Chapter 54
Chapter 54
yadda azababben sonshi yake motsa mata. Da wata irin murya mai laushi yake mata magana,har yanzun bai saki hannunta ba "Idan nace miki banjin dadin wannan karamcin da kika yimin ba nayi qarya,kinyimin abinda babu wadda zaiyimin sai ke din,kin bani nutsuwar cikawa da sauke wannan nauyin,bansan da bakin da zan miki godiya ba hafcy" sunan da ya kirata dashi,wani suna ne mai dadadden tarihi a tsakaninsu,wanda ya jima bai kirata dashi ba,kuma kusan itace silar faruwar hakan. Dukka wadan nan maganganun da yake gaya mata gani take kawai rainin hankali da rainin wayo ne,maganganu masu zafi takeson gaya masa amma saita buge da janye hannunta daga nashi "Tunda dai ka samu yadda kakeso kuma ba shikenan ba?" Ta fada tana duqawa qasa ta soma serving dinsa,tasan idan ba haka tayi zata fallasa kanta ne kawai,saboda ta soma tsarguwa da irin kallon da taga yana binta dashi "Bismillah ga abinci nan"ta fadi tana matsawa gefe "Kiyimin alqawari zaku zauna lafiya ke da ita" "Banyi ba" ta fada a zafafe,saboda yadda takejin ta fara kaiwa maqura,haqurinta ya fara qarewa,ya zuwa sannan takai bango. Ita ta fara janye idanunta daga kallon qurillar da yake mata "Zanyi iya bakin qoqari na,zan mata yadda zanwa qanne na,amma idan ka taimakawa hakan ta hanyar nuna mata mutunci da kimata" ta qarashe zancan hawaye yana sauko mata. Karamin murmushi ya sake,sai ya bude mata hannayensa,with coolness yace "C'mon,is okay". Yadda taso din hakance ta faru,a sassan abbas din ta kwana,ya sake tsumata da muguwar soyayyar nan tasa data sake dasa mata matsanancin kishinsa,ta kuma sake cin buri da alwashin hana kowacce diya mace lasar wannan tsadadda zuma daga gareshi. Tare suka kintsa sukayi alwalar asuba,abinda ya dade bai faru ba,shi ya sanya jallabiyya yadau hula da carbinsa ya wuce masallaci,ita kuma bayan ta idar ta maqale daga gefan gado,zuciyarta nata lasafta mata irin abubuwan da zasu ci gaba da biyowa baya cikin gidan bisa tsarinta da kuma yadda taso,tana jin bacci,tana kuma son komawa,amma tana son ta sake yin wani abun da zai qara wanke ta a wajensa,ya kuma share mata filin da zata aiwatar sa qudurinta hankali kwance. Sanda agogo ya kada shida saita miqe tana fita a sashen zuwa nata,ta kuma fada kitchen tanata qunquni da surutan hanata rawar gaban hantsi,tsahon rayuwar aurenta batajin ta tana shiga kitchen sau uku a irin wannan lokacin,koda abbas kuwa yana da fitar sassafe,saidai ya hadawa kansa komai,kafin ta tashi ma ya fice abinsa. Daga masallaci sai ya wuce sassan widad din don ya gaida baqi,yasan cewa dole akwai manya a cikinsu,duk da rabinsu suna masaukin da gwamnan bauchi da kansa ya bayar yace a sauki baqin. Yadda ya gaidasu cikin girmamawa da dattako ya qara shiga ransu inna laila,dukkan wata haiba da nutsuwa tasa gami da sanin darajar dan adam ta bayyana,widad ita da nujood da anty madeena suka kwana a dakinta,anty madeena tunda tayi sallah ta fito nan wajensu ta barsu a dakin,don haka cikin hikima inna laila tasa aka taso nujood a dakin,saura widad kawai. Har ya miqe zai juya inna laila tace dashi "Tana ciki ai" sam bai kawota cikin ransa ba,to amma ya kamata ya dubata,tunda yanzun dole tana qarqashin kulawarsa,bugu da qari kosa yaushe akwai wani sashe na zuciyarsa dake sake tunasar dashi muryar hajiya cikin sautin dake gaya masa amana ce ita a wajenka,ka riqeta amana. Da qanqanuwar sallama a bakinsa ya tura qofar ya shiga,qamshin sabbin furniture da turarukan wutan da aka ajjiye cikin dakin saman mirror suka cakuda suka bada wani kalar qamshi suka daki hancinsa. Sake maimaita sallamar yayi amma ba'a amsa masa ba,ya dan sake takawa zuwa ciki kadan,sai ya hangota daga gefan gadon,kwance saman lallausar sabuwar dadduma,ta qudunduna sosai cikin hijabinta jakar daddumar,da alama dasu tayi sallah,tana kuma idarwa baccin ya dauketa a wajen. Takawa yaci gaba da yi har ya isa gabanta,yadda ta cure sosai kamar maijin sanyi ko jariri a cikin mamarsa yasa ya fahimci kamar sanyi takeji,saiya waiwaya inda ac din dakin yake,sun qureta ne da yawa,ta kuma hadu da sanyin asuba,ya laluba remote saman bedside drawer ya kasheta,sannan ya maida dubansa ga fuskarta da rabinta ne kawai ya bayyana. Idanun nasa ya dauke,yaja da baya ya nufi qofar fita,dai dai lokacin da hancinta ya cika sa qamshin wani tutare na daban,saita buda idanunta da sauri,take ta hangi bayansa sanda yake ficewa a dakin,saita miqe da sauri ta zauna tana jingina bayanta da gado tana kuma raba ido "Me yasa ya shigo?,haka kawai tana baccinta" saita kalli jikinta "Allah ma dai yaso hijabine a jikina" ta fada tana sake jan hijabin tana rufe qafafuwanta,kamar ce mata akayi zai dawo. *AREWABOOKS:HUGUMA* KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 35 Tun gari bai kammala wayewa ba suka tashi da aikin qarasa kintsa gidan,saboda suna son wucewa a ranar,saidai hakan bata samu ba,don abbas ya sake dakatar dasu yace su sake kwana,wannan ya basu dama suka buqaci mota,ya kira samuel daga office yazo ya kawo musu tare da yi musu jagora,inna laila,batulu anty deena anty halima da hajjaa suka sada widad da gidan hajiyan abbas. Fadin irin dadin da hajiyan taji bata baki ne,bata zaci zuwanta ba sam,saboda taga ba kasafai ake hakan ba,tunda ba unguwa daya suke ba,yadda ta dinga nan nan dasu zai baka mamaki,farincikinta ya gaza boyuwa,ta kirayi gwaggo fanteka donta tayata karbarsu. Duk abinda akeyi fantakea din da kallo take binsu,saidai ta saci ido ta tabe baki,idanuwanta qir akan fuskar widad "Ashe.....ba banza ba,ashe sadakar yalla ya kwaso,kai jama'a,kashin hafsatu ya bushe,ba abinda ba zata gani ba,idan Allah ya tsare ma bata fiddata gidan ba" wannan ta dinga maimaitawa a ranta tana binsu da kallo,musamman da taga kowanne a cikinsu daga yanayin fata zuwa halittarsu da sumar kansu batayi kama sam da hausa fulani ba. Duk da batasan da zuwansu ba haka ta cikasu da abinci kala kala,kasancewarta mace mai karamci,baka rasata da abubuwa irin wadan nan. Tun basu bar gidan ba ta kira abbas ta shaida masa,shima yaji dadin yadda suka karrama masa mahaifiya,yasan zasu fita,tunda muhsin ya gaya masa,don hajjaa tace ya gaya masa,amma baisan can zasu kaita ba. Sai yamma lis suka dawo gidan,a sannan hafsa tana daga jikin window dinta tanata leqe,har yanzu batakai ga ganin fuskar widad ba,sai giftawarsu data gani kawai. Dan kwalinta ta cire ta jefar,ta koma ta zauna jabar saman kujera tana fidda wani hucin azababben kishi dake cinta,tunda zancan nan ya bullo har kawo yau bata sukuni ko qanqani,gaba daya a birkice take jinta,hatta da yaran tace kada a dawo dasu sai gobe ko jibi,sai kawai tasa hannunta a fuska ta fashe da kuka mai cin rai,tana tsananin son abbas tana kuma kishinsa,batasan yadda zata jurewa wannan al'amarin ba,abu mafi dagula mata hankali shine sadakar yalla da akace ya auro,tana sane da yadda
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155