Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 21

Chapter 21

A Rubuce Take Book 1 Complete Hausa Novel – Widad and the Secret of House 1,310 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

wajenta,saita dauke dubanta tana tambayar nujood ko lafiya "Mommy ce tace muzo nan mu zauna,qarfe shida zatazo ta daukemu,makaranta ta shiga" "To alhamdulillah" hajiyan ta fada tana jin hankalinta yana kwanciya. "Bari muneera ta zuba muku abinci kuci" "Zanyi alwala banyi sallah ba" widad ta fada,wadda tun dazun take jinta a takure,saboda yau nujood ta matsa musu basuyi sallah a makaranta ba. Dubanta hajiya tayi,sai taji yarinyar ta burgeta,a shekarunta amma tasan kiyaye sallah,duk da tasan idan bata fara haila ba kadan ya rage ta fara,amma ko su muneera da suke 'yammata sosai wani lokaci sai tayi fama da su kan sallar,kiran muneera hajiya tasa nujood tayi,ta kaisu dakin baqi tace suyi sallar sai su fito suci abincin,duka suka miqe suka bita. Ba jimawa suka gama sallar suka fito,muneera ta kawo abincin,hajiya na zaune daga gefansa tana lazuminta,jifa jifa tana kallonsu sanda suke cin abincin. Yaran uncle muhsin din suna da nutsuwa da tarbiyya,amma sai taga nutsuwar widad ta fita daban,ita tafara tsame hannunta daga abincin,ta kuma gyara wajen takai kwanon kitchen,wannan duka aikin ummu ne,duk da bata aikin komai irin ta horas da ita qananun abubuwa irin wadan nan da kyau,kwata kwata widad din ba maison jiki bace,da karambani ma ta iya wasu abubuwan sosai,wanda take koya wajen anty madina,ko idan ta shiga sassansu Aafiya ko ramziyya. Sunata sabgarsu amma tana zaune waje daya,ita gaba daya jinta take a takure,bata son baqon waje,tana da wahalar sabo kuma,wannan yasa ta qara tsumewa waje daya,Allah Allah take momy ta iso su tafi gida. Zaman daya isheta sai ta fara taya muneera ninkin kayan hajiya,sun kusa rabi muneeran ta miqe tayi kwanciyarta,widad din ita ta qarasa muneera ta kwashe takai mata daki. Shida da mintuna hajjaa ta iso a motarta,suna jinta suka fita da sauri tararta,widad ko murmushi tayi tana gyara zamanta,tana jin zama yazo qarshe sai gida. Da sallama ta shigo falon hajiya na mata sannu da zuwa fuskarta da murmushi "Hajiya ai ke za'a yiwa sannu,yau na hadaki da hayaniyar yara" "O'o,o'o,aini deben kewa ma sukayi,yau babu zaman shurun nan" murmushi hajjaa tayi tana maida dubanta kan widad "Kamar kiyi tsuntsuwa ki janyoni ko?,gani na iso sai gida" dariya ta danyi,hajiya ta dubeta "Da alama kam,don tunda sukazo ta kasa sakewa,tana zaune waje daya" "Ai akwaita da baqunta da rashin sabo,duk da dai dama bata da hayaniya sosai,ga oganni nan" dariya hajiya tayi sannan suka fara gaisawa,ta gaya mata aikin da zasuyi na kwana biyar din,tare da alfarmar zama da zasu dinga yi har na kwana hudu a wajenta "Kin jiki hadiyya,banda abinki ba jikokina bane,har sai kin nema alfarma,ai nan dinma gida ne,Allah ya taimaka yayi jagora" "Ameen hajiya,Allah ya qara girma". Hajiyan nata tsaidata suyi sallar magariba amma tace sayi a gida,ta tattara yaran suka wuce gida suna yiwa hajiya sallama tare da cewa sai gobe,don dama su nujood gidan zuwansu ne su,suna kuma jin dadin zuwa gidan sosai saboda kirkin hajiya. ********* Yammaci ne sosai daya kamata ace a lokacin yana cikin gida yana hutawa,tare da shirye shiryen barinsa bauchi zuwa kaduna,saidai bai samu wannan sararin ba,saboda fitinar da hafsat din keson tsirowa dashi,tun batun zuwanta kaduna da yace lallai sai tayi,ko a yanzun ma ya fito gidan ne saboda yadda ta tasashi gaba da nacin roqo harda qwallarta kan ya barta a bauchin,shi baisan wanne irin tunani ke gareta ba,baisan me yake damun kanta ba,kin gwammace kibar mijinki ki zauna da dangi?. Wasu lokuta matsalolinta caza masa kai suke,sai ya samu ya kebe tukunna yake samun kwanyarsa ta huta,don haka ya zabi fitowa daga gidan. Tun asali ba mutum bane shi mayawaci,idan ka ganshi a waje dalilin aiki ko kuma wata lalura ce ta kaishi,sau tari abokan aikinsa na yawan tsokanarsa,sam dabi'unsa kamar ba na dan sanda ba,saidai ya murmusa kawai,ba kasafai yake basu amsa ba. A hankali yake tuqin nasa,kwanyarsa cike fal da tunani,sannu a hankali har ya qaraso junction mai bada hannu ya tsaidasu,motarsa na sahun gaba,yana iya wucewa idan yaso,to amma sanin doka da qa'ida ta sanyashi tsaiwa kamar yadda ya dace ace kowanne mutum ya tsaya din. Hankalisa nakan radio din motar yana son kamo daya daga cikin tashoshin gidajen radio da yakan saurari labaran yamma,baisan me ya faru ba yaji tashin hayaniya,ya daga kansa da sauri yana duban gefansa inda hayaniyar ke tashi. Matashin saurayi ne tsaye kusa da motarsa qirar 206 yana zazzagawa wani tsoho dake saman mashin masifa,yayi tsai yana duban matashin yadda yake haqilo kamar zai kaiwa mutumin duka,mutane har sun fara taruwa ana bashi haquri,ci gaba yayi da nazarin matashin dake dukan saman motarsa yana fadin shifa sai an biya shi,daga gefe daya wani jami'in dan sanda ya fara ratsowa cikin mutanen yana fadin a bashi hanya,abbas din ya bisu da kallo yana son ganin abinda zai faru. Yana daga wajen yake nazartar komai,yadda dan sandan ya shiga maganar suka hadu da matashin suna son bauwa dattijon rashin gaskiya,sai ya sanya hannu ya bude murfin motar ya fito ya nufi wajen. "Assalamu alaikum.....lafiya me yake faruwa?" Yayi tambayar yana duban matashin da yaketa faman daga jijiyar wuya "Wannan tsohon ne ya gogar ma mutane mota da wannan tsohon mashin din nasa,dubi yadda ya gogewa mutane fentinsu" idanu ya lumshe kana ya bude kusan lokaci guda yana duban inda yake fadin an goge masan,duka duka gugar ba wata me girma bace "Kayi haquri kayi masa uzuri kuma,tunda nasan yana sane bazaiyi haka ba" "Wallahi dan nan tun daxu ma naketa bashi haquri,bansani ba,sauri nakeyi ina da uzuri a gida" "Baba ina ganin mutuncinka fa da tuni na zageka,da haqurin ya mutu sadakar nawa ka bayar?,ka biyani kawai" dunqule hannunsa abbas yayi cikin aljihunsa yana qoqarin hadiye bacin ransa "Kayi haquri tunda shima ya baka haquri" "Kaga malam bazan fa haqura ba,idan ma tsaiwa kayi a nan don ka bani haquri gwara kayi gaba abinka" "Is okay,nawa ne kudin gyaran?" Ba kunya ba tsoron Allah ya karkace ya tsuga kudi,kallonsa abbas yayi na tsahon wasu mintuna yana karantar zallar qaryar dake qwayar idanunsa,sai ya saka hannunsa a aljihu ya ciro kudi,ya irga ya miqa masa. Kunya da haushi suka kama matashin,bai taba zaton zai iya biyan kudaden ba shi yasa ya saka da nauyi,cikin borin kunya yace "Ni ba kudi nake buqata,muje a gyaran motata" "Ko ka karba ka tafi,ko kuma kayi asara ba kudin ba gyaran" "Wai kai waye da zakazo kana cikamin baki malam?,bazan karba ba gyaramin mota nakeso ayi" matsowa dan sandan yayi kusa da abbas ba tare daya lura da waye ba a tsaye "Kai meye naka ne a ciki zaka zo kawai ka shiga rigimar kan hanya?,ka qyale mut....." A nutse abbas ya juya suka hada idanu da dan sandan,gabansa yayi mummunan faduwa,yayi baya babu shiri,gumi ya fara yanko masa,abbas din baice komai ba ya maida dubansa ga matashin "Ina me shawartarka ka karba" "Idan kuma naqi fa?" Wani qaramin murmushi na gefan baki abbas ya sake,hankali kwance ya maida kudinsa aljihu gami da fito da wayarsa a madadin kudin,ya danna kira. Baice komai ba illa adreshin titin da suke kai daya bayar ya maida wayar aljihunsa,ya kuma harde hannuwansa yana kallon yadda yake ci gaba da zuba rashin mutunci,jikin dan sanda yana rawa ya matsa kusa dashi "Bawan Allah kayi haquri ka tafi,zaifi

Table of Contents

Chapters

155 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});