Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 7

Chapter 7

A Rubuce Take Book 1 Complete Hausa Novel – Widad and the Secret of House 1,293 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

LUXURY HOME* *_idan kaji gangami akwai labari_* *_SABUWAR DUNIYA CE_* *ALFAHARIN UWAR GIDA* *FARINCIKIN AMARYA* *MAIDA TSOHON GIDA SABO* *DUNIYAR QYALE QYALE* *KAYA NA ALFAHARI DA TAQAMA* *_Ba iya kyawun idanu suka tsaya ba,harma da ingancinsu da kuma qwarkonsu,ka dade kana mora kana kece tsara a tsakanin tsararraku da sauran mutane_* *nasan zaku tambaya ina ne nan?* *MAAB LUXURY HOME* 😊 *Kai daga jin sunan ma babu tambaya* *_duniyar qawata muku gidajenku ku ganku kamar a wata nahiya ko wata duniyar_* *Suna kawo kayan kitchen rankatakaf manya da qananu* *Kayan gado dana parlor* *Kai...suna kawo kowanne nau'in kayan ado na cikin gida* *Karkiyi qasa a gwiwa kuma kada kiyi sake ma dafe,maza garzaya ki nemesu a* _adress dinsu dake No 22 Ahmadu bello way,kano state_ *Ko kuma kuyi order din kayanku kuna daga gida ta shafinsu na instagram* @maabluxuryhome *Facebook* @maabluxuryhome *Ko ku nemesu ta lambar wayarsu kamar haka* 08034631010 *Kyau inganci da rahusa shine takenmu*😊😊🤝🤝🤝🤝 ____________________________ *Widad* Alhaji salim musayyib mai fata shine cikakken sunan,mazaunin maiduguri da wanda aka haifa a can,ya taso ya girma ya kuma yi gwagwarmayar karatunsa dukka acan din,nau'in jinsin nan da mutane ke kira da suna SHUWA_ARAB,saboda asalin iyayensu da kuma kakanninsu dukka ba'a maiduguri aka haifesu ba,ba kuma anan sukayi rayuwarsu ba,rayuwar da sukayi a maidugurin duka duka 'yar taqaitacciya ce,sanadin kasuwanci,asalin tushensu sun fito ne daga qasar mali zuwa yemen,kuma har yanzu danginsa da tushensa suna can gaba daya ko nace mafi yawa daga cikinsu,iyali ga mahaifinsa musayyib suke ta yado a nan,da kuma nashi ahalin shima daya tara. Matan aurensa biyu dukka 'yan asalin qasarsa wadanda suka hada masa tarin zuri'a da kuma yara masu yawa,dansa na farko da matarsa ta fari wadda ta kasance balarabiyar qasar yemen shine mahmud,wanda yake mahaifi ne ga widad data kasance ruwa biyu,balarabiyar mali kuma bafulatanar usul daga katsina ta gefen mahaifiya,wannan shi ya taru ya bata wani irin sassanyan kyau daya banbanta da kyawun dukka cousin dinta da kuma sauran 'yan uwanta,domin ita daya mahaifiyarta ta haifa ta barta a gidan,sai tarin 'yan uba da kuma cousins da take dasu. Yanayi na rayuwa da kuma kasuwanci ya maido alhaji salim qasar kano da zama,ya fara tara iyalinsa shima,bayan ya aurar da mahmud arziqinsa ya qara ninkuwa fiye dana da,wanann ya siya manya manyan filaye ya hadesu waje guda,ya kuma yanki wani sashe na gidan ya fara ginin matsugunnin da zai zauna da matansa da kuma yaransa,bayan ya kammala suna gab da tarewa matarsa ta biyu ta rasu,sai mahaifiyar mahmud ce kawai Allah ya qaddara mata zama a gidan. Mahmud ne kawai ke rayuwa a wajen gidan,girman gidan ya sanya duk yaronsa daya tashi yin aure,za'a fitar masa da tsarin ginin da zai dace da gidan a gina masa ya tare a ciki,wannan yasa sannu a hankali gidan ya zama babban family house dake dauke da sassa sassa guda biyar,kuma kowanne sashe cike yake da albarkar zuri'a wadata da kuma kwanciyar hankali. Widad ta kasance ta musamman a wajen ummu,saboda ummun ta bude idanu ta gani a matsayin uwa kuma mahaifiya a wajenta,don itace ta raineta tun tana tsumman goyonta har kawo yanzu da shekarunta suke goma sha daya da watanni a duniya. Soyayyar da ummun itama kewa widad din ta banbamta data kowa,saboda itama tana jinta da matsayi biyu ne a wajenta,d'iya kuma jika,ta manta da raino sanda ta amshi widad da nufin rainonta,don a sannan ta aurar da autarta ma anty halima tuni,kasancewar su din basa zurfafawa karatun boko,kina gama primary ma kika samu miji to tabbas alhaji salim zai bada aurenki ne, matuqar ya yarda da addinin mutum da kuma mutuncinsa,ruwan miji ya barki kici gaba,ruwansa yace a'ah. Ko kadan rashin uwa bai wani taba widad ba,saboda ta samu dukka kulawa da 'ya ke samu ga mahaifiyarta daga wajen ummu. Mahfood d'a ne ga baaba maisara,wanda suke 'ya'yan wa da 'ya'yan qani da mahaifin widad,tun kafin ta kawo haka yake nuna yana da interest a kanta,amma ko daya widad din taqi sake masa balle ya samu fuskar da ko hira ta zauna tayi dashi,saboda ita din wata irin mutum ce,tana da wahalar sabo,hakanan idan kanason ganin kazar kazar dinta da hirarta to cikin gidansu ne,musamman sassan ummu ko na anty madina,indai akace maka baqon guri ne zaka tsammaci cikakkiyar magana ma bata iya ta ba. Abu na biyu tana da masifar tsoron maza,saboda kullum hudubar ummu shine,idan ta sake ta yarda ko hannunta namiji ya kama zatayi ciki,idan kuma ta samu ciki mutuwa zatayi,wannan yasa sam sam bata yarda ko inuwa su hada,bama shi ba,dukka samarin gidan da suke a matsayin yayye a wajenta haka dabi'ar ta take. _wannan kenan_ *Bayan shekara uku* Tun daga daren juma'ar da ya kama gobe sallah gaba daya yanayin gari ya canza daga yanayin azumi zuwa yanayin daren sallah,ko ta ina al'ummar musulmi sai hada hada ake,tituna zuwa layuka,gidajen kitso qunshi zuwa shagunan masu dinki ko ina cike yake danqam da jama'a kamar rana. Haka ce ta kasance gidan alhaji salim musayyib,babban gidan dake dauke da family masu yawa,a dabi'ar gidan babu tsawwalawa,koda salla ce kowanne sashe yana yin kalar girkin da mace ko matan sashen suka tsara yi,saboda kowanne part akwai store da kuma kitchen din su tare da me aikinsu,saidai idan an gama ranar sallah dukka suna zubawa abincin mai dan dama su aike sashen surukarsu hajiya ummu,duk da ita dinma ba zama take ba, takanyi abinci har kusan kala biyu,sabida karbar baquncin jikokinta dama surukanta matan 'ya'yanta maza guda biyar da Allah ya bata,su da 'ya'yansu da kuma 'ya'yan wajen diyarta halimatu,hakanan su kansu jikokin dake cikin gidan suma kusan a nan suke zuwa su karba nata,sukance yafi dadi. Dai dai lokacin da sassan anty madina yake a cike da yara yaran matan gidan,wanda ake ta faman saka musu qunshin salla daga mai qunshin da ummu da kanta ke daukowa ayi musu,sannan kuma ga me kitso itama tanata kitse musu kansu duk da baiwar suma da yalwar gashi da suke dashi tubarkalla,babban falon da anty madinan ta ware musu saboda irin wannan hidimar a kacame yake. Daga gefe daya widad ce zaune,tsahon shekaru ukun data qara kyawunta ya sake bayyana muraran,hakanan alamun girma sun fara bayyanar mata,duk da cewa har yanzu gabunta sakarci da kuma wautarta tana nan,cikakkiyar GOYON KAKA,Qunshinta yafi na kowa jan lokaci,saboda ummun tace na musamman za'ayi mata kamar yadda aka saba,masu zumbura baki nayi masu qorafi nayi,to amma kusan idan da sabo an riga an saba,haka sukayi suka gama suka kuma haqura. "Aafiya ciremin lallen nan" widad ta fada tana yamutsa fuska saboda jimawar da tayi a zaune "ke kam kin huta,sauranki kitso" afiya ta fada tana matsowa hadi da fara sabule ledar da aka rufa hannun,harara widad ta jefa mata "Tabdijan,wa za'ayi wa kitson?,Allah ya kiyaye" ta fada tana bata fuska,kitso babban abokin gabarta ne,sam bata qaunarsa,tun daga quruciyarta kawo yau tsaf zata iya irga adadin sau nawa aka taba yi mata kitso,mutane kance saboda tana da suma me kyau ne da tsaho,kusan sumarta ta zarta dukka ta yaran gidan,tamkar zabarta akayi,hakan kuma baya rasa nasaba da gado da tayi ta wajen uwa da uba,don idan ta ware sumarta tana iya saukar mata har tsakiyar gadon bayanta. Dariya afiya ta saki tana ci gaba da tsokanarta "Nikam naga

Table of Contents

Chapters

155 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});