Chapter 103
Chapter 103
har aka gama,motar nada wajen zama biyu,sai wajen zaman driver,hajiya ce ta fara shiga seat din da yake da maqotaka dana driver "Bazan shige ciki ba abbas saboda qafata" "Ba matsala hajiya yayi hakan" yana shirin yima muneera magana kan ta shiga gefan hajiya sai weedad ta fara takowa,tsaf ya fahimci abinda take shirin yi,jiya kawai dama kawaici yayi mata,a yanzun sai yayi kamar bai ganta ba,sai da tazo daf dashi ya sanya hannunsa ya riqe hannunta da kyau,baiko waiwaya ba bare kayi zaton ya riqeta din,cikin sauri ta daga kai tana kallon fuskarsa,yasha muur da kyau,baiko kallon sashen da take kamar bashi bane ya riqeta. Gyaran murya kadan yayi sannan ya kira muneera yace ta shiga gefan hajiya "Saura ki saki baki kima mutane bacci ki barta da kallon hanya" murmushi ta danyi "Bazanyi ba uncle in sha Allah" hannu yasa ya rufe murfin motar,ya bude seat din baya sannan ya waiwaya ya kalleta. Cikin sa'a itama shidin take kalla, idanuwansu suka hadu waje daya,har cikin jininsa sai da yaji wani abu mai kaifi ya saukar masa,ya kuma baza saqonsa zuwa kowanne sashe na jikinsa,ya sake dawo masa da sweet memorie dinsu na shekaran jiya,wannan ya sake sanyawa gaba daya jikinsa ya amsa "Shiga" ya fada da mugun sanyi,narke fuska tayi sannan ta matsa ta shige yabi bayanta,ya maida murfin ya rufe sannan ya yiwa samuel da suka saba yin tafiyar dashi magana kan ya tashi motar suje. Gefe daya na motar ta rakube,gaba daya fuskarta a narke take,kamar wadda ke jiran qiris ta sanya masa kuka,yi yayi kaman bai fahimta ba,sunata hirarsu shi da hajiya,har taji shurun widad din yayi yawa "Widad ko.tayi bacci ne?" Hajiyan ta tambaya ba tare data waiwayosu ba,sai sannan ya juya inda take zaunen,tausayi ta bashi da kuma dariya amma ya danne,suna hada ido sai hawayen da take maqalewa ya sauko,ya miqa hannunsa ya lalubo tafin hannunta,duk da yadda take faman boyonsa ya sanya shi cikin nasa,sannan a hankali ya janyota zuwa kusa dashi ya hade duk wata tazarar dake tsakaninsu sannan ya amsawa hajiyan a ladabce "Idonta biyu hajiya" "Au to madalla". Tun basuyi nisa da tafiyar ba bacci ya dauke hajiya,muneera ce kawai ta rage wadda taketa game da wayar hajiyan,har a sannan tafin hannunsa yana cikin nata yana yamutsawa,santsi da laushinsa ke haifar masa da wata kasala ta daban,maqoshinsa gaba daya ya bushe,ya kalleta ta gefe "Bani ruwa" ya fada a taqaice,kamar jira dama takeyi ta zame hannunta daga cikin nasa,saidai kafin ta gama zamewa ya maida hannun cikin nasa,ta juyo suka hada ido ya kada mata kai "Zan dinga hukuntaki fa" yayi maganar can qasa da wata irin gajiyayyar murya,sai tayi narai narai da ido tana kallonsa,ya girgiza mata kai da sauri "Kinayimin kuka zan cinye idanun" yadda yayi maganar with seriousness ya sanya mata dan jin tsoro,sai ta kifa kanta saman cinyarsa,abinda ya sanya numfashinsa yin qaura na wucin gadi,ita kuma ta tura kanta da kyau tana son goge hawayen daya fara fita kada ya gani. Da sauri ya saka hannunsa ya daga fuskartata,idanunsa suna rurrufewa,bugun zuciyarsa na fita da sauri "Ya isa....banaso.....idan nace ki bari ki dinga cewa to,understand?" Kai ta gyada masa "Good,bani ruwa" a hankali ta dauko masa ruwan,duk da yadda jikinta ke rawa,shima ya lura da hakan,sai ya sakar mata hannun ya karba ruwan,ya balle gorar ya sanya bakinsa bayan yayi bismillah ya soma sha. Tas ya shanyeta,ya maida numfashinsa,ya juya kadan suka hada ido,tunda ya fara shan ruwan ta zuba masa ido tana mamakin yadda yakeshan ruwan,kamar wanda ya jima baiga ruwa ba,suna hada idon ta dauke kanta,ya saki murmushi,ya gama karantar komai daga qwayar idonta "Zo kiji" ya kirata can qasa kamar yadda suke maganar tun daxu, saboda muneera da hajiya da suke cikin motar,bata musa ba ta matso dab dashi,sai yasake hade hannayensu waje daya yana kallonta "Menene auratayya?" yayi mata tambayar kai tsaye,tambayar da ya jima yanason mata ita,tambayar data sakata rufe idanunta gam lokaci guda,zuwa yanzu koda batasan ainihin me yake nufi ba,daga karance karancen data fara ta fuskanci wani abune mai girma,wani babban alaqa ce babban gini da kuma qatuwar dangantaka tsakanin namiji da mace,zuwa yanxu kuma tambayar ta girmi tunaninta,ta kuma haifar mata da wani jin nauyi da kuma kunya. Yadda ya rutsata da ido haka tabar idanun nata a kulle,wayyo Allah kawai take fada a ranta,itadai wannan iskancin ya fara isarta,inda ya barta kusa da hajiyar da duk haka bata faru ba,sai ya saki murmushi yana sakar mata hannyenta,bai sake cewa komai ba,haka itama,a haka har baccin ya soma fusgarta,sai yayi mata makari da manyan kafadunsa,sanda baccinta ya fara nisa kwance tayi bisa kafadun nasa ba tare data sani ba,wannan ya bashi wani irin yanayi mai dadi sanda suke keta dazuzzuka,yayin da tayi wani bacci mai dadin gaske bisa kafadun nasa. Cikin ikon Allah suka iso bauchi lafiya,yayi yayi da hajiya ta fara sauka gidansa amma tace sammm a gidanta zata sauka,dole haka ya wuce da ita gida,sanda suka isa gidan akwai mutane,yaranta matan su uku duka suna gidan su da yaransu,sun gyare gidan sunyi duk wani abu na tarbarta,kowa kallon widad yakeyi,cikin watannin ta sake girma da cika,tayi wani fresh,abinka da farra fata idan ya samu hutu,cikin girmamawa ta gaida kowannensu,tunda dui cikinsu babu sa'arta,sun haifeta ma,qaramar cikinsu ce take ganin zasuyi sa'anni da anty deena. Ina ka saka ina ka aje suka dinga yi da abbas din,shima da yake mai.kirki ne kuma na mutane sai yadan zauna shima a cikinsu kusan awa daya,lokacin har maqota da sauran matan kawunnansa sun fara shigowa yuwa hajiyan barka da zuwa,kusan kowa ya shigo idonsa akan widad "Amaryar abbas ce?" Haka suke tambaya,kowa da abinda ke cikin ransa,ya kusa shafe awa daya sannan ya miqe da zummar tafiya "Dauko mayafinki ku wuce widad kinji,sannunki kema da qoqari ansha hidima,Allah yayi albarka ya bada zuri'a ta gari" baki baba usaina ta tabe,matar daya daga cikin kawunnansa,wadda suna da 'yar alaqa da hafsat din,fuska ta marairaice wa hajiyan,qasa qasa take gaya mata "Don Allah hajiya a barni a nan na kwana" can qasan ranta tana fargabar yadda yake liqe mata,a yanzun baya jin shakkar tabata,idan mommy hafsat ta gani tace mata meye?,gwara tana nan din,basu hadu ba bare ta gani. "Yaa abbas,ka barta zuwa anjima din kamar haka takeso tace ko?" Qanwarsa ta fada wadda ke kusa da hajiya,ta kuma ji abinda take fada din "Idan ka fito saika biyo ku tafi,idan ma baka zo din ba zan sanya a rakota" hajiya ta qara masa bayani. Idonsa ya maida kan widad din data wani lafe a gefan hajiyan,suka hada ido sai ya dauke kansa,itama janye nata idanun tayi cikin ranta tana jin kamar ta tsira,ya gyada kai "Shikenan hajiya,a huta lafiya" "To Allah yayi albarka,a gaida kishiyoyina" a hankali ya juya ya fice daga falon "Tirqashi" baaba usaina ta fada,yaaya bara'atu ta daga kai ta kalleta "Baaba usaina lafiya ko?" Baki ta tabe a fakaice,amma a zahiri sai tadan murmusa "Ina ganin rashin kunya irin ta yaran zamani,kema banda abinki hajiya kibar masa matarsa su wuce mana" "A'ah gwara ta zauna a gaisa sosai,aita kwan biyu dama bataxo ba" hajiya ta amsa mata cikin bagarar da zancan,don batason dogon zance. Sai da suka tsaya a hanya ya sake yin siyayya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155