Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 3

Chapter 3

A Rubuce Take Book 1 Complete Hausa Novel – Widad and the Secret of House 1,311 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ma dafe,maza garzaya ki nemesu a* _adress dinsu dake No 22 Ahmadu bello way,kano state_ *Ko kuma kuyi order din kayanku kuna daga gida ta shafinsu na instagram* @maabluxuryhome *Facebook* @maabluxuryhome *Ko ku nemesu ta lambar wayarsu kamar haka* 08034631010 *Kyau inganci da rahusa shine takenmu*😊😊🤝🤝🤝🤝 ____________________________ waiwayowa yayi yana dubanta bayan ficewarsu gaba daya,maficin da ummu ta tashi ta bari ne riqe a hannunta tana tsige adon jiki,fuskarta a dinke tsaf,yakanyi.mamakin yadda take masa,kamar wata qatuwar budurwa,ya rasa dalilin da sam bata son su zauna waje guda ko su hadu,saidai har yanzu zuciyarsa na bashi nutsuwar cewa quruciya ce kawai da rashin sanin ciwon kanta,da zarar ta sake hada hankalinta zata fuskanceshi? "Amma sai yaushe?,lokaci qara quracewa fa yake" zuciyarsa ta gaya masa,sai ya dan gyada kai "Soon in sha Allah" ya fada yana bawa kansa qwarin gwiwa,qwarin gwiwar da kusan kullum itace madogararsa "Widad" ya kira sunanta "Na'am" ta amsa a cunkushe ba tare data kalleshi ba,murmushi yayi "To kidan kalleni mana?,ummm,ke da zaki zama matata?,so nake ki saki jiki da yayan naki" manyan fararen idanuwanta ta daga tana kallonsa,wani haushi da kuma tsanarsa suka saukar mata,lallai yaaya mahfood ta tabbata dan iska ne,ita yakewa zancen ta zama matarsa?. Yadda ta zuba masa fararen idanuwan nata sai yaji dadi cikin ransa,don takan jima bata tsaya ta kalleshi ba,wannan ya bashi qwarin gwiwar janyo ledar daya shigo da ita wadda ke shaqe da kayan kwalliya,kasancewar ya santa da son kayan ado da gayu ya tura gabanta "Ga kayan kwalliya nan 'yammatan ummu,sai ayita shafawa ko?" Dauke idanunta tayi daga kansa ta mayar kan kayan,saita dalla wa kayan harara,ita zaiwa wayo?,ya dauka bata da hankali kenan,haka kawai,bayan ummu tasha gaya mata ko zama tayi kusa namiji ciki zatayi,shine zai wami bata kayan kwalliya?,to bai isa ba,tana gama wannan tunanin ta miqe abinta ta nufi qofa da saurinta. "Zo mana widad.....widad"ya fara qwala mata kira,gudun kada latifa ko ummu dake daki su jiyo shi,su kuma sanyata dawowa dole saita fella da gudu ta qarasa ficewa,don ta lura shi kadai ne zaifi mata saurin barin sassan. Bata tsaya ko ina ba sai sassan anty madina,taja birki tana zabga haki,dai dai lokacin da dukka yara yaran gidan da suke da shekaru irin nata ke zaune a falon anty madina,kaf cikin matan gidan ta fisu qarancin shekaru,tana da faran faran da son mutane,tana yawan jansu a jiki gami da biyewa shirmensu,wannan yasa kafatanin yaran gidan kowa ke sonta,yake kuma son zama a sassanta. Dago kai tayi tana duban widad,muhassana ce kwance a cinyarta diya ga qanwar mahaifin widad tana mata tsifa "Lafiyarki widad?,irin wannan cin burki haka?" Guri ta samu kusa da khalisa ta zauna tana maida numfashi,sai kuma ta bata rai, idanuwanta sukayi rau rau suka ciko da qwalla "Yaya mahfood ne" "Mahfood kuma?,biyoki yayi?" Kai ta girgiza tana turo baki gaba,ita sam sam ma batason maganarsa,yanzu su mahassana zasu fara tsokanarta "Wai cemin yayi matarsa" tana fadin maganar qwalla na gangaro mata,qaramin murmushi anty madina ta saki,ta rasa wanne irin rashin haduwar jini ne haka tsakaninsu,duk wanda ya kwana ya tashi yasan yadda mahfood din ke qaunar widad,hakanan kowa yasan yadda take gudunsa,bata qaunar hada inuwa dashi "To banda abinki mene ne don yace miki matarsa iyi widad?,bakiga su zahira ba aure za'ayi musu?,kuma daga su sai ku?" Kafin anty madina ta kammala bayaninta widad din ta saki kuka harda turje qafafu,baki anty madina ta sake tana kallonta gami da jan salati,yayin da su muhassana suma ke kallonta suna dariya "Tsaya,bakya sonshi ne shi yayan naku?" Kai ta gyada "Wallahi ni bana sonsa Allah" "To ya isa,ki share hawayenki,an gama maganar,ba wanda zai baki shi" dif kukan ya tsaya,ta tashi ta zauna dai dai tana goge qwallarta tana kuma hararar su khalisa kan dariyar da suke mata "In sha Allahu sai su abba sun baku dauda" dariya sosai anty madina ta tuntsire da ita,duk da quruciyarta wani lokaci idan tayi wani abun kamar babba,dauda shike wankin gidan,na kowanne sashe,daga qauye yazo a gidan aka riqeshi "Bakinki ya sari danyen kashi" khalisa ta fada tana dariya "Saidai naki bakin" widad ta fada tana sake harararta,dole anty madina ta shiga fadan ta raba,ta kuma janye musu hankalinsu da wani abu na daban. Qememe taqi komawa sassan ummun,duk da ummun ta aiko latifa har kusan sau uku amma taqi komawa,zatonta mahfood yana nan bai tafi ba,wayo ummun keso tayi mata don ta dawo,har abbanta yazo ya tafi bata koma din ba,son samunta ma tayi kwananta nan wajen anty madina cikinsu farisa,amma kuma tana tsoron kyankyaso,kada yayi mata irin yadda yayi mata daxun,har sai data fara barci sannan latifa tazo ta tafi da ita bayan ta tasheta ta sakata a gaba. Tana shiga dakin ummu ta haye gadonta taja bargo ta duqunqune sosai harda cusa kanta cikin pillow,tun tana kasa kunne taji shigowar ummu har bacci yayi awon gaba da ita. Washegari ummun bata ce komai da ita ba,saidai ta bata ledar kayan kwalliyar tace ta dauketa taje ta adanata,aifa kamar jira take,saita dire cup din da take shan tea dashi ta saki kuka "Allah ni bana so,banaso ummu" tana turje qafarta a qasa "Hukumullahu" ummun ta fada a ranta tana zuba mata idanu,wannan abun na widad din kuwa na qare ne?,kullum abu kamar ma sake ci gaba yakeyi?,kafin takai ga sake cewa komai akayi sallama falon,ta dauke kanta daga widad ta maida gareshi taba amsa sallamar. Babban mutum ne ko ace magidanci,wanda kallo daya zaka masa kasan danta ne daga tsatsonta ya fito,a nutse ya qaraso falon yana kallon widad da fuskarta tayi sharkaf da hawaye "Ke kuma da baki rabo da rigima me akayi miki?" Ya fadi yana neman wajen zama,baki ummu ta tabe tana girgiza kai "Don anyi maganar mahfood ne" saita zarce da gaya masa abinda ya faru jiya. Maida dubansa yayi gareta yana nazartarta na wasu daqiqu,shima kallon quruciyarta yakeyi,yasan ita ke dawainiya da ita,don idan a wani gidanne ko zancan aurar da yayunta da za'a aurar yanzu ba'a fara ba bare ita,to amma haka tsarin yake,a haka kuma dukka suke tafiya "K'aniyarki" abba ya fada yana tsuke fuska "Don gidanku mahfood ba babanki bane kike masa irin wannan?,maza tashi ki dauki kayan ki adana su" fuskarta jiqe da hawayen ta miqe ta dauki ledar,sai tayi hanyar fita da ita "Ina zaki?,nan ne dakinki?" Cikin muryar kuka ta waiwayo "Anty madina zan kaiwa...." "Eh itace ke iya jurewa shirmensu ai" ummu ta karba zancan tana qarashewa abba bayani,sai baice komai ba,wannan ya bawa widad damar ficewa. Tana tafe ita daya tana sharar qwalla,maimakon sassan anty madina,sai tabi siririyar hanyar da zata sadata da parking lot na gidan,tasan can ne babu kowa,don duka samarin gidan masu fita kasuwa kawo yanzu sun fita din,sai su 'yan makarantar da suke shirin komawa ranar litinin,sune daliban da aka yaye daga primary school zasu wuce zuwa qaramar secondry jss one. Dan bencin da ake ajewa a wajen lokaci lokaci ta haye ta zauna a kai,sai a sannan ta buda ledar tana duba abinda yake ciki,kayan makeup ne sosai irin wadanda takeso,batayi mamaki ba,don uncle mahfood din ya jima da sanin zabinta da kuma duk wani abu da takeso. Sai data fiddosu tsaf ta qare musu kallo,sai kuma ta tabe baki,motsin da taji daga parking space din

Table of Contents

Chapters

155 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});