Chapter 81
Chapter 81
shigowa,sanye da bubu na wani material,ta qulle kanta da dankwalin lace. Zubawa juna idanu sukayi dukka su biyun,abinda yasa hafsat din taji ta tsargu,bata kuma yarda da wayar dake kunnen widad din ba,ita kuma widad din taji wani mugun tsoro ya saukar mata,hafsat din tayi mata wani mugun kwarjini,tana ji anty deena na sake cewa "Hello weedad lafiya ko?" Hadiye wani yawo tayi mai cike da tsoro "Eh anty" muryarta ta sauya ba kamar dazun ba,tabi hannun hafsat da kallo wadda ta miqa hannu kai tsaye tana zare wayar daga kunnenta,ta duba me kiran sannan ta saka a nata kunnen,dai dai lokacin da anty deenan ta sake cewa "Idan da wata matsala ki fada kinji,in sha Allah zan baki shawarwari,basai kin kira ummu kin daga mata hankali ba,ba kuma sai kowa yazo ba" idanu hafsat din ta sauke mata,sai ta dan daga wayar daga kunnenta nesa kadan sannan tace "Bani mana mu gaisa" tamkar a lokacin ta karbi wayar,sannan ta mayar kunnen tana sallama. A sake suka gaisa da anty deena din,don basu manta da yadda ta tarbesu ba sanda suka kawo widad din ba,sun tafi suna yabonta,fargabarsu kuma na shigar widad din gidan kishiya tana raguwa "Da fatan qanwar tamu dai bata da matsala?" "Ah wallahi tana da hankali ga nutsuwa,komai lafiya alhmdlh" cikin jin dadi anty deena tace "To ma sha Allah,muna godiya sosai" "Aiba komai,yiwa kaine ai,bari na baku guri ku qarasabmaganarku" ta fada tana miqawa widad din,jiki a mace ta karba wayar,maimakon ta fita din kamar yadda ta cewa anty deena,sai kawai ta samu waje ta zauna nan saman madubin widad din tana qarewa dakin kallo,kunnuwanta kuma suna sauraren abinda take fadi,shegiya......shuwa ko sadakar yalla,sharrinsu yawa gareshi,yarinya mitsitsiya amma dakinta yana qamshin da nata dakin bai taba yi ba tun zamanin amarci?,take kishi ya kamata,ta maida dubanta ga widad din sanda suke sallama da anty deena. "Wani abu kika gaya musu?" Ta tambayeta tana hade rai tsam kamar tana magana ne da mimi,da sauri ta girgiza kai "A'ah wallahi mommy,muna fara waya ma kika shigo" kai ta jinjina sannan ta sake cewa da ita "Ko.meye yake damunki ni ya.kamata ki fara gayawa kina jina?,tunda yanzun mune muke gida daya dake kinji ko?,dani zaki dinga shawara" kai ta daga,sai hafsat din ta sako qasa tana sake nazartar dakin "Wannan turaren kuma da kike bulbulawa dakin,so kike.aljannu su tare miki a daki su dinga hanaki bacci suna zuwa da daddare suna tsorataki?" Dukka manyan fararen idanuwanta weedad ta fidda waje,iya maganar da hafsat din kadai tayi ta tsoratata matuqa,tsoro sosai ya shigeta,ta fara kada kai "To ki daina sakawa,kibar dakinki a hakama" "Ba sakawa nake ba,haka dakin yake ai" ta furta muryarta tana rawa,a fakaice ta jefa mata harara ta yatsina baki, shegiyar yarinya sai shegen sanabe da kidifiri "To shikenan,ki taso ki wanke uniform din mimi,idan ya bushe kiyi ironing dinsa" tana gama bada umarnin tayi gaba abinta,ai kafin ta kammala fita ma ta biyo bayanta,saboda zancan aljanun yayi mugun bata tsoro,a tsaitsaye ta kashe girkinta dake kitchen,bata ko tsaya dubawa ba tayo sashenta. Sai data gama komai kamar wata 'yar aiki,harda tsarabar sake goge mata falo dasu mimi suka bata,kafin dare ta gaji tubus,tana son komawa amma tana jan jiki,don har yanzu tsoron maganar mommy hafsa dince a ranta,saidai dole ta koma din,tunda a nan din ba wani sakin jiki takeyi ba sosai,kasancewarta mutum mara saurin sabo. Komai da takeyi da takatsantsan take yinsa,ta shiga kitchen ta juyo abincinta ta wuce daki dashi,sai da ta zauna taci mai yawa sosai,don har ita kanta tana mamakin yawansa,amma ba abun mamaki bane,saboda kusan yini tayi da yunwa,data gama din saita tube kayan jikinta ta daura towel ta wuce toilet. A parking lot na gidan ya tsaida motarsa,ya fito hannunsa dauke da ledar da uncle muhsin ya bayar yace a kawowa widad din,don jiya ya dawo daga kano,saqo ne daga mutanen gida,kowa da abinda ya bayar a kawo mata,amma shi abbas din baisan meye da meye a ciki ba,kawai dai ya karba ya taho dashi. Yau din tunda ya fita bai zauna ba,daga gidan hajiya ya dauketa sukayi ziyara sosai bayan sunje gidan makokin,basu dawo ba sai magrib,daga nan kuma yayo gida. Koda ya kashe motar kansa tsaye sassanta ya nufa,hankalinsa yana can,daya fita hajiya na tambayarsa lafiyarta,sai yaga kamar bai kyautawa hajiyan ba,don baisan ya tata tashi ba,wannan dalilin yasa hankalinsa ya dauko da zuwa sashen. A nutse ya buda qofar da sallama abakinsa cikin wannan kwantacciyar muryar tasa mai taushi,falon ba kowa,saidai wannan sassanyan qamshin da ya zaunewa falon daketa faman kadawa,jikinsa ya bashi tana dakinta,don haka kai tsaye ya nufi dakin. Sanda take fitowa daga bandakin lokacin shima ya turo qofar dakin ya shigo,bata ganshi ba saboda ta juya a hankali tana jan qofar toilet din tana rufeta,don ko kadan bata qaunar wani babban motsi,saboda yadda zuciyarta keta rawa,a tsorace take sosai,ta sauke ajiyar zuciya ta fara takowa tsakiyar dakin,sai a sannan idanuwanta suka gano mata shi. Baisan me ya tsaidashi ba daga bakin qofa ya kasa qarasowa ciki,yasan dai tunda ya dora idanuwansa a kanta yaji kamar an tsaidashi a wajen..... widad kuwa baya taja da sauri sanda sukayi ido hudu,jikinta ya fara rawa, idanuwanta suka fara tara hawaye,abu na farko daya zo mata a rai aljanine ya shigo mata part yayi mata suffarsa,fararen kaya ne a jikinsa na wani lallausan yadin filtex,hakanan jakar hannunsa itama farace....an kuma gaya musu a tatsuniya aljanu suna son shigar farare,don haka ta fara hawaye tana fadin "Wayyo ummu na.....don Allah kayi haquri,wallahi na daina,don Allah kada ka yimin komai" haushi dariya da kuma takaici suka qumeshi,yau kuma shine abun tsoron?,lallai abun nata babba ne,quruciyar tata ta gaske ce,rasa abunyi yayi,ta kuma tubure sosai tana masa kuka da magiya,ya lumshe idanu hadi da sauke numfashi ya kuma furzar da iska,ganin yadda yaketa qoqarin yi mata bayani amma ta gaza fahimta. Idanunsa ya sanya cikin nata ya kira sunanta da qarfi,tamkar numfashinta zai fita daga qirjinta ta sandare a tsaye "Kina motsawa anan inda kike zan batar dake,ki tsaya na iso gabanki saina tafi na baki waje" kai ta shiga kadawa,kamar zata saki fitsari a wando,qasan ransa kamar dariya zata qwace masa amma takaici ya hanashi,ya ajjiye ladar hannunsa saman madubi,ya soma takowa idanuwansa a kanta. Yana zuwa gabanta ya hade tazarar dake tsakaninsu,ya buda hannayensa gaba daya ya lullubeta tsam cikin qirjinsa,qamashin shampoo data wanke kanta hadi da shower gel dinta ya nutsa can cikin hancinsa,ya lumshe ido wani numfashi na fusga daga qasan zuciyarsa mai wani irin nauyi "Ya Allah,what's happening?" Ya fada can cikin ransa,jin yadda gaba daya jikinsa ya saki,abun mamaki baiyi abinda ya zata zatayi din ba,a maimakon haka saita tsaya cak a jikin nasa,wani irin nutsuwa taji tana saukar mata, tsoron yana gushewa,ta lullube idanunta sosai,kukan yana dauke mata,ajiyar zuciya tana maye gurbin kukan. Sun jima a haka,kusan mintuna biyar ba wanda ya zame jikinsa daga dan uwansa,dole tasa ya fara neman rabata da jikinsa,saboda yadda dumin jikinta ya fara ratsa nasa jikin,tudun matasan qirjinta ya fara masa barazana,har numfashinsa na qoqarin sauyawa,baiyi mamakin faruwar hakan ba,saboda yasan yana cikin wani irin situation,bako da yaushe yake samun yadda yakeso daga hafsat ba, saboda dan uban qazantarta dake hana masa rawar gaban hantsi koda kuwa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155