Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 133

Chapter 133

A Rubuce Take Book 1 Complete Hausa Novel – Widad and the Secret of House 1,308 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

bata waya bace,ki daure ki cinye komai kiyi masa duk abinda yakeso,zuwa jibi in sha Allah zamu dawo daga bikin 'yar yayar babansu khadija(mijinta),gaata in sha Allah da wurwuri zaki ganni,idan ban samu fita bama zan miki magana saiki shigo mu hadu. Wannan maganar ta tayar da hankalin hafsat din sosai,ganin jibi take tayi mata mugu mugun nisa "Don Allah ki katse bikin nan anty ummee,kizo mu samu mafita,ina cikin mugu yanayi,ji nake zuciyata ba zata iya dauka ba,kamar zata fashe nakejinta" "Indai bakiyi juriyar dana gaya miki ba kikace zakibi son zuciyarki to komai zai lalace miki ne" abinda tace da ita kenan. Tayita kwatanta yadda zata fuskanceshi da fuskar komai ba komai ba amma ta kasa,kwata kwata zuciyarta bata da irin wannan juriyar da jarumtar irin ta anty ummee din,ta gama cusguna ma rayuwarta kuma tayi masa abinda yakeso?,babu abinda idanunta ke hango mata sai sanda suke fitowa daga dakin,yau hannun abbas dinta ne cikin na wata macen?,turakarsa da duk duniya ita kadai tasan kalarta yau sai ga wata mitsitsiyar yarinya ta fito daga ciki?,wa yasan ma me suka aikata suka ajiye mata yarinya a falo?. Duk yadda ta juya ta kasa aiwatar da komai,kawai saita kulle kanta a dakin ita kadai,saqa da warwara ba irin wadda batayi ba akan yadda zata bullowa al'amarin,kota kan yaranta ba ma bata bi,suma yaran dawowar widad yasa basu sake nemanta ba,suna can wajenta,wadda bayan ta gama hada masa tea din ta koma yin wanka ta wuce dasu,ta sake yiwa nawwaran ma wanka,don ita kanta ba cikakkiyar tsafta a jikinta. Zamansa a sassan nasa sai zuciyarsa ta kasa jurewa rashin ganin gilmawarta,ta saba masa da qamshinta,girkinta da a yanzu duk duniya babu girkin da yakejin taste dinsa idan ka dauke na hajiyarsa bayan nata,ya dinga qoqarin danne xuciyarsa,don a qa'ida awannin na hafsat ne,bayason kuma ya fara sabawa jiki da zuciyarsa da aikata wani abu da zai jagoranceshi ga zamowa kasashen namiji mara adalci,dole yayi wanka ya shirya ya biya ta sashenta don a qalla cikin su biyun ya kamata wata a ciki tasan inda zashi kada a nemeshi,hafsat ya dace ya soma fadawa,amma yaci alwashin bazai shiga sashenta ba,zai mata horon da zata sake shiga hankalinta. Tana tsakiyar su mimi din suna assignment,ta dora abinci a kitchen,gown ce a jikinta na chiffon material butter color da zanen green flowers qananu "Zan fita amma bazan dade ba zan dawo" ya furta jikinsa na amsawa,don daga inda yake tsayen yana iya jiyo qamshinta mai dadi,ga kuma qamshin da sashen kansa yakeyi wanda ya cukude da qamshin girkinta. Marairaice fuska tayi tana kallonsa da farare sol din idanuwanta "Uncle.....don Allah kada ka dade" murmushi ya subuce masa, ya jinjina kai yana kallo labbanta "In sha Allah" kusan a tare sukayi masa a dawo lafiya,har ya isa bakin qofa yaji bazai iya wucewa ba,ta gama kashe masa jiki,yana qishirwar lausasan labban nan nata,sai yadan waiwayo ya mata sign din tazo. Miqewa tayi tana sakin murmushi,tana kaiwa bakin qofar ya jawota cikin labule yadda yaran ba zasu iya hangosu ba,baiyi wata wata ba ya mannata da qirjinsa yana sauke ajiyar zuciya,ya dago fuskarta yana dubanta,idanunsu suka sarqe waje daya,sai suka hau yiwa juna kallon kallo,cikin zafin nama ya hade bakinsu waje daya. Da qyar yayi controlling din kansa,ya zareta daga jikinsa yana sake kissing goshinta "Allah yayi miki albarka,take care" ya fada yana ficewa a hankali,sai ta kasa motsawa ta bishi da kallo,yayin da wani lafiyayyen murmushi ya dinga fita daga fuskarsa,yana ji a jikinsa kallonsa take,wannan dalilin ya hanashi waiwayo,don ya bata damar kallon nasa sosai yadda ranta yakeso,ya hangi wasu abubuwa sosai daga zuciyarta,wanda ba lallai ita din ta fahimci shigarsa rayuwarta ba. Sai data daidaita kanta sannan ta koma cikin yaran tana tana labbanta da yatsunta, batasan me yasa duk sanda yayi mata irin wannan abun take tsintar kanta a wani yanayi ba "Kema kin zama yar iska ko?" Ta tambayi kanta da kanta,sai ta bushe da dariya ita kadai,har yaran suna kallonta dukansu,mimi ta tambaya "Mene ne anty" dan zubawa yarinyar ido tayi har yanxu murmushin dake saman fuskar ta bai bace ba,sai ta kama kumatunta "Babu komai mimi,kawai inason daddy uncle...." Ta furta maganar ba tare data shirya ba. Farinciki ya kama yarinyar,ta washe bakinta tana dariya "Shima yace yana sonki" ido ta fidda "Yaushe?" " rannan dinnan" murmushi ta kuma saki,tana juya maganar yarinyar a ranta,saita miqa mata pencil din sukaci gaba da rubutun,zuciyarta wasai cike da tunaninsa,abinda bata taba tsintar kanta a ciki ba akan wani halitta. Dole saboda yunwar cikinta ta fito ta shiga kitchen,ta fara tunanin me ma zata dafa musu?taja tsaki yafi a qirga,ta rasa dame zata fara,saita matsa ta window gaban window din kitchen din nata ta zugeshi saboda iska ta shigo. Tana gama budewar iska me dadi mai hade da wani hadadden qamshin abinci ya cika mata ciki,ta hadiyi yawu da kyau tana tunanin ta inda qamshi kala kala yau yake cika mata gida,tabi wajen da kallo tana qaramin nazari,sai ganinta ya tuqe a sassan widad. Gabanta yadan fadi,kada ya zamana yarinyar ke girkin dake bada irin wannan aroma din,kai ta kada,ko jikinta kunne ne ba zata yadda da haka ba,yarinyar da aka kawo ko ruwan zafi bata iya dafawa ba,yaushe akayi dare har garin zai waye ta iya girki haka?. Tun tana aikin tana basarwa har ta gaza,sai ta ajjiye abinda takeyi ta juyo ta baro sassan nata ta doshi sashen widad din,tana kusantar part din iska da kums hancinta suna tabbatar mata daga can ne qamshin abincin ke fitowa,sai tayi tsaye daga bakin qofa yatsanta a baki,ya akayi haka ta faru?,bata da abinda zatayi,dole haka ta juya ta koma gwiwa a sanyaye,amma kuma ta cika da mamaki tare dason gano yadda akayi haka ta faru. Tana girkin amma gaba daya tunani ya cika mata kanta,ranta a jagule yake,bata qaunar ganin wani ci gaba sauyi ko walwalar rayuwa daga yarinyar gaba daya. Sallama taji da muryar mimi,a mamakance ta waiwayo tana kallon yarinyar "Mommy kizo inji daddy" "Ke.....waye ya koya miki sallama?" Daria ta saki cikin jin dadi "Anty amarya ce,tace duk inda za'a shiga sai anyi sallama,ba kyau shiga guri idan ba'a yi sallama ba" haushi takaici da kuma baqinciki suka cikata,wanne irin sanabe ne haka za'a fito mata dashi akan diyarta,sai taha qwafa "Shi kuma me zanyi masa,har ya gama fushin nasa ne?" Ta fada tana kallon yarinyar kamar itace zata bata amsa,ita dai batace komai ba,sai taja tsaki ta kashe gas din ta fito zuwa dakin baqi da tace yana can. Tunda tayi sallama taga kawunta gabanta yayi mummunar faduwa,saboda tasan cewa lallai ruwa baya tsami banza,ta saci kallon abbas dake zaune daura da kawun nata suna taba hira,wadda duka akan abinda ya shafi security na qasa ne,baiko dubi sashenta ba,haka ta daga kai ta isa ga kawun nata ta zube tana gaidashi kanta a qasa. Shuru tayi ta nutsu sosai kamar da gaske tana sauraron kawun nata sanda yake mata fadan tsafta,iya abinda yafi abbas din yakai qorafinta akai kenan,amma ji take gaba daya ya gama tozartata ya wulaqantata,hausawa sukance wai wanzami bayason jarfa. "Nifa kawu kawai baya ganin qoqarina ne,amma ai inayin duk abinda naga zan iya bakin gwargwado" "Oh.....qarya yake miki kenan?,nace qarya yake miki,to ko ni

Table of Contents

Chapters

155 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});