Chapter 148
Chapter 148
fada yana takowa inda take tsaye,yana karbe jakarta daga hannunta "Uncle....." "Wai ba magana ake dake ba!.....yara suyita musu da na gaba dasu,kaga abban mimi just leave her mu tafi kawai" hafsat ta fada cikin tsawa,bayan baqincikin yadda taga yana lallabarta hadi da riqe mata jaka ya saukar mata ya tsaya mata a qirji. A sukwane widad din ta waiwayo tana jin wutar dai dai take da ita a yau tana tashi cikin kanta,fes ta kalleta ido cikin ido,cikin lallausar muryarta a nutse ta amsata "Sorry mommy....bafa dake nake ba......da uncle dina......au mijina na,da mijina nake magana" *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 97 "Sorry mommy.....bafa dake nake ba,da uncle dina,oh mijina,da mijina nake magana" widad din ta fada kanta tsaye,idanunta cikin na hafsat. Wani abu mai nauyi hafsat din taji kamar an aza mata,kanta ya buga har tana jin wasu sautuka cikin kunnuwanta,ita widad din yau take kalla kai tsaye.....kuma kai tsaye,ido cikin ido take gayawa haka?,a gabanta take kiran abbas da mijinta?. Kafin ta yanke abun yi har widad din ta soma qoqarin zame jakarta daga hannun abbas din,saidai yaqi cika mata,ganin yaqi cika matan saita juya ta fara takawa tana nufar sassanta,tana jin zuciyarta na mata qunci,batasan me yasa mommyn mimin keson shiga harkarta ba,bayan ita ko ganinta batason yi,batason su hada inuwa guda da ita, infact haushinta ma takeji,musamman lokuttan da zata gansu tare da uncle dinta. Sanda hafsat din ta yunqura da nufin fita a motar tabi bayan widad din abbas yayi gaba,sai tayi mutuwar zaune tana binsa da kallo tare da son ganin inda zaiyi,zuciyarta na wani irin bugawa,tana fatar ba bayan widad din xaibi ba,yadda ta zata hakance ta faru,sassan widad din ya shige. Tana shiga ta zare dankwalinta ta aje saman kujera,itama ta haye kujerar wayarta na hannunta tana ci gaba da chat dinta,duk da ranta a bace yake sosai amma batason tabar idanunta da suka tara hawaye su zubda qwalla. Daga bakin qofa ya tsaya hannuwansa cikin aljihun wandonsa,ya zuba mata ido yana kallonta,qamshinsa ya sanyata gane ya shigo,ta daga kai sau daya ta kalleshi ta maida kanta ga chat dinta,qaramin murmushi yaso subuce masa,yana saurin karantarta fiye da kowacce mace a duniya,ya gane fushi takeyi amma batason nunawa,amma kuma shi bashi yayi laifin ba amma abun yana son qarewa a kansa,sai ya tako ya iso gabanta,ya zame a hankali ya duqa saman qafafunsa,ya riqe hannayenta da take chat din dasu yana duban qwayar idanunta "Tashi mu tafi weedad......" Ya kira ainihin sunanta a tausashe,kawai tana daga kai suka hada ido dai kuka ya kufce mata,ya matse hannayenta gam cikin nasa yana jin wani abu na masa suka cikin zuciyarsa,bayason kuka sam,kukan ma kuma nata,bai hanata ba sai datayi kusa minti goma tana yi,sannan ta zare hannunta daga nashi ta dauki dankwalinta ta nufi bedroom dinta. Binta yayi da kallo,bai taba zaton zata bisun ba,amma ga mamakinsa sai gata ta fito,ta wanke fuskarta fes ta sake shafa powder da lip gloss,ta zizarawa fararen idanuwanta kwalli "Muje" ta fada fuskarta babu walwala,yi yayi kamar baiji ba amma idanunsa suna kanta,har zuwa sanda ta tako tazo dab dashi xata wuce sai ya matse mata hanya,ya kuma sanyata cikin jikinsa "Bakya kyau da fushi baby doll,smile please" ya rada mata a kunne,a hankali murmushi ya kubce mata tana dan boye fuskarta. Tuni ta gama cika ta batse,duk inda bacin rai yakai ranta yakai qololuwar zuwa wajen,sau biyu tana aika mimi tayi kiran daddynsu sai tace qofar na a rufe ne,gashi tashi yanzu wuya yake mata,har sai data yunqura zata fita taje da kanta ayi wadda za'a yi,sai gasu sun fito. Sanda ta kalli fuskokinsu ji tayi qafafun ta sun riqe,haka abbas din zaiyi mata?,fuskar widad din kamar ma komai bai faru ba,ta shaqa iya shaqa,sai taji kamar numfashinta xai dauke,dole ta kauda kai daga kallonsu,wata zuciyar na bata shawarar ta fice a motar kawai tace ta fasa zuwa,amma sai wani sashen na zuciyarta ke gaya mata,idan tayi hakan ai kamar taci galaba a kanta kenan. Fuska fs muryarta duka wasai tana tsokanar mimi daketa shirya beads masu dauke da alphabet nawwara na watsa mata,ta buda gidan bayan ta shige,taja yarinyar jikinta ta kama hannunta tana tayata saka beads din tare da warning nawwara cikin wasa kan kada ta sake ta taba musu. Tsantsar baqinciki da bacin rai ya hana hafsat din magana har suka isa asibitin aka sauketa,taso bar musu yaran duka amma nawwara taqi sai mimi ce tabi widad din. Abinda bata sani ba kwata kwata yara basa damun widad,hasalima ita din mayyar yara ce,ko hana mimi zuwa tayata kwana da takeyi hakan baya mata dadi kwata kwata,ita kadai tasan yadda taji,baya ga dan uban tsoron dake bibiyarta harda kewar yaran. Kamar ko yaushe zama yayi a waje ya jirasu har aka gama,wannan karonma mimi ta samu albarkacin widad din,an wanke mata kan tsaf,yarinyar sai murna take tana shafa sumartata tana kallon widad "Anty ashe da dadi" sarai widad ta fahimci me take nufi,tana nufin kanta yayi mata sawai,kuma ta tabbatar iska mai dadi yanzu tana shiga kan. Tunda suka iso gidan,tun basu shiga ba gaba daya aka saukar mata da bacin rai da baqinciki,taji kamar ta cewa abbas don Allah kada ya shiga ya koma da ita,haka ta dinga qoqarin dannewa har ya saka kan motarsa cikin gidan. Tana tsaye daga bakin window tana hangen komai dake faruwa cikin gidan,don haka tana hangen sanda ya ajjiyeta ya koma,ta jijjiga kai tana sakin labulen falon. Da daren ranar ta dinga tsoron kada abinda ya faru xuwanta na qarshe bauchi ya sake maimaita kansa,idan ta runtse ido saita bude,ba motsin komai ko alamu na faruwar wani abu,daga baya tayi dukka addu'o'inta don haka ta samu relief sosai,saidai gidan gaba daya taji ta tsaneshi,tsananin tsana ta gasken gaske,a lokacin taji bata da wata buqata data wuce tabar gidan,bata da wata buqata data wuce ta ganta ba cikin gidan ba,haka ta dinga yawo tsakanin falonta zuwa bedroom,sai tayi kamar zata fita saita koma bakin qofa ta zauna ta fashe da kuka,kusan awa uku tana a wannan halin kafin daga bisani bacci yayi awon gaba da ita a nan bakin qofar a yashe a qasa. *W A S H E G A R I* Yadda parlor din yake fitar da sassanyan qamshi mai dadi,hakanan jikinta yake fidda nashi salon qamshin daban,girkinta ne ko ba girkinta ba,wannan duka bai dameta ba,kusan qamshi da tsafta sun zame mata gaado idan ana gadonsu,tun daga hannun ummu kawo yanzu. Ita daya ce a parlor din,kwance cikin doguwar kujera mai cin mutum biyu,wani doguwar rigar material onion color ne a jikinta mai gajeran hannu,kanta babu dankwali sai sassalkar sumarta mai tsaho baqi da santsi data dameta cikin robber band,sai qyalli take saboda gyaran kan da taje shekaran jiya, hannunta wayarta ce,sunata hira da balkisa,bata jin dadin zaman ita daya,yau gaba daga ko dauriyarsa mimi ba,abinda bata sani ba hafsat dince ta hanata shigowa kwata kwata,ita kuwa koda wasa batayi gefan hafsat din ba,indai ba dalili bane ya hadasu a farfajiyar gidan,suna iya gama kwanakinsu duka basu hadu ba,hatta da gaisuwa da take zuwa mata a yanzun ta ajjiyeta gefe,idan sun hadu su gaisa,idan basu hadu ba fine,ta bawa bilkisa labari, bilkisan tana ta tsokanarta "Sanda nace
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155