Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 16

Chapter 16

A Rubuce Take Book 1 Complete Hausa Novel – Widad and the Secret of House 1,299 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kaina" kai ya girgiza "No oga,zamu jiraka,daga nan station zamu koma,babu wani aiki da zamuyi kuma". Baice masa komai ba ya sauka daga motar ya nufi gidan yana takawa cikin tafiya ta tsayayyun maza. Da sallama ya tura qofar ya shiga,yar farfajiyar gidan babu kowa saidai qal take,fes kamar babu wanda ke rayuwa cikin gidan bare ya bata ba,yana hango takalma daga qofar falon,wanda zaka fara taka wata qaramae baranda kafin ka cimma falon,sai yaci gaba da takawa har ya isa baranda yana maimaita sallamar sa,hadi da yunqurin zame takalman qafarsa kafin yakai ga shiga falon "A'ah qaraso da takalmanka abinka" daga can cikin falon aka fadi,sai ya miqe murmushi daga qasan zuciyarsa na kubce masa,har ta hangoshi kenan,duk da shi bai hangota ba,ya yaye labulen yana sanya kansa ciki tare da jaddada sallamarsa. Daga can saman kujera mai cin mutum biyu take a zaune,babbar macace wadda aqalla ta doshi shekara sittin,zaune sanye da atamfa dinkin riga da zani,kanta lullube da kallabi mai santsi irin na asalin tsaffi a qasar hausa.kyakkyawae bafulatanar bauchi,wadda bata qi dibar komai nasu ba,illa hasken fata,bata cika fari sosai ba irin wanda akasan fulani dashi ba,fuskarta na nuna zallar kamala da nutsuwa da kuma mutuntaka irin ta cikakken dan adam. "Wa'alaikumus salam,maraba...yanzu kake tafe?"tayi tambayar tana gyara zamanta cikin kujerun "Eh hajiya" ya amsa mata dai dai sanda take duban 'yar budurwar dake kwance cikin kujera "Tashi ki bashi waje" tun kafin ma hajiyar takai qarshen maganarta ta soma yunqurin tashi tana lalubar dan kwalinta daya fita,cikin sauri ta fara gaidashi "Ina yini uncle" "Lafiya lau" ya amsa mata yana zama cikin wata kujerar ta daban,bayan ya dan ture kayan da suke kai "Shiga kitchen ki samo masa ruwa" "Tom" ta amsa tana ficewa daga falon. Sai a sannan ta tattara hankalinta a kansa,cike da girmamawa ya zamo qasa yana gaidata,ta amsa masa cikin kulawa da kuma qauna "Alhmdlh.....ashe kun dawo" "Shigowata bauchi kenan nace bari na fara zuwa na gaidaki" ya amsa mata yana komawa mazauninsa "Ma sha Allah,Allah yayi jagora" "Yayi hajiya,saidai fatan Allah ya dada yi mana,duk abinda akaje yi din Allah ya dafa mana an samu nasara" murmushi ya wadaci fuskarta,duk sanda zaiyi tafiya irin wannan sai ya shaida mata abinda zaije yi din,duk da cewa kusan komai din da zaiyi ma cikin rayuwarsa ita yake fara sanarwa,ita yake fara shawarta,takan tsaya tuquru da addu'a koda bai nema addu'arta ba,domin kuwa shi din na dabanne a zuciyarta,yana da wata irin tarin biyyaya me wahalar samuwa ga yaran yanzu. "alhamdulillah, alhamdulillah,Allah abun godiya,to Allah yaci gaba da kula mana da rayuwarku" "Ameeen ya hayyu ya qayyumu hajiya" ya amsata yana sake cire hular kansa kamar tana damunsa ne ya ajjiye a gefansa yana duban tarin kayanta dake ajjiye "Ya akayi maisara ya kawo miki kayanki haka babu guga?" Dan duban kayan tayi "To wallahi dai bana ce ba,kamar dai kallon qwallo suka tafi" fuska yadan tsuke "Qwallon me?,idan bazaya iya aikinsa yadda ya kamata ba sai yayi magana" murmushi hajiya ta saki,shikam akan dukkan abinda ya shafeta baya wasa dashi,baya bada uzuri,hakanan baya daga qafa "Yana qoqari ai,kasan su da son qwallo,kuma yau da gobe ma sai Allah" shuru yayi ya sanya hannu yana karbar cup din da muneera take miqo masa mai cike da ruwa. Sai da ya shanye ruwan sannan ya dubi hajiyan "Saura kwana nawa ne bikin gidan kawu hassan?" "Na zaci zaka leqa ma,yana gida kamar bai fita ba yau" "Sai idan na dawo,na yiwa auwal magana zai fidda kudin gudunmawar nan,zai kawo miki sai a bashi" "To to madallah,Allah yayi albarka,ya qara budi" "Ameen ameen" ya amsa mata yana sanya hannunsa a aljihun uniform dinsa ya fiddo kudi ya ajjiye mata yana cewa "Zan dan huta gobe,may be bazan fito ba" "Baka gajiya abbas?" Murmushi kawai ya saki ba tare da yace komai ba,baijin zai gaji da yiwa hajiyan tashi hidima bakin ransa,domin baya da kamarta a fadin duniya "Allah yayi albarka" "Ameen ameeen" "A gaida gida,a gaidamin kishiyoyin nawa" kamar tace kwana biyu sunqi gidan sai kuma ta fasa fadin hakan,ita din mutum ce mai son zaman lafiya,batason rigima sam,saidai a duk sanda ka qureta bata da dadi. A bakin mota ya samu su Samuel sunata hirarrakinsu,kafin ya iso ya bude masa qofar motar ya shiga,sannan suka zagaya suka shiga suma ya tada motar suka bar layin. Duka duka tafiyar minti talatin da 'yan kai motar ta sake sanya signal sannan suka shiga wani madaidaicin titi mai burji,wanda zai sakada da ainihin unguwar da suka nufi shiga. Basuyi tafiya me yawa ba motar ta fara slow,da alama sun cimma inda suka nufa,ba jimawa ta faka qofar wani madaidaicin gida. Daga girman gate din gidan zaka fahimci girman gidan,idan nace girma bawai ina nufin girma na sosai ba,saidai kana gani kasan yalwataccen gini ne daga ciki,hakanan ya qawatu ga idanun me kallo,yana dauke da tsayayyun katanku masu tsaho da qarko,wadanda ke dauke da fenti ruwan madara har jikin gate din,wanda aka yiwa ratsin zaiba(gold) a jiki. Wannan karon kafin su bude masa ya rigasu budewar,ya zuro qafafunsa dake saye cikin baqin boot zuwa waje yana duban gaban gidan sannan ya sanyo gangar jikinsa zuwa waje "Thanks Samuel" yace dasu bayan yadan waiwaya da kyau "You deserve it sir"ya fada yana saluting nashi cikin girmamawa,jinjina kansa kawai yayi yana nan tsaye har suka tada motar suka fara barin gaban gidan,sannan ya qarasa a hankali yasa hannu yana knocking. Daga ciki wata kakkaurar murya ta bayyana ana tambayar waye,bai bada amsa ba har zuwa sanda mai tsaron gidan ya bude qofar,da sauri yaja da baya cikin matuqar girmamawa yana masa sannu da zuwa "Yauwa sule,mun sameku lafiya?" "Lafiya lau oga" "Ma sha Allah" ya furta yana takawa zuwa cikin gidan,hannunsa guda daya saye a aljihun wandon uniform dinsa,daya hannun kuma riqe da hular tasa. A hankali yake takawa zuwa cikin gidan yana nazartar yanayin gidan,daga farfajiyar gidan ko ina fes yake cikin hankali da nutsuwarsa,duk da bashi da tabbacin abinda zai tarar a ciki amma hankalinsa ya dan kwanta kadan,yaci gaba da takawa cikin taku na qaqqarfan namiji wanda horon aikin damara ke yawo cikin jiki da kuma jininsa. Qofar falon ya murza,yayi sa'a ya sameta a bude,sai ya tura yana sanya kai ciki,bakinsa dauke da sallama. Kamar jira akeyi,yara biyun dake wasa a falon saman dan keken wasan yara suka waiwayo zuwa gareshi,babbar me wayon wadda ke tura qanwarta ta saki keken da mugun gudu ta nufeshi "Abba....abba!" Take fada cikin daga murya dake cakude da sautin zallar farinciki,yayin da daya yarinyar keta kiciniyar saukowa daga kan keken itama don ta iso gareshi. Wani qawataccen murmushi ne ya subuce masa,ya duqa a hankali yana jiran isowar yarinyar,tana qarasowa ya dauketa caraf yana sanyata cikin jikinsa,saidai kuma me?..... janyeta yayi da sauri yana duban kayan jikinta sakamakon qarnin da baisan na meye ba daya daki hancinsa,ya sauke idanunsa kan gaban rigar yarinyar,rigar da idan bai manta ba naira dubu shida ya sanya ya siyeta kafin tafiyarsa wannan aikin,kwanaki goma baya da suke wuce kenan. Jirwaye ne na abubuwa kala daban daban a gaban rigar,wanda shi kansa bazai tantance na meye ba,ya dauke idanunsa ya maida kan fuskar yarinyar dake dauke da jirwayen busassun hawaye,kafin yayi magana yaji ana jan

Table of Contents

Chapters

155 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});