Chapter 19
Chapter 19
data dafa masa,ya dauka yana mata sannu ya fara kurba,sai ta gyara zamanta "Abba na cike foam din nan fa" ba tare da ya dubeta ba yana ci gaba da aikinsa bayan ya tura glass dinsa baya kadan yace "Ma sha Allah,to Allah yasa a fara a sa'a" fuska tadan bata kadan "Amma fa abba akwai matsala" sai a sannan ya waiwayo ya kalleta "Matsala wacce iri?" "Yara abba,bansan ya zanyi dasu ba,babu kowa a gida bare nace driver ya kawosu nan su zauna tare,kuma daga qarfe hudu zamu dinga farawa zuwa shida" ajjiye cup din hannunsa yayi yana dubanta "To yanzu ya za'a yi kenan?" Shuru ta danyi tana juya hannunta,sannan daga bisani tace "Eh to,da wai cewa nayi ko gidan hajiyan gida dubun zansa driver ya dinga ajjiyesu,tunda babu nisa wajen namu daga nan,idan yaso in mun tashi qarfe shidan sai na shiga na daukosu mu zarto gida?kaga kwana biyar kawai an gama" Kai ya jinjina "Qwarai kuwa,hakan ma yayi" "To abba ko zaka gaya mata kada suga yara kawai?" Dan dubanta yayi "Ke hajiya,ai fada zatayi tace don zasu zo sai an gaya mata?,ta wuce duk yadda kike zato,kamar uwa take a wajenmu,ba damuwa idan kinje kyayi mata bayani" "to shikenan ba matsala,godiya nake oga" "Baki da damuwa" ya fada yana murmushi tare daci gaba da aikinsa,ita kuma ta soma tattara kayan abincin da ya gama dasu ta wuce dasu kitchen,sannan ta biya ta dakinsu nujood din ta gaya musu gobe kowa ya dauki kayan gida cikin jakarsa zata saukesu ne gidan hajiyan. *********** Yau din tun safe da ya tashi dukka wayoyinsa na akashe,bashi da niyyar fita sam sam sam kamar yadda ya qudurta tun jiya,zaunawa yaso yayi a gida ya huta,saidai ra'ayin hutun ya kau daga ranshi daga sanda gari ya waye,sai kawai ya hau sanitation na gidan da kanshi,yana yi su mimi na biye dashi yana tayashi da aikin surutu,surutunsu bai dameshi ba,duk da kasancewarsa mutum marason hayaniya,sai surutunsun ya zame masa tamkar abokin hira. Sanda ta tashi ta taddashi yana aikin sai tayi kamar bata ankara da me yakeyi ba,ta qaraso inda yake tsaye saman wata stool yana cire yana,rungume take da hannayenta,tadan rusuna kadan tana fadin "Ina kwana" kansa yadan sauke kan,ya dubeta da manyan idanunsan nan masu kwarjini,a dai dai wannan lokacin kamata yayi ace ta kammala gyaran gidan gaba daya,ta kuma shiryawa iyalinta abun buda baki,shike kwance yana hutun da takeyi amma reshe ya juye da mujiya "Lafiya lau" ya amsa mata yana maida kansa ga aikin da yakeyi,sai taji sam sam ba dadi,tunda ya dawo babu wannan tarairaya da soyayyar tasa mai tsaya mata a zuciya,gaba daya fushin ma data tanada zatayi kamar ma ya fita yin fushin "Dame zan taimaka maka?" Tayi qarfin halin fada,batason ya soma nuna mata halin ko in kula din nan nasa dake mata ciwo,bai iya miskilanci ba ko kadan,idan ya fara sai kinji babu dadi "Inajin yunwa yara sukeji,ki sama musu abinda zasuci" ya amsa mata,sai ta sauke hannunta dake wuyanta,ta wuce kitchen dinta,tunda tuni ya gama da sassansa ya dawo nata. Tea ta hada musu da bread ta soma basu,amma da yake sun gaji da cima daya sai suka watsar suka kama gabansu "Ubanku ya bataku da cima,bazan iya wannan bautar ba,idan na gama kwaci gaba daya" ta fada tana nazarin abinda zaga dafa. Da yake tasan ita din mai laifi ce,duk da batajin tayi laifin har cikin ranta,saita zage ta bata lokaci ta shirya breakfast mai kyau,gasashen kifi tayi da chips,ta dafa masa ruwan tea din da yafiso,sanann ta dama masa kunun gyada still. Sanda ta gama bata gansu falon ba,sha biyu saura,sai ta jere komai a dining sannan ta wuce dakinta. Wanka tayi ta shirya kanta da kyau cikin wata atamfa,ta feshe jikinta da turarukan da tasan yafiso,wadanda takan jima batayi amfani dasu ba,duk da ya siyo su din amma sun zama kamar decoration saman mudubinta,takan ce bata da time na wannan qaqale qaqale din,bata shafawa fuskarta komai ba illa mai,ta taje kanta tana bata fuska saboda yadda yadan dunqule waje guda,ta manta when last data tajeshi,tunda yasa qafa yayi tafiya ta sauke 'yan gyaran da takeyi saboda matsawarsa da kuma qoqarin ganin ta hanashi qorafi a kanta. Daurinta ta kawo gaban goshi saita zari wayarta ta fito. Har yanzu babu kowa a falon,don haka ta zarce sassansa,tana tafe tana duba saqonnin wayarta har ta isa sashen. Ita kanta sai data shaqi iska ta fesar,yadda ya gyara sashen yayi matuqar burgeta,komai yayi fes yana fidda qamshi,tun bai iya wasu aikace aikacen ba har ya zamana ya koya ta dole,yanayin aikinsa karatu uwa uba yanayin matarsa,mutum ne shi sa baya shiri da qazanta sam,duk yadda yakai gason abu ko zama a waje yakan iya haqura idan yanayin baiyi masa ba. A falo ta samu su nawwara,sunyi fes dasu yayi musu wanka ya canza musu kaya,hakan yayi mata dadi sosai,ko banza ya rage mata wani aikin,dama tunanin yadda zata gyarasu takeyi a yadda ta gaji din nan,shi yasa bataso yayi tafiya wasu lokutan,duk da cakudewar aikinsa da yawan ayyuka wasu abubuwan shike dauke mata "Bari na fito da abban muje muci abinci,ku zauna anan" ta fada tana sanya kai zuwa bedroom dinsa. A nutse ta tura qofar ta sanya kanta bakinta dauke da sallama,idanunta suka sauka a kansa,yana tsaye gaban mudubi daure da guntun towel iya qugunsa,faffadan bayansa dukka yana a waje hadi da murdadden dantsensa,ya amaa mata ba tare saya waiwayo ba,jikinsa yake gogewa da wani qaramin towel din,saita maida qofar ta rufe a hankali ta soma takowa zuwa inda yake tsayen,tana jin qaunarsa da kewarsa na motsa mata. Ta baya ta rungume shi,ta kwantar da kanta a tsakiyar bayansa tana sauke ajiyar zuciya "Fushi kake tayi dani abba?" Kansa ya kalla a mudubi,tana bashi mamaki idan tayi wata maganar,kamar batasan komai ba,sai ya girgiza kai kawai yana qoqarin zareta daga jikinsa,don baya son ta bar masa wani feeling da zai dameshi,ya tabata kuma zance ya canza salo "Me kika gani?" "Abun ya motsa" ta fada a ranta,sai taqi bashi damar matsar da itan daga jikinsa ta riqesa gam gam "Nidai don Allah kayi haquri koma meye,duk da kasan kaine kayimin laifi,amma a barshi ya wuce" ta fadi tana qanqamesa gam a jikinta. Rainin hankalinta ya isa,baisan sai yaushe zata fara hankali,ta kuma fara gyaran kurakurenta ba,baisan sai yaushe zata gane haquri yake da ita ba,baisan sai yaushe zafa fahimci yawan uzurin da yake bata ba,sai ya sanya hannunsa ta baya ya jawota zuwa gabansa ya zaunar da ita saman kujerar mudubi yana kallon fuskarta,cikin tattausar muryarsa wadda a boye daga bayanta take cike da bacin ran da yaketa qoqarin binnnewa ya soma mata magana "Saboda nace bazan biya bashin dubu talatin da kika ciyomin ba a matsayin ankon da bansan da zamansa ba bayan sati biyu da suka wuce na miki dinkunan da suka tasamma dubu tamanin shine na zama mai laifi?,wannan shine dalilin da zai sanya ko sau daya ki kasa daga waya ki kirani kiji ya nake bayan kinsan aiki na tafi mai hatsarin gaske?,banda ina da uwa kenan babu wanda ya damu dani?" Yadda ya aza mata idanunsa sai taji sun mata nauyi,cikin jininta ta dinga jin rashin kyautawa na tsarga mata,amma bataso tayi giving up da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155