Chapter 80
Chapter 80
ya fara latse d'iyar mutane,ta miqe sosai ta tsaya tana dubansa "Abban mimi.....ka dinga haquri,kaga dole ayi mata uzuri,akwai quruciya sosai a tare da ita" lumshe idanunsa yayi bisa fuskar hafsan,shi baima gane abinda take fada ba,gaba daya bugun zuciyarsa ne yake neman sauyawa,saiya maida dubansa ga hafsat din dake matsar qwalla "Ga dinner dinki nan,ki taso ki rufe qofar" ya furta yana juyawa cikin mutuwar jiki,sai hafsat ta biyo bayansa tana cewa "Kisa key ki rufe qofan falon kinji,saiki rufe ta bedroom din ma,sai da safe" "To Mommy" ta fada,cikin ranta tana jin tazarar son da hafsat din ke mata abbas din bai kama koda kwatarsa ba,haka tasa muqulli ta rufe qofar sannan ta dawo falon,tsoro ne fal ranta da zuciyarta,tana jin kamar ta bisu,amma kuma haushinsa takeji,don me zai dinga taba mata jikinta,a gurguje ta tattare komai ta wuce bedroom dinta,shima sai data saka key ta rufe da kyau sannan ta canza kayanta zuwa na barci ta haye gado,yau ko.wankan ma bata tsaya yi ba. Ta jima tana juyi ciie da tsoro, duqunqune cikin duvet,wannan gidan yafi na kaduna girma,hakanan gidan kaduna dakunan kusan a kusa da juna suke,tana jin kusancin abbas dake dakinsa a jikinta,sabanin wannan da kowa bangarensa daban,cusa kanta ta sakeyi cikin duvet din,hancinta na zuqo mata qamshin turarensa,wanda ya kama rigar jikinta radam,sai taja tsaki,haushi na cika mata zuciya "Dan iska" ta fada tana murguda baki. **********washegari bata bude qofarta ba har sai dasu mimi sukazo suna buga mata,taji dadin ganinsu,suka dinga wasansu a falonta,ita kuma ta shiga kitchen ta dafa musu jallop din taliya. Da dan gyare gyare cikin girkin,to amma da yake ba wani cimar kirki yaran suke ba sai abincin ya musu dadi sosai,suka zauna sukaci kaman ba gobe,itama cikinsu ta zauna,sunaci suna surutu tana tayasu,sai da suka qoshi sannan mimi tace "Mummy ce ta aikomu,tace kiyi mana wanka,bacci suke wai basu tashi ba" bata ji komai ba,don zamanta da yaran ita dadi yake mata,sannan ita kallon hafsat din take kamar anty deena,don haka ta kunna heater,ta tara ruwa mai dumi sosai,tayi musu wanka kuwa fes,ta shafa musu manta sannan ta dubesu "Ku karbo kaya wajen mommy din a saka muku" da gudu suka fella suka fita,saidai basu jima ba sai gasu sun dawo da kayansu a jikinsu "Mommy tace kizo" jikinta ta kalla,da da hali wanka zatayi kafin ta fita din,don gaba daya bata jin dadin jikin nata,saboda bata samu yin wanka jiya ba,amma kafin ta gama tunanin maganar mimi ta katse mata "Yanzu yanzu wai tace" mayafin doguwar rigarta ta zura tabi bayansu suka fice. Sallamar widad din ta sanyata ninke kudin da take irgawa ta daga bayan pillow dinta ta xubasu tana amsa sallamar,kudin da abbas din ya bata ne ta bawa widad din,anyi rasuwa yana sauri ya fita bai samu leqata ba. Sanda ta karba kudin kamar zuciyarta tayi tsalle ta fito,ita din gotai gotai da ita zai raba musu kudi dai dai da yarinyar da ta haifeta kota kusa haifar ta? "Badai ya fita din ba,meye abun damuwa" zuciyarta ta gaya mata,wannan ya sassauta fushinta,don tayi imanin sisin kwabo ba zata bata ba a cikin kudin. Har qasa ta tsugunna ta gaidata kamar yadda ta saba,saita koma gefe tayi tsaye a darare,ba tare data kalleta ba tace "Kitchen zaki shiga ki gyaramin,idan kin fito saiki fara da falo, bedroom dina kuma idan na gama abinda nakeyi zan miki magana saiki gyarashi,zan gyara dakin yaran da kaina" ta qarashe maganar tana debe kudinta,sannan ta wuce dakinta abinta. Hakanan widad ta zage ta cashi aikin da zata iya cewa bata taba kamarsa ba,ta gyara kitchen tayi wanke wanke,ta dawo falon ta gyarashi tsaf,sannan tayi knocking qofar bedroom din. Tana kwance abinta daga saman gado ta amsa da "Shigo" a darare ta shigo da sallama,a kashingide take tana chart "Mommy na gama" "Gyara abinda ya samu,idan na tashi kya gyara gadon,ko na gyara da kaina" cikin d'ararewa ta fara kwashe tarkacen dake zube a qasan dakin tana hadesu waje guda. KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 52 Har ta gama gyaran dakin kwance saman gadon tana chart "Na gama" ta fada jikinta yana amsawa da wani irin ciwo,saboda wannan shine karo na farko data fara aiki mai yawa haka "Akwai 'yan kayan da zaki daurayemin.....amma,bari nayi kiranki idan na tashi" da to ta amsa,ta juya tana fita a dakin,tana jiyota tana cewa su mimi "Ku bita da Allah kuban waje na huta" da saurinsu kuwa yaran suka biyo bayanta. A falo ta barsu,ta shiga bedroom ta zarce toilet ta hada ruwan zafi tayi wanka,ta hado da alwala,farkon mkhtarin sallar azahar din ya shiga,sai kawai tayi sallarta,tana shafa mai gajiya tana bin jikinta,da qyar ta qarasa,ta shiga kitchen ta hada tea ta hado da bread ta dawo ta zauna tana ci,bata iya shanyewa ba taji ya fita a kanta,sai ta dire cup din ta wuce daki tabi lafiyar gado,bata jima ba kuwa bacci yayi awon gaba da ita,saboda uban gajiyar data tarawa jikinta. Tana tsaka da baccin taji ana dan dukan qafafunta,idanunta a rurrufe saboda nauyin da sukayi mata ta budesu kadan,mimi ce da nawwara "Nawwara ce tayi pupu,mommy tace ki wanke mata" idanu tadan runtse,baccin sam bai isheta ba,amma tana jin ya zame mata dole ta tashi,hakanan ta miqe ta cirema nawwaran pampers ta wanke mata,ta maida mata wandonta,lokacin sallar la'asar ya shiga,don haka ta daura alwala ta bada farali,sanda ta idar cikinta yayi wayam,dole ta shiga kitchen,ta rasa me zata dafa,ta jima a tsaye tana tunani,daga bisani ta raya gwada dafa jallop rice. Nutsuwa tayi sosai ta fara hada jallop din,sai data gama hada komai ta rufe Sannan ta koma ta zauna cikin kitchen din tana taya su mimi wasa,wayarta dake daki ta dauki ringing,sai ta fito tabar kitchen din ta wuce bedroom din,ta dauko wayar dake saman madubi ta duba me kiran. Anty deena ce,saita saki murmushi ta koma bakin gadon ta zauna,daxun da safe da sukayi waya da ummun take cigiyar anty deena di,tace an dauke mata waya ne "Shalelen ummu" baki widad ta tura gaba "Ni wallahi ba haka bane anty deena,duk ku manta dani,kun kawo ni nan kun ajjiyeni" murmushi ta saka "Banda abinki widad,ashe muma ba'a sonmu kenan, kowacce mace 'yar wani gida ce daman ai" "Amma ku ai kuna kusa da gida,kuma ana zuwa,ni kam ba wanda yazo,ummu ma taqi zuwa" "To daga aure weedad sai muhau zirya?,kiyi haquri kinji?" Kai ta gyada kamar tana a gabanta ne,saidai anty deena ta fahimci ta amsa ne tunda taji shuru "Komai lafiya ko?" Ta jefa mata tambayar,sai taji kamar ta tsokano ta,idanunta suka hada qwallar da itama ba zatace ga dalili ba. Ta bude baki tana shirin yin magana aka buda qofar dakin nata,ta daga ido tana duban bakin qofar dakin,hafsat ce ke
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155