Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 58

Chapter 58

A Rubuce Take Book 1 Complete Hausa Novel – Widad and the Secret of House 1,315 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

zai faru ma ta gwammace basa nan. Sai data mata da gaske tabar kukan ta shigo,momma dake zaune ta bita da harara "Ja'ira,zakiyi bayani ne" kasa hada idanu tayi da kowa,sai ta wuce ciki sum sum sum. Dakinta ta murda ta fada tana sauke ajiyar zuciya mai qarfi,sai a sannan ta nutsu,ta soma bin dakin da kallo. Sosai ya qayatar da ita,an gama shirya mata komai sai qamshin sabinta yakeyi,ta waiwaya ta dubi bandaki inda anty deena tace akwai ruwan zafi,ta shiga tayi wanka,ta kuma zabi kaya masu kyau ta sanya,ta juya zata shige sai aka turo qofar,anty basma da anty ramziyya da anty marwa suka shigo,kowanne riqe da yaronsa,marwa dince kawai mai ciki bata samu rabo da wuri ba. Nan bakin gadon suka zauna sunata tsokanar widad tare da da son jin me ya faru jiyan,kuka ta saki sosai "Ni wallahi ku daina banaso,bayan ummu ta hana,babu kyau,wallahi ba ruwana" haka ta dinga fada tana sharar qwalla,su kuwa ganin abun suke kamar almara,wai yau widad din ummu ce aka aurar?,a wata uwa duniya?,ta tafi tabar ummu duk qaunar dake tsakaninsu?,Allah ne ya kawo anty madina ta korasu,sannan ta kada kan widad zuwa wanka,bayan ta fito kuma ta shiryata da kyau cikin wani lace da yayi masifar karbarta,ya fidda kyau da hasken fatarta,ita kanta ta dade tsaye gaban mdubi yana kallon kanta,tana ta zuba shirmenta na kyan da tayi,anty madina na binta da murmushi gami da goge qwalla a fakaice. Daga bakin gadonta take zaune riqe da waya a hannunta,lokaci lokaci tana saka hannu ta share hawayen fuskarta,duk furuci daya da zatayi da anty ummee tana jin kamar zuciyarta zata tsinke saboda baqinciki bacin rai da zallar kishi kai daci "Har kusan qonewa nayi garin saurin na hada masa tea nakai masa,amma wallahi acan na sameta,namiji dan babansa......alamun dana gani ma sunsha dambene,saboda ko dankwalin kanta gashi nan watse a qasa,don Allah anty ummee mai zaiyi da wannan mitsitsiyar yarinyar,banda tsabar cin fuska?" Tayi maganar tana jin kamar zuciyarta zata fito ta bakinta. "Kinga ki ajjiye wannan a gefe,matuqar zakici gaba daga inda kika tsaya,zaki nuna komai ba komai bane.....hatta kusantar tata ma saikin hanashi gaba daya,meye a cikin ido ne banda ruwa?,ai nasara tana tare da jajircewa" "Wannan nasarar anya kuwa tana tare dani?" "Kin saare a dare daya kenan?" Anty ummeen ta tambayeta tana jinjina zallar gajen haquri irin na hafsa din "Shin ba'a gabanki komai ya dinga gudana tsakanina da amaryar abban sayyid ba?,yanzu tana ina?" "Banqi ta taki ba.....amma akwai nisan tazarar banbanci mai yawa tsakanin abbas dashi.....abbas anty.....yana da ra'ayin riqau kafiya da kuma magana daya,yana da wuyar sha'ani,yana da wuyar canza ra'ayi,idan yace eh.....tofa a haka zata yita tabbata" "Uhmmm,mace fa tafi gaban tunanin dukkan wani mai tunani,saidai idan ba zaki iya ba" "Zan iya" ta fada tana son sake bawa kanta qarfin gwiwa,ji take kamar ta rufe idanu ta kuma bude taga komai ya tarwatse,komai yazo qarshe,ta rufe idanunta kana ta budesu duk kusan lokaci daya sannan tace "Na rasa ta yadda abbas yaga yarinyar nan anty ummee......abbas fa?,mara damuwa da abubuwa masu yawa,wanda wani abun ma sai kinta cewa kalli....ko ka gani" ta jefawa anty ummeen tambayar da taketa damunta tare da yi mata yawo a kai,har yanxu kums bata samu amsarta ba "Namiji yafi gaban haka,kedai ki maida kai ga mission dinki....." "Ina zuwa" ta fada da sauri tana sauke wayar daga kunnenta sanda fa jiyo alamun taku ana nufowa dakin,ta kuma san babu wanda zai shigo din sai shi. Da hanzari ta ajiye wayar,sannan ta fada bandaki ta maida qofar,da tattausar muryarsa yayi sallama ya tura qofar ya shigo,sai ya tsaya daga bakin qofa yana qarewa hargitsatsen dakin kallo,komai baya kan tsarinsa,baisan kuma sai yaushe zata gyara ba. Ajiyar zuciya ta sauke,ta matsa gaban babban madubin dake bandakin wanda ya cika da jirwayen ruwan wankan da ba'a wankewa,ta debi ruwa ta wanke fuskarta,saboda batason ya gane ruwan hawaye ya fita a idanunta,taja zaninta da tayi daurin qirji dashi saman t.shirt dinta ta gyara daurin,sannan ta goge fuskarta da towel ta fito. Suna hada idanu ta cika fuskarta da fara'a,sai ya dan lumshe idanunsa ya kuma budesu lokaci daya yana kallonta,qasan zuciyarsa kuma yana masa sanyi na yanayin da ya ganta a ciki,ba wata damuwa "Yanzu nake shirin fita mu gaisa da baqi,gashi ka tarar dani" ta sake fada tana murmushin da ita kadai tasan ciwon da yake mata. Agogo ya kalla kafin ya amsa mata "Kaman yayi wuri,gwara ki kwanta ki sake hutawaYou are very tired, you need a rest maman nawwara" ya fada yana sauke mata murmushi. Duk da cewa bata kalleshi ba amma tana jin saukar murmushin nasa har tsakiyar zuciyarta,murmushi ne da ita kadai tasan tsadarsa "To ya za'a yi,kamawa takeyi ai,gashi na kasa hada musu breakfast" ta sakeyin maganar tana zaqulo hijabinta cikin hargitsatsun kayan wardrobe dinta wadanda yana daga tsaye yake tayata kallon yadda suke a hautsine,haka suke koda yaushe,idan kayi magana tace su nawwara ne tana bacci suka aikata,ko kuma suna neman teddy dinsu ne "Ba matsala,kinyi qoqari sosai,zan saka a kawo musu breakfast" "Da dai yafi,na gaji da jegon jaka" ta fada qasan ranta tana zura hijabin a jikinta,sannan ta matso tana cewa "Bari naje mu gaisa kada suga rashin kyautawa ta,mun tashi gida daya ban leqasu ba" da kallo ya bita,duk da qoqarin sakewarta amma yana hangen wani.abu can qasan qwayar idanunta,zuciyarsa na alaqanta hakan da kishin da takeji a kansa. Hannayensa ya bude mata,cikin taushin nan nasa "Zaki wuce bamu gaisa ba madam" kallonsa tayi saita kauda kai tana qoqarin kawo murmushi kan fuskarta,tabbas idan tace zata shiga jikinsa a wannan yanayin kuka zata barke dashi,kukan kuma zai zame mata tonon silili ne. "Ina kwana oga?" Ta fada tana ci gaba da tafiya,sai ya maida hannayensa yayi folding nasu a qirjinsa yana kallonta,qaramin murmushi na sauka saman labbansa,irin gaisuwar da yafi qauna daga wajenta kenan,amma dama yasan zaiyi wahala ya samu yadda yakeso din "Alhmdlh madam,a dawo min da yarana mana?" "Zasu dawo dole yau" ta bashi amsa ba tare data juyo ba "Alright" ya amsa mata yana kallota ta cikin madubinta "Bari naje na dawo" ta fada tana jan masa qofar,tana so taje ta saje tantance widad din,yadda ta ganta a jiyan haka take ko idanuwanta ne da kuma sharrin dare?. Idanuwanta nakan dukka wani kayan qawa na falon,da qyar ta iya riqe kanta saboda yadda zuciyarta ke wani irin tsalle,ko ba'a gaya mata ba auren 'yar gata ne daga dukkan alamu,saboda yadda aka shirya gami da qawata sassan nata gaba daya,babu ce kadai babu,jere mai aji da nutsuwa. Ta basu fuska sosai ta gaidasu inna laila dasu momma,har tadan zauna suna dan taba hira,tana ta baza ido taga ta inda widad din zata fito,saiga nujood,kamar inna laila tasan buqatar ta tace da ita "Kira widad,kice tazo ta gaida yayarta" "To" ta amsa tana okomawa ciki da mopper din hannunta data goge inda ruwa ya zuba. "Yaaa latifa" widad din ta fito tana fada,hannunta riqe da dankwalin lace din nata da yaqi dauruwa,anty deena dake wanka kuma tace lallai saita daura. Hankalin hafsa ya fara kaiwa wajen,tana tafe da dankwalin fuskarta a kwabe tamkar shagwababbun 'ya'yan fari,gashinta dake wani irin sheqi da walqiya a daure cikin ribbon jelarsa na reto

Table of Contents

Chapters

155 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});