Chapter 73
Chapter 73
ya sake bata second option,nan ma ta girgiza kanta da sauri. Ranshi ne ya baci,har yaja tsaki a fili,wacce irin yarinya ce ita?,duk option din da aka bata bai mata ba? "Ba zaki dakina ba,bazaki dakinki ba,to zaman gadinki zanyi?" Ya tambayeta emotion din fuskarsa yana sauyawa zuwa bacin rai. Maimakon amsa saita sakar masa kuka sosai,abind ya hasalashi ya sakar mata tsawa,tsawar data sanyata durqusawa a wajen tana kuma sakin wani kukan tare da kiran sunan ummu. A take jikinsa yayi sanyi,yaga kuma rashin kyautawarsa muraran "Sai ka dinga haquri da ita,kana kwatanta mata abubuwa,bata zama cikakkiyar budurwa ba,da quruciya har yanzu a tattare da ita,to zaka yita ganin yarinta,sai kayita haquri kana gyara mata,amma data gane abinda kakeso da wanda baka so,zakaji dadinta fiye da kowa" maganar da sukayi da hajiyansa ta qarshe ta dawo masa,wannan yasa temper dinsa ta sauka,ya tako a hankali ya tsaya a gabanta "Get up....tashi" ya fada a tausashe,saita miqe din tana sanya gefan dankwalinta tana goge fuskarta,duk da hawayen sunqi tsaiwa "Yanzu ya kikeso ayi?" Ya tambayeta yana narkar da idanunsa cikin nata,itama kallonsa takeyi,ya fuskanci ko a jikinta bata jin nauyin kallon qwayar idanunsa,ta gaza bashi amsa sahihiya,ya kuma gane tsoron hada daki takeyi kawai dashi,kamar kuma yadda take tsoron kwana ita kadai,tsahon wasu sakanni da shuru ya biyo baya sai ya gyada kai "Shikenan,ki kwanta a daki,zan zauna a falo har kiyi bacci" a hankali ta gyada kanta,hakan yayi mata,yafi ace ya koma dakinsa ya kulle ba kowa a kusa,duk da dakunan kusa da juna suke. A gaba ya sanyata har dakin nasa,ya dauki duk.abubuwan da zai dauka ya ajjiye a falon,ya maidata dakin ya tsaya harta kwanta sannan ya ja mata qofar ya dawo falon ya zauna saman kujera hadi da jingina filo bayansa da gefansa don yafi jin dadin zama,sannan ya buda wani qaramin littafi ya soma dubawa. Fakare tayi cikin bargon data lulluba har kanta tana rarraba ido,lokaci lokaci tana dan jiyo motsinsa daga falo,wannan ne ya sanya mata nutsuwa,har sannu a hankali bacci ya saceta ba tare data sauya koda kayan jikinta ba. Awa guda y bayar sannan y shigo dakin,ganin qarar qofar dakin bai sanyata ta motsa ba ya fahimci tayi bacci,sai ya koma da baya yana sake rufe mata dakin,ya koma falon ya kwashe kayayyakinsa ya wuce nasa dakin "Case closed" ya fada a ransa,amma yana tunanun haka zasu maimaita da ita gobe?,kenan wani sabon duty dinne ya sameshi "Ya rabb" ya furta yana furzar da iska daga bakinsa,ya ajjiye komai a muhallinsa y wuce bandaki don yayi wankan da rigimarta ta hanashi yi. Tunda gari ya waye ta dawo falon ta zauna,bayan ta dafa ruwan zafi kamar yadda latifa ta koya mata,ta hada da cup da tea flask din ta dora saman table,tun daxu take jiyo motsinsa cikin dakin,amma bata yi qoqarin shiga ba,saidai ta zubawa qofar dakin idanu tana qiyasta sanda zai fito. Yana taba handle din ta sake zubawa qofar idanu,ya fito a hankali cikin police uniform,sun masa wani irin kyau kai bakace uniform na ya sanya ba,haiba da kwajininsa sun fita sosai,tsayayyen namiji da siffar qarfi ke bayyana a halittarsa,qafafunsa saye cikin baqaqen boots,yana shirin rufe qofar ya lura da ita,sai ya waiwayo yana dubanta da mamaki kan fuskarsa,da yaji shuru yayi tunanin har yanzu tana daki baccin takeyi,dalili kenan da bai tasheta ba. Sosai ya sake mata kwarjini,wani tsoronsa ya sake shigarta,sai ta dauke idaninta ganin yadda yake kallonta,tura baki gaba, itafa duk wanda yake kallon mata dan iska ne a wajenta,ta sauke qafafunta qasa sannan tace "Ina kwana?" Bai amsa ba sai daya rufe qofar dakin,sannan ya tako zuwa wajen yace "Lafiya lau...." Ya fada yana duban kan dining din,sannan ya sake dubanta "Kinci abinci ne?" Kai ta girgiza "Akwai kayan tea a cupboard na kitchen din,zan fita anjima za'a kawo kayan cefane,ba wata damuwa?" Kamar jiya yauma fuskarta kamar ta fashe,yana nufin ita kadai zata wuni a sassan kenan?,wai Allah,ya zatayi,lallai zata mutu da tsoro indai yace zai sake kaiwa dare,ganin batace komai ba sai ya dora "Akwai mutane cikin gidan nan,zaki iya shiga ku gaisa,ko kuma idan na dawo saiki shiga" ya fidda kudi ya ajiiye mata "Sai na dawo" ya fada yana nufar qofar,binsa tayi da kallo,kamar ta zura da gudu ta bishi "Don Allah kada ka sake kaiwa dare irin na jiya" ta fada muryarta tana rawa,waiwayowa yayi yana kallonta,ba tare daya shirya ba murmushi ya subuce masa,shi kam ya jima baiga matsoracin mutum ba irinta "In sha Allah" yace mata sannan ya fita. Ta kusa minti talatin a wajen tana jin yadda gidan yayi mata shuru,sai da cikinta ya fara kiran yunwa sannan ta miqe,kana kallonta zakasan a tsorace take,duk da akwao motsi jifa jifa daga harabar gidan,kitchen ta shiga tana neman inda kayan tea din suke,tsahonta bazai kai ba,sai tasa kujera ta taka ta dauko ta dawo dining din ta doma qoqarin hada tea din,gana daya ta rude,saboda ummu ko latifa ke hada mata,koda ta gama hadawa ta dandana sai taji test din baiyi mata ba,ta bare baki kamar zata saki kuka,haka ta runtse idanu tana kurba har ta kusa shanyewa,dai dai lokacin da wayarta ta dauki tsuwwa,ta firgita da ringing din wayar daya soma fita,don a bazata yazo mata,saura kadan cup din hannunta ya subuce,ta ajjiye kofin ta nufi dakin da sauri. A can qasan gado ta gano wayar,a lokacin ana sake kira karo na uku MOMMY ta gani,shine sunan data sakawa hafsat,ta saki murmushi tana jin dadi,itace ta fara kiranta,cikin zumudi ta daga "Hello.....ina abban mimi?" Abu na farko da hafsat ta fara fadi kenan,ba tare data damu tayi sallama ba "Mommy ina kwana?,inasu mimi?" Ta maida mata da tambaya,ba tare data bawa tambayarta ta farko muhimmanci ba,saboda ba wannan bane damuwarta ba "Lafiya lau....ina abban mimi?" "Ya fita mommy" "Jiya a ina kika kwana?" "A dakina" "Shi kuma abban nasu fa?" "Ban sani ba,na rigashi yin bacci" gaban hafsat ya fadi "Da kika farka kenan a dakinki kika ganshi?" Kai ta girgiza kamar tana gabanta,gabanta kuma yana faduwa cike da fargabar kada ta karanci ya rungumeta,babban abun kunya kenan,tana kuma tsoron kada zancen yaje kunnen mutane a dauka ita din 'yar iska ce "Daga dakinsa naga ya fito sai ya tafi office" "Karkimin qarya fa widad?" Kai ta langabe muryarta nayin sanyi "Allah ki tambayeshi ma" ta furta zuciyarta na addu'ar Allah yasa kada yace ya rungumeta idan ya tashi bata labari. Ajiyar zuciya ta sauke,hankalinta yana kwanciya "Shikenan,ina fata baki manta komai ba?" "Eh momy" "Da kyau,ki kula da kyau kinji ko?,ki kula" "To mommy.....mommy amma ki bani mimi ko...." Bata tsaya jinta ba ta gintse wayar,iya abinda takeson ji kenan,sauran koma meye ba damuwarta bane,ta aje wayar gefan gadonta tana furzar da iska "Shegiyar yarinya,kike cewa wani wai na tambayeshi,abbas din zan yiwa wannan tambayar?,ko ke ban isa na miki makamanciyarta a gabanki ba" sai kuma murmushi ya subuce mata "Anty ummee kinyi a rayuwa" ta fada a fili,ta duqa tasa qaramin muqulli ta bude drawer din jikin gadonta da take bawa kulawa ta musamman,kudade ne a ajiiye a ciki,ta fiddosu ta fara rigasu tana hade kansu waje guda,ranta na mata fari sol,yau sai taji gidan ya mata dadi,musamman idan ta kalli sassan widad din ra ganshi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155