Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 110

Chapter 110

A Rubuce Take Book 1 Complete Hausa Novel – Widad and the Secret of House 1,317 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

cikinsu tayi hakan,duk da kusan abun ma qurarren lokaci yazo,amma duk da haka alhmdlh da aka gano bakin matsalar. A ranar dukka wata kunya anty madeena ta cire ta dinga gayawa widad komai gatso gatso,jikin widad har rawa ya dinga yi saboda mamaki,ta dinga kallon anty madeena tana mamakin haka take? "Eh kalleni da kyau,wannan abun da kika gudowa,kowa yana yi indai mata da miji ne an daura musu aure,harni kaina da kike gani" kunya ta sanyata cusa kanta a cinyoyinta ganin anty madeena din ta danganta abun da kanta,ta kasa daga kanta,sai kuma kwanyarta ta shiga mata research,me yasa mommy hafsa ta dinga jaddada mata kada ta yarda ya taba ko yatsarta yadda ummu take gaya mata sanda tana gida,meye dalili?,tambayar data rasa gano amsarta,sai kawai ta daga kai ta fuskanci anty madeena taga gwara ta tambayeta....... *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks: Huguma* Page 72 "Umman walidi.....amma abinda mommy hafsat take fadamin ba gaskiya bane kenan?,naga itama babba ce kamar ku,amma bata taba gayan abinda kika gayamin yanzu ba" "Me take ce miki?" Anty madeena ta tambayi widad din tana kallonta,cikun fargabar kada ta koya mata dabi'ar banza "Ta gayamin abinda ummu ta jima tana gayamin har nabar gidan nan,tace idan ya kama hannuna Allah zai qona ni,idan na yarda ko kusa dani ya zauna sabon Allah ne,kuma Allah zai iya qonani,kuma koda wasa ya tabanin tana ganewa,har waya take tana tambayata" "Ke kuma idan ta tambayekin sai kike gaya mata?" Anty madina tayi hanzarim tambayar widad tana datsar numfashinta,kai widad din ta gyada,haushi da takaici ya saka anty madina sakin salati,sai yau ta yarda kaf gidan babu wanda yakai widad din rashin wayo,da gaske ne,ada da ake fada tana ganin ba haka bane,kawao miskilanci ne yayi mata yawa,ashe harda rashin wayon "Yaushe duka ta gaya miki hakan akan uncle din" "Kullum saita kirani,ta tambayeni dame dame nayi,dame dame yayimin" wanu malolo ya tsayawa anty madina,sai yanzu ta gane.....hafsat din tayi amfani da rashin wayon widad,da kuma tarbiyya me kyau data samu na girmama na gaba da kai da bin umarninsa ta kitsa mata wannaj baragurbin tunanin,tayi kuma sara akan gaba,suma sun manta basu fayyace mata irin rayuwar da ake nufi da rayuwar aure ba. Zama na dirshan anty madeena tayi ta fara dora mata bayani akan matsayin hafsat din a wajenta,ta fayyace mata wace kishiya fes,sannan ta rufe da cewa "Ba cewa akayi ki rainata ko kiqi yi mata biyayya ba,amma babu ruwanta da ko mene tsakaninki da uncle dinki,matsayinku daya a wajensa ke dashi,ki rufe sirrinki,karki yarda ki sake gaya mata komai dake tsakaninku". Sai kusan sha biyu na dare sannan anty madeena tabar dakin ta wuce dakin mijinta,tabar widad a zaune tanata saqa da warwara,komai ya yiwa kanta girma,tana ta jujjuya maganganun da sukayi da anty madina,tun daga farko har zuwa qarshe, yanzun itama data tafi dakin kawu abinda sukeyi kenan?,abinda ya fado.mata a rai kenan,kunya ta kamata ita kadao cikin dakin,saita cusa kanta a cikin filo tana sake hasashen abubuwan da suka dinga faruwa tsakaninta da abbas din. Bayan sallar asuba anty madeena ta zayyanewa daddynsu walidi yadda sukayi da widad din,tana dariya dariya tace masa "Kaga babu sauran batun zuw wajen ruqiyya,a gayawa yaaya abba yayi haquri" kai ya jinjina yana murmushi "Na yarda widad din muguwar sakaliya ce,ku daman baku fada mata komai ba?" "Wallahi sam ban kawo haka a kaina ba,saboda naga yawanci yaran yanzun ma kafin a gaya musu sunsan komai,amma ita din shekarun nata sunyi qanana da yawa a sanda akayi auren,kuma dai dama widad din gaskiya ko cikin yaran gidan nan tana cikin 'yan ba ruwa na,gatan da qaunar dake tsakaninta da ummu ne kadai yasa ake ganin ta sangarce da yawa,amma tana da dadin zama ainun" "Shikenan,bari gari ya qara haske,zan shiga na yiwa ummu bayani,sai a shaidawa yaayan kafin yakai.ga fitowa,don nasan da abun ya kwana,da wuri zaki ganshi ya shigo" anty madeena dai tana dariya ta fice daga dakin. Tare suka shiga kitchen da anty madeena din,saidai yadda taga widad din tana hada breakfast din cikin qwarewa yasa ta tsaya tana kallonta,sosai abun ya daure mata kai ya kuma bata mamaki,widad dince da iya sarrafa abinci haka? "Me ya faru anty naga kina kallona" murmushi tayi tana sakin habarta "Hmmmm,ba dole ba,irin wannan delicious haka da ake hada mana yau,lallai aure me gyara mutum,su Aafiya suzo suyi kallo,yau widad din da ummu ke hanawa dosar kitchen yau itace da hada breakfast tsaf mai rai da motsi" dariya tayi kawai,ita kanta a yanzun shiga kitchen na daya daga cikin hobbies dinta. Kamar yadda daddynsu walid ya fada kuwa da wuri abban nata ya shigo da shirinsa,yana parlor yana breakfast ummu na ciki tana gyara dakin alhaji da ya tafi umra daddyn walid din ya gayawa abban komai. Kofin hannunsa ya ajjiye yana girgiza kai "Ashsha.....ashsha" sai yaja tsaki "Zataci qaniyarta,wanne irin shirmen banza ne wannan?,dama wannan shirmen da shashancin tazo yi mana?" "Har yanzu quruciya ke damunta yaaya,sai anyi a hankali" abban bai tanka masa ba,illa wayarsa daya ciro yayi kiran uncle muhsin. Widad kuwa batasan me akeyi ba,tana can tare da anty madeena tanta karanta mata abubuwa,da azahar saiga anty deena,kamar tayi kuka haka ta dinga yiwa widad fada "Me yasa kika taho,bance komai ya shige miki duhu ki gayamin ba?" Haduwa sukayi suka dinga wayar mata da kai,anty deena bata bar gidan ba sai bayan sallar magariba. Washegari dai taga an hau mata shirye shirye,sai da azahar anty madeena ke gaya mata gobe zasu maidata kaduna,hawaye fal a idanunta take qorafi "Tunda na tafi fa anty banzo ba ba'a jemin ba,kuma yanzu kwana hudu kawai sai ace na koma?ko alhaji ban gani ba" "Eh ai wannan zuwan da kikayi mu ba irinsa mukeso ba,ki bari kizo cikin dadin rai da yardar mijinki,babu me cewa ki koma sai idan ranki yaso" dole tana ji tana gani taja bakinta tayi shuru,sai cika kawai da take tana batsewa. Washegari samuel ya iso,tana ta kukanta kamar ranar za'a fitar da ita zuwa gidan miji,ita umma batulu,anty halima da anty madeena,anty deena ma taso zuwa,amma kuma a ranar mai gidanta zai dawo daga tafiya. *_BAYAN WATANNI HUDU_* *********A nutse motar ta cusa kai cikin gidan,bata saurara ba har sai data dangane da muhallin da aka tanada saboda ajiyar motoci,ya dai daita tsaiwarta sosai sannan ya kasheta,ya zare key din daga jiki yana fadin "Alhamdulillah". Waiwayawa yayi gefansa,tana kwance,ta lafe sosai cikin kujerar tana baccinta hankali kwance, murmushi ya subuce masa,bai dauka da tace baccin zatayi da gaske shi din zatayi ba,a hankali ya sanya hannu ya zare littafin dake kife saman cikinta wanda ya fadi bayan bacci ya dauketa,yadan duba page din da take ya saka mata alama sannan ya rufe ya dorashi a gaban motar. Idonsa ya sake mayarwa kanta,ya zubawa baby face dinta ido,baccin da alama yayi mata dadi,ya saki murmushi,koda yaushe idan ya kalleta saiya tunata da wata wauta da quruciya data tafka,kome tayi ganinta take dai dai ne,har suyita rikici idan yace ba haka bane. Hannu ya saka yadan bubbuga seat din,a hankali ta bude idanunta,ta zubesu fes cikin nasa,ta kafeshi dasu tana dubansa,he look gorgeous,kaftan din da ya saka sun bala'in amsarsa,ta gani tun daga gida kafin su fito,harma

Table of Contents

Chapters

155 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});