na zahiri baiga wani hali ko wani abu da take mata da zai sanya ya hana ko ya tuhumi zuwanta ba,sannan yafi ta'allaqa zuwan nata can akan su mimi,yasan halinta sarai nason yara,saidai sauyawar yanayin nata a yau yasa yaji bai gamsu da yadda ya ganta ba "Zanje na dawo indai da qarfe kika yanke sai an miki anti tetanus" narai narai tayi da.idanunta jin batun allura,yayi murmushin gefan baki,idan ya biyewa wannan sakalcin nata tabbas yasan ba za'a yi ba. Har yakai qofa ya waiwayo yana kallonta,idanunsa qasa qasa,kasa jurewa kallonsa tayi tadan kauda kallonta gefe "Ko zaki rakani,gidan suraj zanje na dubashi" kai.ta girgiza alamun a'ah,yau din tana jin gajiya sosai a jikinta,bugu da qari ma kuma tana son yin waya. Kai ya mirgina hagu da dama sannan yace "Alright,take care" yayi maganar yana aza mata nauyin kallon nan nasa,saita jinjina masa kai,ya juya ya fita. *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 75 Kamar yadda ya saba ko yaushe bayan sallar asuba yana shigowa ya tabbatar da lafiyarta yauma haka "Gidan hajiya nakeso naje yau" ta fadi masa bayan sun gama gaisawa "Ba damuwa,jiya ban samu zuwa ba,ki shirya na fita dake idan zan fita anjima kadan" saita gyada kai,tana maida idanuwanta ta lumshesu,kwata kwata daga jiya zuwa yau batason zaman gidan. Karfe goma na safe ta gama komai a bangarenta,ta gyarashi ta hada breakfast dan dai dai cikinta,ta kuma shirya cikin atamfa dinkin doguwar riga,tana zaune a falonta tana buga game a wayarta tana jiran fitowar abbas,hatta mayafinta yana gefe. A nutse ya tura qofar falon,yana sanye da shadda butter color da aka tsarama wani lafiyayyen dinki me aji,a kanta idanunsa suka fara sauka,sai yayi tsaye riqe da handle din qofar yana kallonta idanuwansa suna lumshewa,tayi masa kyau har baisan iya yadda zai musalta ba,atamfar ta karbeta ainun,har ya gaza gane doguwar riga da kuma atamfa wanne ne yafi mata kyau,ya dan rufe idonsa yana shafar qirjinsa da hannunsa,yana jin tana sake saka kai sosai cikin zuciyarsa tana samun kyakkyawan mazauni,illa take masa a kowacce rana,kullum yaqi yake da zuciyarsa,yana ganin kamar ya fiya zaqewa da yawa,yanason canzata,yana son sake kawo kusancin da yafi wannan a tsakaninsu,baisan ta yadda komai zai zo ya kuma kasance ba. Batasan da tsaiwarsa ba,saboda hankalinta yayi gaba a game din da takeyi,sai da qamshinsa ya fara kawowa hancinta ziyara,ta daga manyan idanuwanta a hankali,idanuwansu suka sarqe waje guda,siririn murmushi ya subuce mata,ta shagwabe fuska "Ka tsoratani uncle" ta fada tana tura baki gaba,yabi dan qaramin bakinta da kallo,wanda yau yasha jambaki pink,hakan ya qarawa lips dinta color akan ainihin color dinsa. Hannu ya saka ya yafitota yana jin jikinsa na mutuwa,ta miqe a hankali tana dubansa tare da takowa inda yake "Uncleee.......na gama fa na dauko.mayafina?" Kasa amsa mata yayi har ta iso gabansa,yasa hannu a tausashe ya kamo qugunta janyota gabansa,suka zama very close sosai a tsakaninsu. A tare suka lumshe idanu sannan suka bude,suka zubawa juna idanu kamar shiri,kowa da abinda jiki da zuciyarsa ke gaya masa,ya motsa labbansa da salon miskilancin nan nasa "Kinyi kyau baby doll" murmushi ya kubce mata tana kallon manyan idanunsa da suka qara masa kyau a idanunta,kafin tace komai sautin muryar hafsat

Table of Contents

Chapters

155 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});