Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 88

Chapter 88

A Rubuce Take Book 1 Complete Hausa Novel – Widad and the Secret of House 1,302 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ba zata amsa ba,sai kuma tayi qasa da kanta "Zan kwana a nan" ta fada a hankali gabanta yana faduwa,zuciyarta na gaya mata girman laifinta,ta yaya zata hada dakin kwana dashi?. Qaramin murmushi ya saki "Silly girl" ya fada qasa qasa,ga dan banzan tsoro ga shagwaba da sakarci harda na siyarwa,sai ya matsa gefe daya "Bismillah" ya furta a hankali,ta rabeshi sosai ta shige dakin,ya rufe qofar ya sanya key sannan yabi bayanta. Ta jima a zaune har ya gama komai na shirin kwanciya bacci tana binsa da idanu,pillow ya dauka ya jefar a qasa sannan yabi pillow din ya kwanta idanuwansa a rufe yana karanto addu'an bacci,ya gama ya shafe jikinsa,ba tare daya bude idanun ko ya dubeta ba yace "Ki kwanta kiyi kuma addu'a" a takure take sosai saman gadon,duk kuwa da cewa ita daya ce,duk juyin da zatayi idanunta a kansa,har sai data ji saukar numfashinsa a hankali alamun bacci yayi awon gaba dashi,sannu a hankali itama jikinta ya saki,wani bacci me dadi wanda babu fargaba a ciki ya sureta. KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:huguma* Page 57 To tun daga wannan rana kwananta ya dawo dakinsa,saidai tana kammala sallar asuba take komawa dakinta ta shirya shirin makaranta,wani lokaci shike kaita,wani lokacin kuma samuel ko daya daga cikin yaran dake qarqashinsa. Aikin da yakeyi yasa a yanzun zamansa a gida yafi yawa,wannan ya fara haifar da shaquwa a tsakaninsu,duk da baya barin kowa ya rabi inda yake wannan aikin amma yawancin lokuta suna tare,badai hira sukeyi da ita ba,amma zata dauki littafinta ta zauna a wajen,ko ba komai tana jin motsinsa bata da kewa,lokaci bayan lokaci tana barin karatunta tadan zuba idanu tana kallonsa,idan sun hada ido kuma sai ta basar,murmushi kawai yakeyi ko yayi kamar bai gani ba yaci gaba da abinda yakeyi,aikin nasa ke bata sha'awa yake kuma burgeta,tanason masa tambaya amma kuma tana jin nauyi,don har yanzu bata gama sakewa dashi ba. A lokacin yayi qoqari matuqa ya koya mata abubuwa da dama,har ya fara sakar mata,don majority ita ke dafa musu abincin rana,kuma ya ciyu saboda gyaran bashi da wani yawa. Wannan karon ma bai samu zuwa bauchin ba sai bayan sati biyu,tanata hada kaya ta zaci da ita zaya je,sai yace a'ah,tayi zamanta,ta dinga masa kuka amma daga baya dole ta haqura,ya yiwa mai gidan magana matar gidan ta bata 'yar tayin kwana suke kwana tare,friday ya tafi ya dawo sunday da magariba,saita samu kanta cikin murna da farinciki ranar daya dawo din,wanda ita kanta batasan dalili ba,tunda dai ya tafi taji gaba daya bata da sukuni. Zuwansa bauchi a yawancin lokuta bacin raine,yana zuwa ne kawai don ya sauke nauyin da Allah ya dora masa,ya kuma kwatanta adalci,amma baya ga haka baiga wani alfanu da yake samu ba,hafsat din ta yita mita da nunqufurcin bai taho da weedad ba,don ta tara ayyukanta jingim suna jiranta,gidan ya hada mugun datti da qura yadda ya kamata,to koda yaje ma kusan washegarin ranar a aikin kintsa gidan ya qarar dashi,daga qarshe sassan weedad din ya bude ya kwanta yayi baccin gajiya a falonta,ki sashen nata da babu dan adam baiyi wannan qazancewar ba,da yamma ya fice wajen hajiyarsa,wadda ta dinga jajjabin abinda yasa baizo da weedad din ba,a haka dai ya qare weekend din nasa a gantale babu wata kyakkyawar maraba. Haka kawai ta samu kanta da son masa gwaninta,yana fita sallar magariba din a gurguje ta shiga kitchen,ta hada masa simple spaghetti jallop,da murmushi yake kallonta sanda ta dire masa ita,taliya ba cimarsa bace,amma kuma sai yaji ta burgeshi dari bisa dari,ko babu komai tafi hafsat din wadda a qalla nata shekarun sun ninka na weedad din,amma ko irin hakan batasan tayi masa ba,don haka yaji bazai iya watsa mata qasa a ido ba,yaja taliyar ya soma ci,taste dinta sai ya bashi mamaki qwarai,har ya kasa jurewa "Yammata irin wannan abincin fa?,a ina kika koyo shi?" Sunan daya kirata dashi ya bata kunya,saita kifa kanta saman pillow tana dariya,batasan sanda suka fara irin wannan wasan dashi ba "Kaine ka koyamin" kai ya girgiza yana sakin murmushi "Wannan kaman ba aiki na ba" kuma ya fada dinne har zuciyarsa,saboda dandanon ya zarta yadda ya koya mata din. Daya tashi komawa bauchi da ita ya tafi saboda hajiyarsa dake ta tambaya,hakan ya yiwa hafsat dadi,ta sake miqa dukka wasu ayyukan gida ga weedad din,bata samun zama ko hutu saita gama dukka wasu aiki na sassan hafsat din,hakanan hidimar yaran gaba daya ta dawo hannunta,wankansu wanki cire pampers,basu abinci da sauransu,tun tana jin gajiya da wahala har ya soma zame mata jiki ta saba. Wani zuwa da sukayi,ranar asabar da azahar,tana kitchen din hafsat din tana gogeshi bayan ta gama wanke kwanukan da suka cika babban sink din kitchen din,cikin ranta cike fal da mamakin yadda take barin kitchen ya hada wannan uban datti da kayan wanke wanken kamar na gidan biki ko suna,mimi da nawwara na falon data gama gyarawa suna wasa,ta kadasu can don su barta ta gyara nan din a nutse,a dole ta sake qwarewa ta samu kuma experience sosai akan harkar kitchen da kula da yara. Sau biyu anty ummee na sallama sai surutansu mimi,har sai data bude qofar falon ta shigo,tabi falon da kallo zuciyarta cike fal da mamakin yaushe hafsta ta koyo tsafta?,yaran da suka ankare da shigowarta suka watsar da kayan wasan suka taho da gudu suka rungumeta "Ina babarku?" "Tana dakinta,ta kwanta tace kada a tasheta" "Babanku yana nan ne?" Kai ta girgiza "Ya fita a mota" "Muje cikin" ta fada tana kama hannunsu,har yanzu tana mamakin kintsuwar falon,duk da tazo kwana hudu da suka wuce amma ba haka ta samu falon ba. Tana kwance male male saman gadonta tana sana'artata wato chart,harta bude baki data ji an bude qofar zata hau masifa,a zatonta weedad ko yaran ne saita maida maganar dake cikinta tana murmushi ta miqe ta zauna saman gadon ganin anty ummee ce "Daga ina haka ba kira ba sanarwa?" Harara ta balla mata tana samun gefan gadon ta zauna "Kedai baki da hali,don zanzo gidanki saina gaya miki?" Dariya tayi "Allah ya baki haquri ba haka nake nufi ba" bedroom din nata anty ummen ta sake kalla "Nace ba,wai yaushe kika fara tsafta ne?,don nidai banga haka a jikinki ba" tafadi tana kallon jikin hafsat din,wadda ko brassiere babu,sai wata t-shirt data mata yawa da zanin atamfa,kanta kuma tsifa ce rabi da rabi. Fuska ta tsuke tana kallonta,tasan halin anty ummee idan ya motsa in ba cin mutunci tataba mata ba bata jin dadi "Ni dadina dake wlh cin fuska,aidai jikin nawa babu qazanta ko?" "Nima bance akwai ba" ta amsa mata tana boye dariya,sai hafsat din ta gyara zama tana cewa "Yarinyar nan ce sunzo weekend,ai na gayamiki indai sukazo bani da matsala,nima

Table of Contents

Chapters

155 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});