Chapter 104
Chapter 104
sannan suka wuce gidan,ba wani zumudi ko kadan a tattare dashi,abu daya ke sanyawa yaji dokin zuwa gidan,yaransa da yayi kewarsu. *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 68 A farfajiyar gidan ya cimma yaran suna wasa,ya tsugunna suka dafeshi gaba daya ya miqe dasu,yau din ba yabo ba fallasa,basuyi datti ba amma kuma bai samesu fes yadda yakeso ba,dukkansu kansu a tsefe yake a daure da band,yana rungume dasu a jikinsa suka sanya kai cikin falon dake sassan hafsat din. Shima yau dai falon babu laifi,saboda babu dattin,amma bawai kar kar yake ba,yaji dadin hakan har qasan ransa,ya kuma tsinci kansa da fatan samuwar canji daha gareta da kuma dorewar dabi'unta. Bata parlor din,don haka ya zarce bedroom din nata kanshi tsaye,har yanzu yaran suna kafadarsa suna masa surutu,ya tura qofar dakin,dai dai sanda ta waiwayo suka hada ido,tana tsaye gaban mudubi,saita dauke kanta tana amsa sallamar,jikinta sanye da wata koriyar atamfa riga da fallen zani "Sannu da zuwa" ta fada cikin careless,kamar wanda yaje qofar gida ya dawo,bai amsa mata ba sai daya sauke yaran a qasa,ya saka hannu a aljihunsa ya fidda chocolate ya miqa musu "Ku jiremin falo maza mimin daddy" da gudu suka falla sukayi falon kuwa,sai ya maida dubansa gareta,har kullum idanuwansa ba zasu gaji da gayawa zuciya da kwanyarsa yadda yakeson ya ganta ba haka ya ganta ba,kamar yanzun,kai zaka ce matar qauye ce,koriyar atamfar da aka tashi aka yima wani sungul dinki,ba wani abun jan hankali a jikinsa nare style din zamani,daurin kanta kamar na matar qauye,amma duk da haka baiji ya wani tunzura ba,ko tsananin buqatar da yake ciki ce ta kauda duk wani aibu daga idanuwansa?,idanma hakanne harda tasiri 'yar tsaftar daya isketa a ciki. Duk duniya ta shaida auren soyayya sukayi da hafsat din,amma dabi'unta nata nesatata daga zuciyarsa,ya taka a hankali yayi tsaye a bayanta yana goye da hannayensa "Tsakani da Allah haka akewa miji maraba?,mijin da yafi wata guda baya tare da iyalinsa?" Waiwayowa tayi ta watsa masa wani kallo,a yau taci alwashin gwada mishi amfaninta,tunda kare ma ai yana da ranarsa,tasan a buqace zai dawo,zuciyarsa cike fal da tarin buqatun da babu wadda zai dosa da nufin saukewa idan ba ita ba "Bayan marabar daka samu daga wajen wadda ta fini?,ina cewa bani kadai bace iyalin naka" "Na fiki sanin hakan,amma yanzun taki marabar nake da buqata" ya fada yana rungume ta ta baya,saita fara qoqarin tureshi amma ya hana mata wannan damar,har ta gaji ta haqura,sannan ya saketa don kanshi "Kome zakiyi ki dinga qoqari kina zurfafa tunaninki,ina yawan gaya miki,ki dinga sanya hankalinki a gaban fushinki" "Eh ai dama kullum ni nake da laifi,kaikam baka aikatamin komai,duk wani rashin kulawa da kake nunamin ina hadiyewa baka gani ba" "It's okay.....na sameku lafiya?" "Gamu lafiya lau" ta fadi kamar wadda aka cusawa tsumma a baki "Ma sha Allah" ya fada yana shafa sumar kansa sannan ya juya zuwa falon,don sam tarbar da yake da buqata ma bata iya taba har kwanan gobe. Abinda ya fara dawo masa akai yadda widad tayi welcoming nasa,duk da cikin quruciya take komai.....amma komai nata burgeshi yakeyi,yaga zallar kewarsa a idanunta,irin kewar daya rufe mata idanu ta gaza ganin koda hajiya da take kunya da kuma marmarinta,kewar data gaza boyuwa daga idanunta......irin yanayin da yayita begen samu daga hafsat tsahon shekarun da sukayi a tare amma abun ya faskara. Wannan tunanin ya haifar da murmushi saman fuskarsa,bai zauna a falon ba ya dauki yaran suka wuce zuwa sashensa,can dinma ba laifi an dan gyarashi,duk da dama sashensa baya barinsa yayi datti. Ba jimawa ta shigo da kayan abinci,ta zuba masa ta koma gefe ta zauna tana danna waya,fuskarta kadaran kadaham,amma bata tsoma bakinta a hirarsa da yaransa ba,sai daya ci rabin abincin,taga babu alamun widad tare dashi sannan ta magantu "Ina ka baro antyn tasu?" Hankalinsa nakan zarema yaran uban qayar dake jikin kifin data dafa,bata damu data tsaya ta gyarashi da kyau ta cire qayar ba ya amsa mata "Na barta gidan hajiya" haushi ya cikata,saboda ba qaramin aiki ne yake jiran yarinyar ba,taci buri sosai wannan karon,don ta dauki alwashin daga shi har widad din saita fito musu da sabon taku,zuwa weekend din da ya dinga yi babu ita kafin tafiyarsu ta taso ba qaramin qona mata rai yayi ba,saboda ta riga ta saba da ayyukan widad din,wani lokacin tun ranar laraba zata fara hada dalar qazantarta ta jirayi zuwan widad din,tasan idan tazo kamar anyi ruwa an dauke ne,fes ko ina yake komawa. Bata sake tambaya ba don kada ya ramfota,amma cikin ranta addu'a take Allah yasa kada tace zata kwana,a badini ji taje kamar ta tafi gidan hajiyan ta janyo widad din tayi mata shegen duka. Suna qoshi suka bigire da bacci a wajen,dama kusan lokacin baccinsu ne,hannunsa riqe da yatsar nawwara ya saki ajiyar zuciya sannan ya kalli hafsat "Ki kaisu dakinsu kizo ina son ganinki" yayi maganar a tausashe yana duban tsakiyar qwayar idanunta,dauke kai tayi,don batason ya karya mata zuciya kwata kwata,taja tsaki qasan ranta sannan ta yunqura zata miqe wayarta ta dauki tsuwwa,saita dakata ta daga wayar ta sanyata a kunnenta "Hello.....kin qaraso?,kina falo?, okay gani nan" sai ta katse wayar,ta sunkuya ta dauki mimi ta fita a falon. Miqewa yayi ya shige bedroom dinsa ya zarce toilet,yayi brush ya sake alwala,sanann ya fito ya rage kayan jikinsa ya dawo falon,har a sannan bata dawo ba,bai dauka zata dauki tsahon lokaci haka ba,sai ya kunna tv ya kama labarai ya fara kalla,duk kuwa da cewa hankalinsa baya wajen. Kusan minti talatin ba ita babu labarinta,kamar ya shareta sai ya fasa,ya koma ya dauko jallabiyya mai santsi saqar qasar oman ya zuba,ta masa masifar kyau ta qara fidda wannan sirritaccen kyansa,ya dawo ya dauki nawwara suka baro sashen. Ba kowa a falon,amma da alama anyi baquwar ta tafi,dakinsu ya kai nawwara sannan ya dawo ya wuce dakinta. A gaban mudubi ya sameta tana hada kudi,suka hada ido,tasha jinin jikinta amma ta basar,ya zube hannayensa a aljihun jallabiyyar jikinsa yana mata duban da yasan yana ratsa qashinta da kyau "Gani na biyo sahu" ya fada cikin wani salo,ta lumshe idonta, muryarsa ta tabata da kyau,amma girman kanta sai ya motsa "Baquwa nayi,kuma yanzun ma wata baquwar gareni tana hanya" bai sauraren ta ba ya taka zuwa bayanta ya kuma rungumeta da kyau ta bayan,baiyi qasa a gwiwa ba ya fara aike mata da wasu saqonni masu nauyi da tsuma zuciya,sun isketa da kyau kuwa,ita kanta tasan waye abbas din fiye da kowa a duniya,ta wannan fannin idan ana taron bada award.....ba award ba idan akwai abinda ya fishi ya cancanci a bashi,tun tana dojewa har sai da ya zaqulo dukka wani qwarin gwiwarta yayi watsi dashi,ya gigita tunaninta da kyau ya kuma yi mata masauki saman gadonta ba tare data ankara ba,sadai tafiya nayin nisa,yana gab da kaiwa inda yake da muradi hudubar shaidaniyar zuciyarta ta dawo mata,ta tattara qarfinta gaba daya ta tureshi ta koma gefe tana cika tana batsewa. Da qyar ya daga kansa ya kalleta,idanunsa sun canza launi sosai,a sannan idan ka kalleshi zakayi tsammanin barkono aka watsa masa "Me kikeyi haka?" Baki ta turo masa "Sai yanzu kasan ina da amfani?,bakasan fushina ba balle damuwata
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155