Chapter 2
Chapter 2
sakata ba ummu,sakalcinta yayi yawa ne,fisabilillahi duk cikin gidan nan wace ake nunawa gatan da kike nuna mata?,ai ba ita kadai bace jika a gidan,sannan ma girma takeyi fa,nan da shekara uku tsaf xa'a iya tayar da batun aurenta,niba tsangwamarta nake ba,so nake naga ta gyara" ido ummu tadan zuba mata na wani lokaci kafin ta janye dubanta daga gareta,ta fuskanci ba zata gane ba "Allah ya kyauta" kawai ta sake cewa,tasa hannu ta janyo purse din da latifa ta ajjiye mata,ta bude ta fidda 'yan dubu dubu ta lissafa ta miqa mata "Gashi,ki lissafa ki cire kudin da zaa qara na kayan da zaki canzo din,ragowar ki siya ma yaran sauran abinda ya rage" hannu biyu tasa ta karba tayi mata godiya,duk daba haka taso ba,ta rasa me yasa ummun take kasa dai daita widad da sauran jikokinta. Sanda ta shiga kitchen zamanta tayi wajen latifa bayan ta zuba mata abinci,tana ci suna hira,sai ka rantse da Allah ba ita ta gama sambada ihun ganin kyankyaso ba,tana ta zubawa latifa surutu ita kuma tana biye da ita,wannan yasa akwai shaquwa sosai tsakaninsu,kusan tana daya daga cikin wadanda basuson kukanta cikin gidan. Sai data cinye tas sannan ta ajema latifa kwanon ta sauka daga kujerar data hau kai ta zauna "Kizo ki wanke hannunki mana kafin ki fita" latifa ta waiwaya tana ma widad magana,wadda tuni ta kusa qofa tana sude hannu "Ina zuwa,zan wanke a wajen anty madina,na manta na baro alawar madarata dazu a can,Allah yasa su faruqu basu shanyemin ba" bata ko sake tsaiwa sauraron latifa ba tayi qofa abunta. Su uku ne yanzun zaune a falon sabanin dazu,anty halimatu,ummu da kuma wani baqon daban. Matashin saurayine fari ne shima kamar yadda na lura da kusan mafi yawa na launin fatar jama'ar gidan farare ne,yana da sassalkan gashi mai santsi gami da duhu,kamar yadda sumar qabilar larabawa ko buzaye suke da ita,sanye yake da shadda dinkin zamani da ya zauna masa sosai a jikinsa,kanshi babu hula,hannunsa riqe da wayarsa yana dannawa,gefe daya kuma suna hira da ummu da anty halimatu. Turus widad tayi tana kallonsa,ta tsareshi da idanu duk da babu wanda ya ankara da fitowarta a cikinsu,dubansa take tana jin wani haushi yana cikata,tsaki taja a hankali don kada su jiyota,sai kuma ta tura baki gaba kamar zata saki kuka. ,juyawa tayi kamar zata koma cikin kitchen din,amma kuma saita sauya shawara,saboda tasan indai ta koma din ummu tasan tana can kuma zata kirata ta fito,abinda bata so din kenan,sai ta dawo tana duban bayan kujerar falon,akwai hanya da zata sadata har qofar falon,don haka ta duqa ta fara tafiya a durqushe ta bayan kujerun,gabanta yanata faduwa,fatanta Allah yasa kada ummu ta ganta. A hankali ummu ta waiwaya zuwa sashen kujerun,motsi take jiyowa,saita sauke idanunta zuwa qasan kujerun,fararen qafafuwan widad ta hanga,dariya taso subuce mata amma saita danne,ba tare da kowa dake wajen ya ankara da abinda ke faruwa ba tace "Widad!" Idanunta na kan qofar falon,ba zaka zaci ta ganta ba,cak widad ta tsaya tana zare manyan idanuwanta waje,gabanta yana faduwa,tana jin kamar ta juya ta koma,amma kuma idan tace zata koma din asirinta zai tonu "Widad,ko bakya jina ne?" Ummu ta sake kiranta tana kallon sashen da alamu suka nuna a nan take a tsaye,saddaqarwa tayi,ta tabbatar ummu ta ganta,don haka sai kawai ta miqe tsaye,fuskarta a daure,ta tattare dan qaramin bakinta ta turoshi gaba,sannan ta fara takowa zuwa inda suke. Dukkansu suka bita da kallo,halimatu ta tabe baki tana dauke kanta,haushin widad din yana sake kamata,ummu kuwa girgiza kai kawai tayi,cikun zuciyarta tana cewa "Allah ya kyauta aikin quruciya". Ta bangarenshi kuwa da kallo ya bita,ya kafeta sosai da idanuwansa,irin kallon da sautari abokansa kan masa dariya,su kuma ce sukam basuga abun kallo ga qwaila kamar widad ba,tun tana tsumman goyonta Allah ya jarabceshi da soyayyarta,har yau kwanan gobe kuma babu abinda ya canza a zuciyarsa game da ita,saidai ita din da baiga alamun koda sakewa dashi tattare da ita ba bare akai ga zancan soyayya,soyayyar da yake da yaqinin bata santa bama,batasan kuma mece ce ita ba,shi yake saka ran ta koya daga gareshi,saidai bata sakewa dashi bare ta bashi wannan damar,tako ina bashi da matsala,yasan zaya sameta za'a bashi ita kamar yadda yake muradi,amma kuma babbar matsalar daga gareta ne. "Bakiga mutane ba ba zaki gaishesu ba?" Ummu ya fada tana hade fuskarta tsam waje daya,duk yadda takai ga gantanta widad da nuna soyayyarta a gareta,amma bata da sassauci wajen tarbiyya. Kamar wadda aka sheqawa mari haka ta waiwaya gareshi "Yaya mahfood ina yini?" Tattausan murmushi ya saki yana kallonta,kanta babu dankwali kamar yadda ya santa,bata qaunar daura dankwali sam "Lafiya lau widadun ummu,ya makaranta?" Bata amsa masa ba,saita juya ga ummu tana bata rai "Gani ummu" ummun na shirin miqewa tsaye tace "Bani nake nemanki ba" saita miqe a abunta tana riqe da hijabinta a hannu "Muje ki gyaramin wardrobe dita kafin ki wuce gida" ummu ta fada tana yin gaba. Miqewa halimatu tayi ta saba yaronta a kafada tabi bayan ummun tana cewa "Har yau ita widad din dana koyawa yadda akeyi bata koya din ba kenan?" "Nidai ba wannan na tambayeki ba,in zakimin kimin,idan kuma fashin baqin naki zakiyi ki barmin kayana,ko intisar tazo sai tayimin" jin ummun ta fara mita saita tsuke bakinta,tabi bayanta kawai din kawai,sai falon ya rage saura su biyu. *_DOGUWAR TAFIYA CE,WADDA KE QUNSHE DA TARIN DARUSSA,TAFIYA CE MAI DAUKE DA WANI IRIN SALON KISHI,GOGAYYA CE DA FAFATAWA TSAKANIN MABANBANTAN MATSAYI BIGIRE GAMI DA MATAKI NA RAYUWA_* *_Ta fita zurfin karatu_* *_Ta fita yawan shekaru_* *_Ta fita wayo dabara da siyasa_* *_GOYON KAKA CE_* *_SAKALTACCIYA_* *_ME QANANUN SHEKARU K'WARAI_* *AKWAI TAZARA MAI TARIN YAWA A TSAKANINSU,KWATANKWACIN SAMA DA QASA* *AMMA DUK DA HAKA TA CITA DA YAQI* *GARIN YAYA?* *_Kin karanta HANGEN DALA?,to ba shakka wannan tafiyar ta fishi zafi darussa da kuma ilimi a cikinta(in sha Allah)_* *_ku taho kawai muje,kuyi jumurin bibiyata,kamar yadda aka saba har kullum,babu gaggawa cikin tafiyata_*😄✋🏽 *KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?* *KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?* Littafi daya---400 Biyu---600 Uku----800 Hudu-----1k Biyar din duka----1200 *ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥 0022419171 Maryam sani Access bank *MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN* 09166221261 🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪 *Ina yan uwa 'yan nijer?* *Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta* +227 90 16 59 91 Littafi daya---450CFA biyu---650CFA uku----850CFA hudu----1050 CFA Biyar----1250CFA *A DADE ANAYI SAI GASKIYA!* *SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!* *Thanks for choosing us*🔥 *_A RUBUCE TAKE!!!_* (Kaddarata) *HUGUMA* Free page 02 *MAAB LUXURY HOME* *_idan kaji gangami akwai labari_* *_SABUWAR DUNIYA CE_* *ALFAHARIN UWAR GIDA* *FARINCIKIN AMARYA* *MAIDA TSOHON GIDA SABO* *DUNIYAR QYALE QYALE* *KAYA NA ALFAHARI DA TAQAMA* *_Ba iya kyawun idanu suka tsaya ba,harma da ingancinsu da kuma qwarkonsu,ka dade kana mora kana kece tsara a tsakanin tsararraku da sauran mutane_* *nasan zaku tambaya ina ne nan?* *MAAB LUXURY HOME* 😊 *Kai daga jin sunan ma babu tambaya* *_duniyar qawata muku gidajenku ku ganku kamar a wata nahiya ko wata duniyar_* *Suna kawo kayan kitchen rankatakaf manya da qananu* *Kayan gado dana parlor* *Kai...suna kawo kowanne nau'in kayan ado na cikin gida* *Karkiyi qasa a gwiwa kuma kada kiyi sake
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155