Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 84

Chapter 84

A Rubuce Take Book 1 Complete Hausa Novel – Widad and the Secret of House 1,314 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

karyewa,saboda komai yayi mata tana kallonsa banbarakwai,don ba haka ummu ta saba mata ba,indai tace bata da lafiya gaba daya komawa take kamar jinjinniya a wajen ummu,ta yita tattarota tana langabe mata a jiki,takanyi kamar ta maido ciwon a jikinta "Muje kici abinci,sai mu fita na kaiki kiga likita ko?" Kai ta girgiza da sauri,don ita bata qaunar ma abinda zai sanya ayi mata zancan asibiti,bata qaunar magani sam sam sam,babban abinda yake saka a gansu a rana ita da ummu kenan "Why.....zaki zauna ne a gida cikin yana miki ciwo?" "Ai zai daina" ta fada muryarta na rawa,saboda yadda ciwon ya fara mata azaba da gaske,wannan shine karo na biyu daya taba mata haka,duk da cewa duka duka period din nata ma wannan shine yinta na hudu. "it is not possible ki zauna da ciwo,oya......taso kici wani abun ko kadanne idan ma ba zaki asibitin ba" ya furta yana miqa mata lallausan hannunsa mai dumi,wanda ya wadatu da sassanyan qamshinsa. Hannun ta kalla sannan ta rintse idanunta da gaske tana jin yadda ake kartar mararta,yadda tayin sai ya tuna masa koda wasa ba zata taba yarda intentionally su hada hannu ba,don haka kansa tsaye ya miqa hannu ya kamo.hannunta guda daya,ya kuma dagota gaba daya. Luuuuu ta tafi jikinsa ba tare data shirya ba saboda wani azabar murdewa da marar ta sakeyi fiye da dazun,kamar numfashin ta zai bar gangar jikinta,take ta zabi bin gangar jikinsa ta yiwa kanta madogara,tana gama samun kyakkyawan masauki saita saki kuka tana kiran sunan ummu,hannayensa ya saka gaba daya ya rufeta da kyau cikin jikinsa. A yadda ta samu masauki me kyau cikin jikinsa ya sanya hatta da bugun zuciyarta da kai kawon numfashinta tana jinsa sosai cikin jikinsa,kamar jininsa suke bi cikin kowacce bugawa da zaiyi. Sunkuyo da tasa fuskarsa yayi ta gefen fuskarta dake kwance kan qirjinsa da yake ya fita tsayi sosai ya cusa tasa fuskar yana leqata,wani irin kuka take a hankali hade da sheshsheqa,hucin numfashin ta ya daki fuskarsa,sai ya lumshe idanunsa tsigar jikinsa na tashi,ya sake riqeta sosai zai motsa,saita kuma qanqameshi tana sake sakin kukan,abinda ya sanyashi kusan daskarewa a wajen,gaba daya ta manna masa jikinta da kyau,lallausar fatarta takai ko ina a jikinsa ba tare data sani ba,ita din kuma tayi hakane saboda batason su motsa daga wajen,ta tabbatar ta bata wajen da jini,bataso kuma ya gani,kunya takeji,da wanne ido zata kalleshi?. "Let's move from here,mu koma daki ki kwanta na fidda mota kiga likita,jikinki shacking yakeyi" yana fada ya sunkuya kawai ya dauketa cak,bata da sauran zanbi sai kawai ta boye kanta cikin jikinsa,bayan ta saka hannu ta riqeshi da kyau. Bai lura da komai ba sai daya shimfide ta saman gadonsa sannan yaga hannunsa ya baci,ya daga kai ya kalleta,sake saka masa kuka tayi,abinda taketa gudu kenan,ta rintse idanu tana jiran jin fada ko duka daga wajensa,kamar yadda yaa ma'aruf ya taba mata saboda kawai ta kawo abinci ya bata flask din ya riqe hannunsa ya baci. Maimakon taji abinda ta zata saima jiyo sautin ruwa da tayi a toilet,ba jimawa ya fito da alama wankewa yayi,suna hada ido ta dauke kanta hawayen naci gaba da sauka,ciwo da kunya duka suka hadar mata,ya qaraso gabanta a hankali ya tsugunna "Dama kina period ne?" Wayyo Allah,ji tayi kaman zata nutse a wajen,ta jawo filo ta cusa kanta tana sake sakin kuka,wannan abun sam bai kyauta mata ba,inda ta san zaizo gida zata dage sai ya kaita. Sake maimaita mata tambayar yayi amma shuru, ganin da gaske ba zata amsa mishi da komai ba,taqi daga kai ma ta fuskanceshi,sai kawai ya miqe yana murmushi ya fita a dakin. Da kansa ya gyara wajen data bata din a falo,wajen bashi da wani yawa sosai,ya dauki waya ya kira na 'yan mintuna ya kashe. Da pad ya dawo mata,ya ajjiye mata yace ta shirya zai fiddo mota suje asibiti,yana zaune a falo ya dora qafa daya kan daya yana amsa waya ta fito tana rab'e rab'e,kunya kamar qasa ta tsage ta shige,wayar na a kunnensa ya waiwaya ya dubeta,can qasan ransa fal dariya,duk da babu ko alamun hakan a saman fuskarsa,ya jima baiga yarinya mara wayo mai tsananin tsoro da kunya irinta ba,iya period kawai data fara ya gani?,inda ace ya karba budurcinta ne fa gaba daya?, Shi kansa daya raya zancan a ransa sai daya sake maimaitawa,sai kawai qaramin murmushi ya kubce masa,ya cije lips nasa na qasa kadan saboda yadda yaji jikinsa ya amsa gaba daya,baisan lokacin da hakan zai faru ba,amma tabbas duk sanda ya kasance qila saita kusa mace masa saboda tsoro. Wayar ya kashe ya mayar aljihu sannan ya miqe,ya tako kadan gabanta "Zaki iya tafiya?" Kai ta jinjina masa ba tare da ta iya kallonsa ba "Muje to na gani idan zaki iya din" ya matsa gefe yana kallonta,ta rabashi a hankali ta fara takawa tana hada hanya,taku uku ya cimmata,ya riqo kafadunta suka ci gaba tafiya,tanason zare kanta,amma hakan da yayi mata saita dinga jin kamar relief yake bawa ciwonta,a haka suka qarasa,ya buda gaban mota ya sanyata ya kwantar mata da kujerar,sannan ya shiga ya tayar da motar suka fice daga gidan. Da yake private hospital ne basu samu wani layi ba suka samu ganin likita,duk tambayoyin da yayi mata kusan shuru tayi,tanajin kamar ta narke,maza biyu a daki guda suna mata tamba game da period dinta,abinda ko acikin gidansu boyewa take ba kowa yasan ta fara ba, murmushi likitan yayi ganin lokaci lokaci tana satar kallon abbas "Yallabai,da alama kai din ba yayanta bane na hannun dama,ko zaka bamu waje qilan tafiyin bayani" haka kawai cikin ransa yaji bazai iya barinsu su kebe ita dashi ba,don yaga baima fahimci matar aure bace,yayi yunqurin miqewa da nufin matsawa daga koda zuwa bakin window ne,saiji yayi caraf an kamo hannunsa,ya waiwaya a hankali,itace ke kallonsa tana qwalla "Kada ka tafi please" hada ido sukayi da likitan,sai ya saki dariya sannan ya miqe "Ta gaya maka abinda takeji,sai kayimin bayani,ina zuwa bari na samo nurse,za'a yi mata scanning,tunda kace ciwon mara ne" sai likitan ya cire abinda ya saqala a wuyansa ya ajjiye ya fice daga office din. Cikin kunya ta soma qoqarin zame hannunta daga nasa,amma saiya qara matsowa yana sanya dukka tafukan hannunsa a ciki da saman nata,ya rahe gap din dake tsakaninsu sosai yana dubanta "Uhnnnn.... tell me,kinga idan ya dawo baki fada ba zan tafi na barku tare" qoqarin tsaida kukan nata take tayi,taja majina sannan tace cikin muryar kuka "Marata ce take ciwo sosai" ta fadi cikin mugun jin kunya "dai dai ina?" Ya tambayeta yana kallon qwayar idanunta,sai ta motsa hannunta dake mararta kadan,kamar mai tsoron kada ya taba hannun nata. Idanunsa ya mayar kan hannun nata,sai yasa yatsansa ya nuna wajen "Wajen nan kenan?' ta gyada kanta a hankali,sai ya dauke dubansa daga wajen yana fidda numfashi,ya miqe a hankali,yayi taku biyu kenan saiga likitan ya dawo,bayansa wata nurse ce,zata kusa shekaru talatin,ba yarinya bace. Yana dariya ya tambayi abbas me tace?,ya zube hannayensa a aljihun wandonsa yana duban likitan "Ciwon maranne dai" "Ba damuwa,da Allah ki mana scanning,bari naje mota na dawo" ya sake fada yana diban wasu takardu ya fice. Sanda taga an gama saitan scanning machine din tace kuma tahau sai

Table of Contents

Chapters

155 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});