Chapter 1
Chapter 1
_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_ *_A RUBUCE TAKE !!!_* (K'addarata) *Huguma* Arewabooks: huguma Free page 01 Babban falo ne,wanda yake malale da marron din carfet mai taushi da kuma saitin kujeru kalar labulen wadanda suka yiwa falon qawanya,a tsare falon yake,ta yadda duban farko kuma kai tsaye ba zaka dauka falon tsohuwa bane,saboda ya wadata da kayan alatu na rayuwa bakin gwargwado. Daga tsakiyar falon,mamallakiyar falon ce zaune saman carfet din,babbar macace wadda gashinta mai tsaho da kuma santsi ya fara bayyanar da furfura saman sumarta,kana iya hangen hakan sakamakon gocewar daurin dankwalin dake kanta,fara ce sol har yellow takeyi,tsufanta bai boye kyan siffa da take dashi ba,wanda da alamu ta sameshi ne tun daga zamanin quruciya kawo yau,kana kallonta kasan ba cikakkiyar bahaushiya bace,hakanan kammanninta bana fulani bane. Daga gabanta kuma wata matar ce da suke diban kamanni da ita,saidai nata shekarun gaba daya ba zasu rufa talatin ba,ita dinma fara ce sol kamar matar dake zaune kusa da ita,wanda kana dubansu zakasan cewa 'ya da uwa ne,yaro ne saman cinyarta tana shayar dashi,dattijuwar mahaifiyar tata kuma tana daga kayan dake gaban nasu "Duk da kayan sunyi kyau humaira,amma gaskiya nafison wadanda sukafi wadan nan tsada,Banason siyawa widad kaya masu sauqin kudi,gwara masu dan tsada da inganci" mai da dubanta halimatu tayi ga kayan tana sake qare musu kallo duk kuwa da cewa itace ta siyosu da hannunta,kayan irinsu ta siyawa yaranta,ta siyama widad din irinsu ne a nata zaton shine qarshen abinda zatayi ta burge ummu,saita maida dubanta ga dattijuwar "Ummu,yanzu duk kyan wadan nan kayan basuyi miki ba?" Kai ta girgiza "Basuyimin ba,kuma tunda nace basuyimin ba ai sai a canzo ko?,tunda dai kudina na saka zan siya,ba kudin wani bane" baki halima ta tabe tana sanya hannunta guda daya tana tattara kayan gefe,zuciyarta cike fal da bacin rai,akwai maganganu da yawa a ranta,amma tasan bata isa ta fadesu ba,yanzu yanzu rai zai iya baci indai akan widad ne "Kin karba min kudin a wajen yaayan?" "Yace sai ya dawo zai bayar na ajiye miki" sake baci ranta yayi,wannan karon ta gaza boyewa "Uhmmm,Allah sarki,to Allah yasa suna da rabon saka ankon" kallonta ummu tayi ba tare da tace mata komai ba,idan da sabo ta saba da irin wadan nan dabi'un,ta rasa me yasa suka gaza fahimtarta,tana ganin son rai ne kawai da son kai irin na dan adam. "Latifa!" Ummu ta waiwaya bayanta inda qofar kitchen dinta yake ta qwala kira,daga ciki aka amsa sannan mamallakiyar sunan ta fito,wankan tarwada ce,mai matsakaicin jiki,a nutse ta qaraso "Gani ummu" "Shiga dakina saman pillow akwai purse dita ki daukomin" amsawa tayi da to sannan ta juya. Saidai bata ko kai ga isa dakin ba,ihu ya karade gidan cikin wata siririyar murya,ihu ne sosai hade da kuka. Da sauri Latifa ta dakata da tafiyar,sannan ta waiwayo tana duban ummu,itama ummun ita take kallo,fuskarta cike da tsoro "Ummu kamar muryar widad fa" kai ta jinjina da sauri "Haka nake shirin fada nima" "Yo wace idan ba ita ba?,kaf gidan nan waye yake wannan tabarar idan ba ita ba?" Dauke dubanta ummu tayi daga kan.haliman zuwa ga ladifa,wadda tuni ta fara nufar qofa "Yawwa,dubamin ita don Allah latifa" "Yanzu kuwa" ta amsata tana ficewa daga falon. Yaronta halima ta kwantar a gefe sannan ta miqe itama tabi bayan latifan tana qunquni cikin ranta. Babbar harabar gida ne wadda ke dauke da interlock shimfide a ko ina,duk da irin girman harabar gidan,jikin kowacce katanga data zagaye gidan dake dauke da sassa sassa guda biyar shukoki ne da.flowers da sukabi bangon gidan suka zame masa ado. Daga bakin daya daga cikin sassan gidan wasu daga cikin ma'aikatan gidan ke tsaye,daga inda kake kana iya hangota,yarinya ce da duka duka ba zata wuce shekara goma zuwa sha daya a duniya ba,farace sol,irin farin nan me cakude da surkin jaa,ma'abociyar yalwatacciyar suma me santsi data sauko har zuwa bayanta ta kuma bazu har saman kafadunta saboda tsallen da take faman yi tana kuma dage maroon din doguwar rigar dake jikinta,manyan idanunta cike da hawaye da suke saukowa saman kumatunta wasu na zirara har gefan dogon hancinta da ya gauraye da majina da hawayen "Babu komai fa widad,na gaya miki na cire shi tun dazu" wata mace dake tsaye a gafe sanye da riga da zani na atamfa ta fada tana qoqarin riqe yarinyar. Dai dai lokacin latifa ta qaraso halima na biye da ita "Meye haka?,me ya faru?" Yayi tambayar tana nufar widad da keta zabga tsalle da kururuwar kuka "Tana tsaka da barci a falona bayan sun gama guje gujensu,kawai ina kitchen ni da marka na jiyo ihunta,da nazo sai tace wai kyankyaso ne ya shige mata riga,dana duba sai naga ashe qwaro ne dan qarami,na daukeshi aka fitar dashi,amma tace kyankyaso ne,nayi duban duniya ban ganshi ba" tsaki halima taja "Iskancin banza da wofi ne da zallar tabara data yi mata yawa,wuce mu tafi kafin na tsitstsinka miki mari" ta fada cikin tsawa "A'ah dakata a duba matan halima" latifa ta fada tana tsugunna wa gaban widad din,ta dage rigar tata da kyau sannan tace "Kalli ki gani,babu komai a jikinki" cikin tsoro dubi fararen qafafuwanta,ganin ba komai din kamar yadda latifa ta fada,saita gyada kanta,saidai kuma har yanzu batabar kukan da take ba. A gaba halima ta sanyata tana ta faman sababi m,wannan ya sake tunzura kukan widad din,har suka isa qofar falon ummu. "lafiya ko?,me akayi mata?" Ummu ta fada idanuwanta da hankalinta gaba daya yana kan widad,tambayar data yi mata sai ya zamana kamar an tunzura ta,cikin sassarfa ta shige falon,tana kuma isa ta fada jikin ummun tana sake sakin kukan. "Me kuwa akayi mata banda tsoron banza da wofi da take dashi,wallahi ummu sakalcin yarinyar nan ya fara yawa,haba" halimatu ta fada cikin huci tana neman saman kujera ta zauna kamar zata fashe "Kin taba gani haka kawai mutum yana kuka ne?,ke me yasa kike haka?"ummu ta fada tana jifanta da harara "Kyankyaso ne ummu yabi ta jikinta,an cireshi amma ta dauka bai fita ba" latifa data shigo ta sake yima ummu bayani tana dosar kitchen. Waiwayawa ummun tayi tana jifar halimatu da harara "To kinji,amma shine zakice kukan banza takeyi?,bayan kinsan widad da tsoro,kinsan kuma halittarta ce a haka?" "Da sakalci wallahi ummu,haba don Allah,ko nabiha da take qanwarta bata wannan abun sai ita shafaffa da mai" "To anji,saiki rufawa mutane baki hakanan" ummun ta fada tana maida hankalinta ga widad dake kwance saman cinyarta tana share hawaye "Sannu kinci abinci?" Kai ta girgiza alamun a'ah "Anty madina ta zuba mana,sai nayi bacci" "Shikenan,tashi maza kije latifa ta zuba miki,idan miyar tayi miki yaji ta zuba miki wadda takeyi yanzu tunda naji kamar ta soyu,ki biya bandaki ki wanke fuskarki,bazan sake bari kije ko ina cikin gidan nan ki kwanta bama bare irin haka ta sake faruwa" miqewa widad tayi a hankali ta soma barin wajen,sai data shiga dakin ummun ta wanke fuskarta kamar yadda tace matan,ta cire rigar jikinta saboda jiqewa da tayi ta saka wata,riga da zani ne,da qyar ta iya daura zanin saboda rashin iyawa da rashin sabo sannan ta wuce kitchen wajen latifa. "Halimatu,banason irin wannan dabi'ar nasha gaya miki,idan baku tausayawa widad ba bai kamata ku sata a gaba ba" "Nifa ba a gaba na
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155