Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 135

Chapter 135

A Rubuce Take Book 1 Complete Hausa Novel – Widad and the Secret of House 1,326 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

gaya miki yanzu" sosai taji qunci da takurar da zuciyarta ta shiga yana warwarewa,ta goge hawayenta fes tana sakin dariya "Bansan wacce irin godiya zan miki ba 'yaruwa,bansan dame zan saka miki ba" "Ni dubu hamsin ma nake nema,inda zaki bani ita da komai lafiya lau" "Ki bari zamuyi maganar kawai anty ummee" ta katse zancan "Shegiya uwar son abun duniya,duk bala'in son abun duniyar taki wallahi Allah sai naci dake,duk wayon amarya sai an sha manta" anty ummeen ta fada a zuciyarta "To shikenan,sai na jiki" daga haka sukayi sallama,saita miqe ta shiga bandaki ta gyara fuskarta,ta dawo tahau gyaran dakin nata,cikin ranta tsanar widad na sake shigarta,gyaran dakin da a baya saita manta ma ya akeyinsa,don ita ke komai,koda brassiere dinta ta yasar duka zata kwashe ta kuma wanke,amma gashi cikin qanqanin lokaci komai yana shirin canzawa?,ba zatayi sake ba kuwa,ba zata bari haka taci gaba da faruwa ba cikin gidanta,zata bi kowacce hanya don ganin komai ya dawo bisa kan tsari yadda ta shirya. ************washegari wajen sha biyu na rana saiga nujood ita da sauran qannenta,dadi ne sosai ya kama widad,ta rungumeta kana taja baya tana cewa "Hajjaa fa?" A shagwabe,nujood daketa baza hanci ta dubi widad din batace komai ba,har sai da widad din tadan daki kafadarta "Kina jina ina tambayarki don wulaqanci" "Aina kasa magana ne,wani shegen qamshi kikeyi widad,ke bakiga ma yadda kika canza ba gaba daya,kinga wani shegen kyau da fatarki tayi?,wai dama haka auren yake amma naji abba na maganar saina gama secondry na shiga university ki higher institute?" Harara widad ta watsa mata,tana ji a ranta nujood din bata da hankali "Ke kike ganin haka dalla malama" dariya suka saki a tare,sannan suka zauna saman kujerun falon,suka hau surutu har wani bayajin muryar wani. Nan suka wuni a tare,saidai rabi da rabin hankalinta yana kan abbas din,yace mata zaije yakai hajiya dubiya,idan sun wuce ziyarce ziyarce zataji shuru,idan kuma sun gama da wuri he promised her zai dawo gida da wuri. Zuwa azahar ta gama yanke abinda zata dafa masa,taja nujood kitchen din,nujood nata tsokanarta "Uhmmm,kaga matan aure,Allah har mamakin girkinki nake widad,yaushe kika qware haka?" Murmushi tayi "Online classes ne dani sun kusa guda goma,kuma kowanne da irin abinda suke koyawa,dukkansu kuma expert ne,idan suna miki classes kamar a gabanki akeyi" "To ya girkin mutuniyarki?,har yanzu yana nan jiya iyau,hala kina dan sanmata idan kika dafa?" Nujood ta fada tana dariya,saboda tuna girkin da aka tarbesu dashi ranar da suka kawo widad din. Shuru widad din ta danyi tana nazari,sai kuma ta tuna,da sauri ta daki bayan nujood tana dariya kafin ta tsagaita "Oho,da yake ni bacin girkinta nakeyi ba" "Ah dole uncle abbas yaji dake wallahi,irin wannan delicious haka,lallai kwanan nan mommyn mimi za'a shiga uku" ta fada tana feshewa da dariya,tana kunna gas ta kalleta "Kaman yaya?,saboda girkina yafi nata sai uncle yafi ji dani?" Harara nujood ta balla mata "To zauna nan,ke bakisan maza mayun abinci bane?,ki dinga kula daga yau,yadda yakecin abincinki da yadda yakecin nata" nan kuma sai hira ta balle. Nujood tadan girmi widad da kadan,ta kuma fita wayo da shiga cikin jama'a,don takanje gidajen qannen hajjaanta hutu,kuma dukansu yaran mata ne,wasunsu suna da abokan zama,tana ganin yadda suke abubuwa,uwa uba qawayenta na makaranta suma kusan suna da yayye aurarru,kuma suma suna zuwa gidajensu,to idan aka hadu hirarsu bata wuce ta aure da gidan miji,musamman yanzun da suka shiga ss,kowacce tana ganin kamar ta zama senior. Shuru widad tayi tana biye da hirarrakin nujood,mamaki ya dinga kamata, zuciyarta ta dinga kawo.mata abubuwa da yawa game da hafsat,kenan matsayinsu daya da ita duk da qarancin shekarunta?,duk da ta girmeta amma matsayinsu daya kenan?,duk da bata tambayi nujood komai ba,amma ta tsinci abubuwa da yawa cikin hirar da sukayi. Nujood ce ta kama mata aikin,ta shurya lafiyayyar wainar shinkafa da miyar agushi data zuba naman rago wadatacce,don da safiyar abbas din ya aiki yaron office dinsu yayo cefane na duka kayan buqata na gidan,ita dama yawanci idan yasa akayi irin wannan siyayyar kadan yake diba mata,tunda basa wuce kwanaki hudu a bauchin suke komawa,saidai idan wani abunne ya taso. Ta taba ganin ya aika an siyo masa wainar,saita gwada yi masa sau daya,duk da bata tashi ba amma tayi dadi ba laifi,ya kuma ci sosai,data tambaya muneera sai taji ashe tana cikin favorite foods dinsa,yanzun kuma ikon Allah sai bata bata kunya ba,ta tashi tayi kyau sosai,tayi saqa saqa a ciki,ta kuma yi laushi,anty madeena ce ta bata wannan recipe din ta gwada,ta kuma sake tambaya a classes din da takeyi. Bayan ta gama suka gyare gidan fes tare, nujood ta soma hada kan yaran "Yamma tayi yanzun zakuga bala ya iso daukarmu" fuska widad din tadan bata "Haba mana nujood,ku bari zuwa magriba" baki ta kama "Waaa....niiii?, rufan asiri bazan iya.kallon love din da za'a balle yau ba, bakiji wai irin qamshin daya cika gidan na ba?,har waje wallahi,ina ganin kishiyarki yau saita hadiya yawu ya kusa sau saba'in" ta sheqe da dariya,hakanan maganar nujood ta bawa widad dariya "Ki daina sharri wallahi,ba lallai ma ta jiyo qamshin ba kike abunki" ido nujood ta zaro "Lallai yarinyar nan bakisan kishiya da kishi ba" harara widad ta watsa mata "To yaya babba" sai suka saka dariya. Kayan makeup ta hadawa nujood da sauran qannenta,sannan ta bata turare tace ta kaiwa hajjaa,ta rakasu farfajiyar gidan,saida drivern ya iso suka shiga mota sannan ta juya zata koma ciki. Kacibus sukayi da hafsat din,ido ta zubawa widad,itama saita zuba mata nata idon,dauke kai widad din.tayi ta wuce abinta,abun da ya qara daurewa hafsat din kai,tabi da kallo mamaki yana cikata,sai kuma ta ja qwafa cikin ranta tana sakin murmushin mugunta "Yaro man kaza,yaro baisan wuta ba sai ya taka" ta fada a fili,nishadi yana cika Zuciyarta. Ganin duhun magriba ya kawo jiki sai ta lafe a falon tanata duba agogo,sanda taji shigowar motarsa saita narke cikin kujerar tana tsumayin shigowarss,ba jimawa kuwa yayi knocking,ta taso a hankali tana tura baki gaba ta bude masa. Ko gama buduwa qofar batayi ba ya shigo ciki,cike da zaquwa ya sanya hannu ya dagata cak ya rungumeta cikin jikinsa yana sansanar kowanne sashe na jikinta,idanunsa a lumshe kunnuwansa na karbar daqon shagwabarta,ya tattara dukka qarfin halinsa ya taka zuwa ciki da ita,suka zube saman kujera,muryarsa na rawa yace "Me ya faru baby doll?,kukan na meye?" "Uncleeee......" Ta kirashi a narke "Ba kai bane,baka dawo da wuri ba,tun da rana nake jiranka" muryarta har tsakiyar kwanyarsa,tattausan murmushi ya subuce masa,ya cusa kansa cikin gashin kanta bayan ya zame dankwalin "Uhnnn......inda na dawo me zaki bani?" Ba zato yaji bakinta a kunnensa,da zazzaqar muryar ta din nan ta rada masa wani abu da ya sakashi qanqameta cikin jikinsa "Wayyo Alla na" ya fada cikin taushi,saita qyalqyale masa da dariya cikin matsananciyar kunya tana boye fuskarta,hannuwansa duka biyu ya saka ya daga fuskartata yana kallonta cikin tsakiyar idanunta da nashi idanun da suka canza launi "Gani na dawo,ko yanzun baby banyi late ba,don Allah kada ki fasa" ido ta lumshe sosai tana sake sakin murmushi,cikin hirarsu da nujood ta tsinci wannan,ashe haka uncle din nata keso yaji ta furta hakan? "Naje nayi sallah na dawo?" Ya tambayeta a narke shima,kamar qaramin yaro,saita gyada masa kai,ya miqe

Table of Contents

Chapters

155 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});