Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 82

Chapter 82

A Rubuce Take Book 1 Complete Hausa Novel – Widad and the Secret of House 1,318 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ta bashi dama,lokuta mafi yawa kuma takan tsuqe,tare da kawo masa qorafe qorafen "Ni na gaji yau wallahi......bacci nakeji......bani da lafiya fa....." Ko sau daya bai taba waiwayawa yabi ta kanta ba,ya gwammace ya kama kansa,don baijin zai iya begging dinta akan abinda yake halalinsa,sannu a hankali ta fara cire masa sha'awar ta kwata kwata daga zuciyarsa,sai ya dauki lokaci bai waiwayeta ba,abun har ya fara zame masa jiki. Kamar raqumi da akala haka ya zaunar da ita gefan gadon,ya jawo kujera ya zauna yana fuskantar ta. Nazarinta ya fara,ya zuba mata idanu yana kallonta tun daga santala santalan cinyoyinta zuwa jiqaqqiyar sumar kanta da ta fara tsanewa,idanunsa suka tsaya ga fafaren kafadunta dake cikin farin towel,a lokacin ne hankalinta ya dawo jikinta,ta soma curewa waje daya sabbin qwalla suna cika mata idanu "Mene ne?" Ya tambayeta ganin yadda hankalinta ya tashi lokaci guda "Kaga fa....bani da riga" furucin ya qaraso fitowa da hawaye masu dumi daga idanunta,karon farko da yajin haushi ya kamashi "To sai menene?" Kuka ta fashe masa dashi tana nuna masa hijab dinta "Don Allah ka bani hijab dina na saka,Allah ummu ta hanani" "Tace miki harda ni kada na ganki a haka?" Ya jefa mata tambayar,yau kam sai ya qure tunaninta,kai ta kada "Ban sani ba,ka daina kallona don Allah" ta sake fada tana kuka,shuru yayi yana duban baby face dinta dake jiqe da hawaye,ya gama karantarta,a haka ta taso ba tare da tasan cikakkiyar ma'anar aure ba,kuma ko a yanxun indai yanason ta fahimci abinda zai gaya mata saidai ya bata hijabin yadda takeso,baisan dalil ba,sanda ya miqa mata hijab din,sai yaji baya buqatar ta saka,amma haka ya lumshe idanunsa harta gama sakawar,sannan ta tsareshi da ido tana jan majina. Shima ita din yake kallo,kafin daga bisani ya kauda dubansa,ba lallai ma ta gane meye miji ba bare aure,sai ya ajjiye wannan maganar ya soma mata wadda yake ganin tafi muhimmanci akan wadda da farko yaso yayi mata ita. *Arewabooks:Huguma* KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 53 "Daga yau,duk sanda kike ke daya a nan,ki kunna tv din falo,ki kamo saudi qur'an.....kinjini ko?" Ya furta yana kama kunnensa,saita gyada masa kai "Good.....sannan,baki iya addu'a ba sanda mutum yaga abinda ya tsoratashi?" "Na iya" ta fada a sanyaye "To daga yau ita zaki dinga ya,kada na sake ji ko ganin kina ihun nan......ki fahimta?" Nan ma kai ta gyada masa,ya jijjiga kai,shuru ya ratsa na second biyu "Kin yini lafiya?" "Ina wuni" ta maida masa da gaisuwa da muryarta dake dan rawa har yanzu "lafiya lau" ya amsa mata yana miqewa "Ga saqo can daga kano" fadin kano din da yayi ya sanyata warwarwwa ta farat daya,ya bita da kallo sanda yaga ta doshi kedar fuskarta na haske da murmushi,sai ua juya ya fice daga dakin,yanata juya al'amuranta a ransa,raino ne hajiya ta bashi,raino kuma me wuya da baisan sanda zai gamashi ba. Sanda ya isa sassan hafsat yayi mamakin ganinsa a tsaftace,zai iya cewa ya manta lokaci na qarshe da yaga komai a muhallinsa a sassan nata,baiyi dai magana ba,amma kuma hakan ya masa dadi, zuciyar sa kuma ta sauka,akaci sa'a a yau din ta danyi wankan dare,ta kuma qure adaka da daya daga cikin tsadaddun suturun da yake mata,don tana son ta sake amintar dashi,ta kums kore kowanne zargi daga ransa,uwa uba kuma akwai kudaden da takeson karba daga wajensa a daren. *********To tsahon kwanaki ukun da sukayi a bauchin widad ita kewa hafsat din dukkan wasu aikace aikacen sassanta,kama daga wanke wanke shara da wankan yara da dyk wata lalurarsu,koda bata shigo sashen ba zata shigo da kanta ta fiddota,idan abbas yana gida yafi zama sashensa,takanntattara ta bishi can,bata fita sai idan yasa qafarsa yabar gidan shima. Baisan meke faruwa ba,tunda ya sani akwai alamun tsoronsa sosai tattare da yarinyar,bayason ya dinga matsa mata ko takura mata,ganin yadda taje sakewa walwalarta take qaruwa idan tana tare dasu mimi sai ya saki komai shima,wuni take hidimar sassan hafsat din,girki kawai hafsat din keyi,itama widad din taje tayi nata. Quruciya qarancin shekarunta da rashin wayo ya sanya bata dauki hakan a bakin komai ba, saidai wasu lokutan tana jin aikin kamar yayi mata yawa,amma bata fasa yi mata ba,don a ganinta gaba take da ita,sannan tana samun sassaucin mugun tsoron da hafsat din ta dasa mata a ranta,tsoron abbas din da koda yaushe take zayyana mata abu kaza babu kyau....abu kaza babu kyau,ki tsare mutuncinki,dukka wani halali ta haramta mata shi,tayi amfani da wayo da dabararta da shekaru data daranma widad din. Ranar lahadi da yammaci suka tattara suka bar bauchin,kamar wancan karon,wannan karonma wani abune ya tsaya mata a rai,ta zubawa motarsu idanu sanda take fita daga gidan,zuciyarta a mugun quntace,saidai taci alwashin tafiyar tasu babu abinda zata bari ya sauya,data koma cikin gidan kuma ta sake qarewa sashenta kallo taga yadda ya fara komawa hayyacinsa,sai taji inama widad din a kadunan take,ta tuna gobe fa itace zatayi dukkan hidimar da widad din ke mata,ga shirin makarantar mimi,ranta sai ya baci,haka ta wuni tana qunci tana kuma jibgar yaran,saboda kwanaki biyun bata saka hannu a hidimarsu,duk wata lalura tasu widad dince,wanka tsarkin kashi abinci da sauransu,su kansu yau din duk sai suka zama sukuku,kada ma mimi taji labari,minti daya biyu saita kira sunanta,saida hafsat din ta fara doke mata baki sannan ta samu salaama. Tun a mota widad in ta dinga bacci,baccin gajiyar data debo a kaduna na ayyukan wahalar hafsat,koda suka isa gida ma sai daya tasheta,ta murza idanunta ta buda motar ta fito a kasalance tayi sassansu. Sallar magariba da isha'i kawai tayi ta sake kifewa a dakinta,sanda ya shigo gidan tayi nisa a duniyar bacci,sai ya maida mata qofar dakin nata ya rufe kawai ya sanya ledar takeaway din a fridge don kada ya lalace,mamaki yana dan kamashi da irin baccin da takeyi,kamar wadda bata samun baccin kirki. Washegari da zai miqa ta makaranta ma kusan a makare suka fita,don sai daya shiga dakin ya tasheta sannan ta samu ta shirya a gurguje,don ko gyaran gidan bata samu yiba sai da aka taso daga makarantar,samuel ya aika ya daukota a motarsa ya ajeta gidan,tana shigowa suna cin karo da maami matar gidan,wadda yaranta duka maza ne,shi yasa ba wanda ke shigowa sashen "Yaushe kuka dawo haka babu sanarwa?" Ta tambayi widad tana qare mata kallo cikin uniform din da suka bala'in karbarta "Jiya da daddare ne,uncle yace na shigo na gaisheki ma daman idan an taso daga makaranta" "Oh....makaranta kenan aka fara zuwa,aji nawa?" Ta sake tambayarta "S.s one" kai ta gyada,lallai namiji,shan koko daukan rai,banda qalata irin tasa,itadai bataga abun daukarwa kai wannan dawainiyar ba,amma wataqila kyan yake rudarsa "To Allah ya taimaka" "Ameen,a dawo lafiya" ta fada tana yin gaba zuwa cikin gidan,ita kuma ta amsa tana

Table of Contents

Chapters

155 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});