Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 125

Chapter 125

A Rubuce Take Book 1 Complete Hausa Novel – Widad and the Secret of House 1,326 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kice idan ta gama tazo su gaisa da umminki,a kwashe kayana abincin nan ma a wajen" ta kuwa falla da gudu tayi dakin,abbas yabi yarinyar da kallo,yana jin shima kamar yabi bayanta. Sauke idanunsa yayi yana miqewa tsaye hadi da daukar wayarsa dake aje gefe "Kada ka fita fa,inason zamuyi magana ne ai" aninda ya dauke wutar magana cak a falon,kowa yayi shuru sai sautinta daya fita dake yawo,da mamaki ya kalleta,wacce magana ce da basuyita ba kafin ya fito sai a nan? "Hajiya wajenki nazo akan abbansu mimi" "Tooo.... ikon Allah,koma to ka zauna" hannuwansa ya sauke,ya koma hannun kujerar daya tashi a kai ya zauna,can qasan zuciyarsa nason darsuwa da bacin rai amma yana kaudarwa,tunda har yanzu baisan dalilin zuwan nata ba,saidai kwanyarsa nata son hakaito masa abinda ya faru da zai sanya tayi tattaki qafa da qafa har gaban mahaifiyarsa ta kawo qararsa,duk da bawai yau aka fara ba. Kafin takai ga cewa komai widad ta fito,riqe da hannun mimi sunata dariya abinsu,cikin wani lace sky blue da ratsin farin zare da aka yiwa dinkin tea bubu,bata daura dankwali ba sai siririn mayafi data dora a kanta mara nauyi kalar sky blue din. Idonsa ya lumshe ya kuma budesu yana sake zubesu a kanta,yaji wata nutsuwa na maye gurbin abinda keson motsawa daga zuciyarsa. Tare da qamshin nan nata ta iso,ya buwayi falon kuwa gaba daya,cikin ransa yake raya tabbas itama da qaunar turare cikin jininta,ta duqa cikin girmamawa ta gaida baba hassana. Kadaram kadaham ta amsa mata,tana qare mata kallo a fakaice "Tirqashi" ta fada qasan ranta ganin yadda yarinyar take sake juyewa,kyakkyawar siffarta da kuma kamanninta suna sake ninkuwa da bayyana kansu,idan akace za'a hadata da hafsat ko a yanzun ratar me yawa ce,balle kuma ace nan gaba?,ai sai abinda idanu suka gani,ita kuwa lami(mahaifiyar hafsa) tana aikin me?. Sanda widad din take gaida hafsan sai data tattaro dukkan qarfin halinta sannan ta iya amsa mata,gaba daya yarinyar tayi mata ba zata,tsahon wata dayan da bata ganta ba sai taga ta cika sosai,ta kuma fara zama cikakkiyar mace,gabanta yayi.mugun bugawa sanda zuciyarta ta laqana mata tambayar shin me zai kawo wannan sauyin?,ita kadai ta girgiza kai,bata yarda komai zai faru ba,a yadda abbas din yazo mata a zafafe jiyan ta tabbatar bai samu komai daga gareta ba,inda ya samu din ta tabbatar bazai zo mata a birkice haka ba,bataga wani sauyi daga wajensa ba duk sanda yayi mata zuwa irin wannan,saima qaruwa da abun yayi,duk da cewa taga wasu qananun sauye sauye,kamar mitar rashin shaving da turare a jikinta,saidai basukai mizanin da zata dorasu a komai ba,tunda batasan da zuwansa ba ai,ganinsa tayi katsam,bai kuma gaya mata yana da buqata ba ballantana ta shirya,kai koda ya gaya matan ma iya abinda zata iya shi tayi shi kuma zata ci gaba da yi. Motsawa baba usaina tayi "Bari na baku waje,naga kamar magana zakuyi" "Haba,kiyi zamanki,duka ba 'ya'yanki bane" hajiya ta fada da kyakkyawan nufi,dama haka takeso,don haka ta koma ta zauna din tana cewa "Hakane,ia bakaqi ba,kada aga kamar bakasan matsalar kowa ba sai taka,d'a ai na kowa ne, bare abbas da kowa yakecin moriyarsa?". "Ina jinki hafsatu,mene ya faru?,ina fata ba matsala bace" fara matsar hawaye tayi sannan ta magantu "Matsala ce hajiya, matsalar kuma abban mimi ne da kansa yakeson haifar da ita cikin gidansa" "Tofa!,tirqashi!" Baba usaina ta fada da madaukakin sauti bayan ta kama haba,yayin da abbas ya bude dukka idanunsa a kanta yana kallonta,tare da sauraren wanne kalar sharrin kuma zatayi masa "Mene ne ya faru?,gayamin" gyara zaman "Hajiya,kwata kwata abban mimi bambanci yake nunawa tsakanin da widad muraran,bayason huldarmu ni da ita,qiri qiri sai suzo weekend har su gama bazanga fuskarta ba bare ta zauna a gidanta ba,wasu ma basai suyimin sharrin na hanata zama ba?" "Laahhhh,da gudu kuwa,mutumin yau da baka iya masa?,tabdi" baba usaina ta karbe zancan "To bama haka ba,ta yaya zamu shaqu mu fahimci juna da ita hajiya tsakani da Allah,sannan su kansu yaran nan bakiga yadda sukeson zama da ita ba,amma gaba daya basu samun ganinta,a haka kan iyalinsa zai hadu?" Shuru hajiya tayi tana jinjina kai,maganarta ta qarshe ce kawai taja hankalinta,har takega tayi magana me ma'ana,baba usaina nason tsoma bakinta tace wani abu,amma kuma kwarjinin abbas din ya hanata,banda "Gaskiya ya kamata a aduba,saboda gobesu dana yaran" shi taketa maimaitawa "Kinzo da magana me kyau da ya kamata a duba,ki kwantar da hankalin ki, za'a gyara lamarin in sha Allah, Allah yayi muku albarka,ya qara hada kanku,ya wanzar da zaman lafiya a tsakaninku" "Ameen ameen.... yauwa,hakan dai yafi gaskiya,ta nan ne zasusan darajar juna,ita tasan darajar uwargidanta". Taso ta sake qirar wani abun,amma hada idon da sukayi dashi yasa ta kasa cewa komai,sai kawai ya miqe ya fice afalon ransa yana masa suya,fita yasoyi amma sai ya kasa,yana daya daga cikin kujerun dake harabar gidan ya zauna kawai,qafarsa daya kan daya yana dan jefata a hankali,bacin ransa yakeson dannewa,ba kasafai ya fiya son barin bacin rai yana masa tasiri ba. Ba jimawa baba usaina ta fice,daga bisani hafsat din ta fito yaran suna biye da ita,hajiya a bayansu tana rabawa yaran alawa da manyan biscuits data saba basu,daga inda yake zaune yana kallonsu,yasan babu lallai su ganshi,har suka fice daga gidan ya kasa motsawa sai rakiya da yayi musu da idanu. Sai da aka kira azahar ya fita masallaci yayi sallah,daya dawo sai ya bude setting room din gidan dake farfajiyar gidan ya kwanta,har yanzu abun yana masa yawo a zuciya,shi har yanzu baiyi girman da za'a daina kawowa hajiya da kawunnansa qararsa ba?,har yanzu baiyi girman da kunnuwan hajiya zasu daina jin matsalarsa da damuwarsa ba?,har yanzu hafsat batayi hankalin da zata zauna dashi su fahimci juna su warware matsalarsu ba shi da ita ba tare da duniya taji ba?,kansa ya kada a hankali yana kiran sunan Allah,ya rasa yadda zai rabata da wannan halin,bayan shi din har yau bayajin zai iya tuna wata rana da ya taba kai qararta gidansu ba. Wayarsa dake saman kansa ya dauko,ya lalubo number dinta dake rubuce da sunan BABY DOLL ya kira, ringing daya aka daga,muneera ce,ta gaya masa sallah takeyi,yace idan ta idar ta gaya mata ta sameshi a setting room,ya ajjiye wayar yana gyara kwanciyarsa. Minti biyar cikakku qamshinta ya fara marabtarsa,ya rufe idanunsa yana budesu,suka sauka a kanta,hannunta dauke da madaidaicin tray data dora wani glass jug akai da qaramin cup guda daya. Ido ya zuba mata yana qare mata kallo son ranshi,kamar kowanne lokaci sai yaji damuwarsa tana raguwa,a nutse ta iso ta sunkuya a gabansa tana ajjiye masa jug din,sai ya fara yunqurin tashi,ta miqe zata ja baya ya samu nasarar riqota,yayi mata mazauni saman cinyarsa,kunya ta sanyata boye kanta a kafadarsa,taqi yarda su hada ido "Ki kalleni please baby.......zuciyata ba dadi,nasan zan samu relief" har cikin zuciyarta taji wani abu ya tabata da fadin hakan,saita daga kanta da sauri,kodai qarar da mommy hafsat ta kawowa hajiya ce ta bata ransa?,ta tuna kalaman mommynta na qarshe "Banda kai miji qara,abune mara kyau,koni bance ki kawomin qararsa ba,idan ya bata miki rai ki gaya masa ku fahimci juna" sannan ta tuna da kalaman ummunta "Kome mijinki yayi miki ya isa ne,banason qorafe qorafe dakai qara" sannan tana tuna yadda take

Table of Contents

Chapters

155 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});